✨💫✨💫
*SHAHEED*
✨💫✨💫
*1442H/2021M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:- HIJJART ABDOUL*
*SADAUKARWA GA:-* FANS
*TUKUICI GA:-* SWEETHEART
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*SHAFI NA 19📑*
*__________📖* Lokacin da su Shaheed suka dawo daga asibiti a lokacin suma su Abba suka dawo dan haka sai da su Abba suka fara shiga Sannan suma suka shiga kafin su Shiga.
Hassana tace, "Ka ajje ni anan kaga Abba ya dawo zaiyi maka faɗa".
"Ba abinda zai ce".
Ya faɗa be kula ta ba bare ya aikata, ya shiga yayi parking mota suka fito ita de Hassana jikin ta har wani ɓari yake gudun kada ayi masa wani abun kamar kuwa ance da Abba juyo wanda yayi gaba yabi Umma basu wani yi nisa ba yaga Hassana ya juyo ya sake kallan ta ya ɗauke kai har ya wuce kome ya tuna oho ya dawo wurin da Shaheed yake.
Yace, "magana ka dena ji?"
"Abba me ya faru?"
Tas! Tas! kakejin ƙaran mari an waske shi da mari masu zafi da raɗaɗi gami da azaba, Shaheed ba shiri ya saki abin hannun sa ya fara mirza fuskar sa idan sa ma ya kawo ƙwallon tsabar zafi gashi marin abazata yazo masa be taɓa tsammani bare ya shirya zuwan su, yana mirza wa yana kallan Abba.
Abba yace, "Ina tambayar ka kana tambaya na? reni ya fara shiga tsakani na da kai ko?"
Be saurare shi ba ya kalli Hassana da idan ta ya fara zubar da ƙwalla.
Yace, "kin wuce ko sai na haɗa dake".
Fuuu ta wuce ciki tana neman yin tuntuɓe.
Yace, "Wannan ya zamana karo na ƙarshe da zan ganka da dangina ko wani nawa idan ba haka ba kuma".
Ya ɗaga hannun sa tare da nuna ɗan yatsa.
"Nida kai ne".
Ya wuce shide Shaheed azaba ta ishe shi besan sanda kayan hannun sa ya zube ƙasa ba, sai yanzu da ƙwalla ta zubo masa, ya kalli ƙasa sannan ya sani har yanzu yana shafa kuncin sa duka biyu sabida ba a wuri ɗaya aka sakar masa marin ba, a hankali ya duƙa ya kwashe kayan ya wuce ciki yana shafa fuskar sa da hannun sa guda ɗaya.
Tana kwance ita da Khadijah tana karanta musu wani novel tayi bacci ganin tayi bacci yasa ta kunna kallo tana tayi tunda ba laifi hannun nata na kaiwa wurin socket din tana cikin kallan ya shigo sam bema kula da Mimi zai zauna a kan ta cike da Khadijahn.
Tace, "Zaka danne ta".
Wani mahaukacin zabura yayi sabida abu biyu tsorata da yayi da maganar ta sannan kuma yadda tayi magana ya tsorata shi kada ya danne ta, tsaye yayi yana kallan ta yana ƙifƙifta ido ita kuwa ta maka masa harara, ta juya ta cigaba da kallan ta, daƙyar ya tako wurin ta ya tsugunna.
"Like seriously?"
Ya faɗa yana rarraba maganar ya kafe ta da ido.
"Please kice wani abu na tabbatar Please".
YOU ARE READING
SHAHEED
Random"Mamanah ya za'ayi ace kina fad'ar haka? kidena Mamanah bana so kinsan yarda nake ji ne? kinsan yarda naci burin rayuwa dake shine zaki kike fad'ar wanna maganar?" "Idan bata fad'i maganar da zata sa ka shiryu ba. Me kake so ta fad'a maka? idan har...