Episode 6

138 4 0
                                    

¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09

👩‍🦰👩‍🦰👩‍🦰👩‍🦰
KANKI KIKA CUTA
    👩‍🦰👩‍🦰👩‍🦰
         👩‍🦰👩‍🦰
            👩‍🦰
(Tsantsar cin amana)

Story and ✍️ written by
Khadeejaht Hydar
(Young Novelist)

From the experience writer of.
.*IHSAN
*UQUBAR UWAR MIJINA
*WATARANA SAI LABARI
*PRINCE AIRAN AND MAIMOON.

And now with the heart touching one.
KANKI KIKA  CUTA

karku manta novel  d'ina na kuɗine mai son karantawa zai iya biyan ƙuɗi ta banki kota kati,bayan angama free pages.

Musa Khadijat Nana
0029001824
Unitƴ bank
Sannan kanuna shaidar biyanka ta whatsap dina
07069688588.

Masu son biya ta hanyar kati kuma,ku tura ta wannan number.MTN
07061651640

Vote me on wattpad
YoungNovelist4

My Facebook Group

https://www.facebook.com/groups/228916361333651/

Free Pages.

EPISODE SIX.
A STRANGER
      
A lokacin daya iso gidan yace tafito waje ,cikin zumuɗi ta gyara fuskarta tafito waje tana doka murmushi,daga nesa yake kallonta tana sanye cikin code less blue mai adon fari ta yafa ɗan madaidaicin gyale fari wandaya rufe jikinta da flat takalmi blue saida ta ƙaraso yaga fuskarta ba kwalliyarnan ta yanzu me canza kamannin mutum illa powder da lipgloss me sheƙi tayi kyau sosai ta kashe ɗaurinnan na zamani wanda kana iya hango sumarta ɓaki ƙirin me laushi wanda akecema virgin hair ya nuna ta ƙasan ɗankwalin ta,da murmushi yace"....Matata kinyi kyau kinganki kuwa kamar de Jaddatee kakarsu sukecema Jaddatee,murmushi tayi tace"...kadaina haɗani da wannann tsohuwar matartaka,dariya yayi yace"...tade fiki kyau.

Cikin mota suka shiga suka zauna tagaidasa da tambayar ya yabar su Mama,duk lfyarsu kalau wlh sunmabani saƙo nabaki harda Haleema,tace"...Allah sarki bestie nasan tayi kewa ta nima haƙa wlh ai Haleema tana sona sosai,shiru yamata can kuma yace"...ya karatu dafatan ana maida hankali ko?,tace"....eh Yaya fira suka dingayi cikeda so da ƙaunar juna,dayake glass ɗin motar abuɗe yake saiga Falmata tazo suka gaisa hartana tsokanar Saleema wai to aide gashi ya dawo yau anbarni  naji gari,dariya sukasa duka Saleem yace".....ngd naga kin iya kulamin da mata kyautarki dabance tana dariya ta musu sallama ta wuce".

Fira sukasha sosai yabata tsarabarta da wanda su Mama suka bata da nashi dana Haleema,tayi murna sosai suna zaune aka ƙirasa da wata number,ɗagawa yayi yasa a handsfree saboda hannunsa dake riƙeda chocolate sunasha,Sallama akayi ya amsa yana tuna ina yasan muryar hakama Saleema batadamuba taci gaba da shan chocolate ɗinta dake hannun Saleem wanda shikebata abaki,amsawa yayi hankalinsa nakan Saleema cikin dakewar murya yace"...wake magana,cikin kissa tace"....wacce ke mutuwar sonka kamar ranta,murmushi yayi don sarai yagane me maganar amma sai yanuna bai ganeba yace"...ai ni inada mata kuma kwanannan zamuyi aure insha Allah,Saleema wacce tadaina shan chocolate ɗin hankalinta yakoma kan wayar dayake ,a hankali ta ɗauki wayar tafara magana cikin kwantar da hankali tace"....Malama ki ƙirasa anjuma yanzu tana tare da matarsa kuma abinci yake bani zaki iya ƙiransa anjuma daga haka takashe wayar ta buɗe baki da nufin yabata chocolatw ɗiɓ ,samata yayi abakinta  yace"...yanzu munyi sabuwar amarya zaki korarmana ita,cikin basarwa tace"....ta makaro ai kuma ni banga me aurar min miji ba wlh,sun ɗan jima bata nunamasa taji haushiba sukayi sallama da alƙawarin jibi zai dawo ta kwashi tsarabarta da taimakon Falmata suka kai ciki"..

Bayan sun jera komai  a inda ya dace tayi wanka dayake tana fashin sallah kawai tahau whatsap,saƙo tagano da sabuwar number buɗewa tayi tafara karanta kamar haka.

Mrs Saleem nasan bakisanniba to dafatan kin fara shirin barin Saleem donshi nawane wlh bandamu kowa ya mutuba saina aureshi kota halin ƙaƙa ne.

Reply Saleema tamata da uhm Allah yafiki kuma aurena da Saleem anriga an ɗaura daga sama,mutu ka raba takalmin kaza daga haka ta dannan mata block,saƙon Saleem tagani ko buɗewa batayiba yanata mata magana amma shiru ba amsa kuma yanaganinta a online.

Ƙiranta yayi amma taƙi dagawa yayita ƙira amma taƙi dagawa daga bayama tasa wayar a silent tayi kwanciyarta,wayar Falmata yaƙira yace"....pls kibawa Saleema waya naƙira taƙi dauka,ohk daga haka tamika mata wayar tafice daga ɗakin,tana amsa tayi shiru cikin kwantar da murya yace"...Saleema what happend pls tell me,nata ƙira da msge amma shiru,cikin faɗa tace"...kaje ka ƙira sabuwar budurwarka harkabata hanyar bina ta whatsapp tana zagina harda cemin ita zaka aura to Allah yafi....baƙin ciki yasa takasa ƙarasa zancen ta kashe wayar"..

Aibashiri ya ɗau mota daga Hadeja yazo birnin kudu,tana kwance kawai taji Falmata nacewa tunda kin hanasa sukuni ai sai ki tashi kitafi yana waje yana jiranki amma Saleema akwai ƴar iska taƙatasa zancen da murmushi,ko kulata batayiba balantana ta tashi,fitaFalmata tayi mintuna ƙadan kawai taji muryarsa ƴana cewa ƙawarmu na gode".

Banza tamasa ba zato ba tsammani kawai tajisa abayanta yana ƙoƙarin juyo da'ita,da hanzari ta tashi tana ƙare haɗa fuska ,janyota jikinsa yayi ya rungume yace"...meyafaru ne wai Gimbiyata,kuka tasamasa wanda tun ɗazu take sonyi amma yaƙi zuwa,bubbuga bayanta yayi tadanyi shiru tukun tace"...dazu kana waya da wata agabana kuma kabata numbata tanata zagina,shi dariyama tabashi wai yabata numbarta,cikin kwantar da murya yace"...sit let's talk zama tayi yakamo hannunta yace"...do u believe that i love you,gyada kai tayi yace"...Saleema wlh ke ƙadai nakeso a yanzu a duniya bana fatan ƙara wata bayanke amma bansan abinda Allah ya tsaraminba,ni bansontaba kuma bazansotaba pls ki kwantar da hankalinki babu ne shiga tsakaninmu,a hankali tace"...promise me u wont turn ur back at me,da murmushi yace"...wlh Saleema ko rayuwata aka buƙata donke zan bayar ballantana wani minor abu,tsaf suka shirya ya ƙarbi wayarta yaga harta goge yace"...inta ƙara miki mgna karku kulata zanyi maganinta"....

Bayan ya koma gida  yaƙira layin tana ganin ƙiran ta ɗauka cikeda zumuɗi amma kafin tayi magana yafara zazzagamata masifa yace"...bansan bakida tunani da hankali ba sai yau kinason kici amanar ƙawarki wacce tayarda dake to kisani ni SALEEM TAMEER banda matar  AURE SAI SALEEMA TAMEER,kuma this should be the first and last time dazaki ƙirata ko ki ƙirani  if not zanfaɗamata kece ke shirin cin AMANARTA ,ke ko kunya bakijiba ,Saleem fa tainda yashiga batanan yake fitaba ,amma a maimakon taji haushi saima tayi murmushi tace"...Yaya Saleem kadainaganin wai shekaruna sunyi ƙadan ko bazan iya maka ta ƙarfi amma mark my words ko duniya zata juye saina aureka kuma saina rabaka da Saleema,kuma da kake cewa cin amana to ai iyawace kowama yayi,amma kasani I love you,eh na tabbata bakida hankali sheƙarunki nawa baki wuce ashirinba amma kiniya cin amana to wlh ki guji haɗuwata dake daga haka ya akshe wayar a ransa yace"....saina koyamiki hanƙali"..

A ranta tace"...to kafaɗamata mana ai gwara tasan wake mata adawa,tayi tsaki tace"...komai saitace ya Saleem to wlh nan da wani lokacima inkikaji sunan Saleem sai kin gudu ƙin ɓuya shikuma sai ya tsaneki kamar ya kasheki,saikin daina  taƙama dashi saikin daina alfahari dashi,tayi tsaki tafaɗawa Fareeda yadda akayi a waya.

Saida Saleem ya kwashi watanni bakwai a jigawa yana jiran Saleema ta samu hutu saisu koma tare,gobe yakama zasu koma lagos ta hada duka kayanta hakama Falmata zata wuce yobe gobe,bawanda ya faɗawa Haleema zuwansu kuma Saleem ne yace sumata suprise wanda shi yayine don yasan zatazo yadda tayi  abayancan yanason Saleema taganta ,in anci sa'a ta harbo jirgin dakanta don yasan inyafaɗa zai mata shock".

Saleema da Falmata  ne a zaune suna magana Falmata tace"...ki rike addu'a sosai zai miki maganin komai,Saleema tace"...nagode Allah yabar zumunci  kuma zan riƙe  yadda kikace,Falmata tace"...  Insha Allah babu me shiga tsakaninku sai ikon Allah kuma ita zataji kunya,amin cewar Falmata,nasan in Haleema taji wannan zancen saita ɗaukarmin mataki,Falmata tace"...karki faɗawa kowa tukun muga me Allah zaiyi,daga haka suka kwanta don gobe da wuri zasu tashi"..

Tohm nima fans anan zan tsaya saikunjini gobe.

KANKI KIKA CUTAWhere stories live. Discover now