👨✈💗👩✈ *GIDAN SOJA*👨✈💗👩✈
By
*UMMU DILSHAD*
Marubuciyar
*(1) LABARINA*
*(2) DALILIN BAKIN KISHINA*
*(3) GIDAN SOJA*
👇
Intelligent writers Association...®✍
(Onward together).Dedicated to, Daukacin members na kungiyarmu ta *(INTELLIGENT WRITERS ASSOCIATION)* kudin na dabanne har cikin Raina nakejinku, tundaga kan boss harzuwa Ni kaina Ina Mana fatan Alkairi, Allah ya Kara daukaka Mana kungiyarmu Ameen
*BISIMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM.*
🅿8
Tsananin mamaki ne yakama Haj maimunatu, General, dakuma Hamza a inda shikuma Saifullahi abun tsananin farinciki yasashi Wanda seda ya haddasa bayyanar murmushi akan fuskar shi, abangaren lantana kuwa tsananin bacin Rai da razana hakan ya jamata, Wanda yayi sanadiyyar sata kwarewa ta kama yari sedai kafin kowa ya yankara da ita bare amata sannu ta tashi da gudu tabar gurin, bangaren su ta nufa tana zuwa ta fada daki da gudu tana kuka me tsuma zuciya, tareda jin zafin abunda Farrah din kemata na son ganin ta rabata da masoyinta Kuma ita tana ganinma kamar da gangar Farrah din ke Haka Dan kamar ta lura cewa lantana tanason Saif din, Wanda ita Farrah din da nata dalilin daban.
Acan fallon kuwa Haj maimunatu ce tasaki Wata irin shewa tana fadin Heeeeeeeeee a hayyeeee tafada tana tafi, kagani ko kasancewa yarka ta kosa kagani Kuma kaji da kunnenka Dan Haka seka gaggawta yin abunda tace inba hakaba tarihi ya maimaita kanshi, kamar yadda aka.........kallon da Gen din ya watsa mata me dauke da harara ne yasa ta fasa karasa abunda tayi niyyar fada seta rufe bakinta Bata Kara cewa komaiba.
Gen ya nisa tareda kallon fuskar Farrah cikin yanayin farinciki yace Yar Dady shin Wai dagaskene abunda nakeji yanzu daga bakinki? Kuma Ina son sanin Dalilin yanke wannan hukuncin naki, murmushi tayi me sunan *kafi kuka ciwo* zuciyar ta tana mata wani irin zafi na takaicin rashin kokarin Hamza gurin kasa bayyana ma mahaifinta soyayyar dake tsakaninsu tareda zargin ko yasan wacece itane yasa yaji ya fasa aurenta kuma ya gujeta, sannan ta kalli Hamza ta koma ta kalli Gen tace, Eh Dady dagaskene Ina so arage yawan watannin bikinmu, saboda Ina matukar San sanin asalina bayannayi aure saboda ina tsoran kar akai bikin bayan birthday Dina Kuma Yaya saif yaji asalina ya fasa aurena Dady ta karasa maganar tana hawaye nafison insani bayan aurena ne saboda Koda ya rabu Dani akalla zan kafa tarihin cewa na taba Auren Wata daya, hawaye suna gudu akan kumatun ta takalli fuskar Gen a inda take fuskarshi ta juya daga farinciki zuwa bakin ciki, da sauri Saifullahi ya Ciro handkerchief fari tas ya Mika mata Yana fadin, karba ki share hawayenki Ni Saifullahi Dan uwankine Kuma jininkine sannan kodama bamu hada komaiba kaunar da nake Miki bazata taba barina in rabu dake ba Koda kuwa agaban idona akayi zina aka haifeki Farrah Ina sonki Ina kaunarki son da bantaba yima Wata halitta irinshiba tunmuna yara nake kaunarki inata jiran sanda Zaki girma ne kawai in Aureki, ke kadaice acikin zuciyata da Ruhina duk girman zuciyar dake manne a kirjina ke kadaice kiketa nin kaya acikin baban tafkin so da kaunar da Allah ya halitta aciki Wanda har abada be taba kafewa ba Kuma baze taba kafewa ba, Farrah Ina sonki Ina kaunarki har abada kece kadai Zaki samarmin da farinciki a Rayuwa ta.
Sosai Gen ke jin dadin kalaman Saifullahi Wanda yayi dalilin gushewar bakinciki da kukan Farrah ya haddasa mishi Nan take ya Fara tafa hannayenshi biyu Yana fadin _bravo Dana Saifullahi ina jin dadin yadda kake nunama Farrah so da kauna_, ya juyo ya kalli su khalil da kannen Farrah da gabadaya bakinsu abude yake saboda Tsabar mamakin dama Yaya saif ya iya kalaman soyayya Haka?
Sannan Gen ya koma ya kalli sauran masu hidimar gidan yace Dan Allah kuyi gingering din Dana Saif da tafi, take gurin ya kauraye da tafi, su farida da Nabeela sunayi suna dariya suna fadin Kai dama Yaya saif ka iya soyayya Haka farida harta fadin Yaya waya koya maka, dariya Gen yayi Yana fadin soyayyar Farrah ce ta koya mishi hakan yasa Saif tsananin jin kunya ya tashi da gudu yabar gurin, itama Farrah yashi tayi tabar gurin ta wuce daki tanata kuka tana fadin *Allah babu abunda zance da Kai se godiya, hakika zuciyata Hamza takeso to Amma ga Kuma zuciyar Yaya saif nitake so Allah Kai kadaine ka kaddara wannan al'amarin Kuma kaikadaine kasan meye mafi Alkairi daga ciki, Allah inhar aurena da Yaya saif shine mafi Alkairi Allah ka tabbatar dashi inkuma kasancewata da Hamzane mafi Alkairi Allah karka Bari adaura aurena da Yaya saif ka kawo abunda ze Hana hakan* sannan ta Kara fashewa da Kuka me tsuma zuciya.
YOU ARE READING
GIDAN SOJA
RomanceLABARINE A KAN GIDAN BABBAN TSOHON SOJA DAYASHA GWAGWARMAYAR RAYUWA, SANNAN AKWAI CHAKWAKIYAR SOYAYYA.