15

72 10 1
                                    

✨💫✨💫
            *SHAHEED*
                       ✨💫✨💫
*1442H/2021M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:- HIJJART ABDOUL*

*SADAUKARWA GA:-* FANS

*TUKUICI GA:-* SWEETHEART

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

   

*SHAFI NA 15📑*

*__________📖* Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya nufi ƙofar waje, kamar mai tsoron wani abu haka yake tafiya yana duba inda yasan ana zama a gidan gashi ko ina yayi tsit alamar dare yayi sai iska mai daɗi da take kaɗawa kasancewar ana zafi duk da yanayi ne na dumuna, haka yayi tabi har yazo bayan part ɗin su yana dubawa yana lalleƙawa kamar kuwa ance juyo ya ganta zaune a ƙasa ta haɗe kai da gwiwa tana zabga kuka na fitar hayyaci ma kuwa wata irin ajiyar zuciya ya sauke lokaci guda kuma wata nutsuwa ta same shi sannan ya karasa wurin ta a hankali shima ya zauna a ƙasa  yana fuskantar ta, bata san da zuwan sa ba dan kuka ne take yi na irin anjima ba'a mata abinda aka yi mata ba ko kuma ta tuno wani abu ne Allah kaɗai ya sani, ganin ba dena wa zatayi ba kuma bata kula dashi ba yasa shi kama hannun ta data haɗe kan dashi a zabure kuwa taja baya ganin shine yasa ta ƙara fashewa da kuka tana shashsheka, tana girgiza masa kai alamar a'a, murmurshi yayi mata mai cike da tausayi sannan ya ƙara jawowa ta sosai jikin sa ya ɗaura kanta a cinyar sa ya fara goge mata hawaye yana girgiza mata alamar ta dena ya isa haka nan, daƙyar ya samu hawaye suka dena zubowa sai ta koma ajje ajiyar zuciya bata dena kallan shi ba kallo ne na irin ina san nace wani abu amma bansan taya zan fara ba ganin haka yasa shi sakar mata murmurshi.

Yace, "Yi hakuri bazan sake ba, kinji ko?"

"Kuma yanzu tana wurin mu, bazamu mayar musu da ita ba".

Gani yayi tayi ɗan murmurshi kaɗan tana cigaba da kallan sa.

Shima zamewa yayi ya kwanta a ƙasa suna kallan juna kafin lokaci guda kuma su koma kallan sama suna kallan watan da taurari.

Yace, "Mamanah ta sanar da cewa nazo na rarrashe ta, kinsa wani lokacin zuciya ta na bani cewan ke ita ce?"

"Ina Maman?"

"A mafarki na ganta yanzu".

Ya faɗa da ƴar ƙwallar a idan sa.

"Dama ace nima naga Mamanah".

Ta faɗa itama tana kai hannu ta share ƙwallan ta.

"Maman ki ta mutu ne? kamar yadda tawa ta rasu?"

Kallan ta yayi jin tayi wani irin murmurshi takaici.

Tace, "da'a ce mutuwa nasan inda ta tafi amma sai dai kash bansan ina take a halin yanzu ba".

"Me kike so kice?"

"Abinda kaji na faɗa".

"Please Meemeenah ki bani labarin rayuwar ki ko yana ko zan samu hasken wani abun akan alƙawarin dana..."

Sai kuma yayi shiru tunawa da abinda Ahmad ya faɗa masa akan kada ya sanar ta, kuma sai ita ce zata sanar dashi sauran labarin dan shi ba duka yasani ba. Kallan shi tayi yayi murmurshi.

SHAHEEDWhere stories live. Discover now