33

73 5 0
                                    

✨💫✨💫
            *SHAHEED*
                       ✨💫✨💫
*1442H/2021M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:- HIJJART ABDOUL*

*SADAUKARWA GA:-* FANS

*TUKUICI GA:-* SWEETHEART

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

 

*SHAFI NA 33📑* 

*__________📖* Washegari da safe yaje ya anso mata passport ɗin ta ya biya mata kuɗin jirgi dake shi an biya masa daga inda aka tura su, kuma kuɗin dayawa sabida a gobe yake san su tafi a haka kuwa akayi aka shirya musu tafiyan nasu zuwa gobe har shi duk shi an biya masa kawai tafiyan ce duk sanda ya ga dama da wancan sati biyu da suka wuce zai tafi sai kuma abu yazo ya cabe masa ko ace yayi hijira.

Sanda ya fita tana bacci dan haka bata san yaushe ya fita sai tashi tayi taga baya nan, gyara gidan tayi tsab sannan ta shirya Breakfast iya cikin ta taci ta fita gidan Mummy tace suka gaisa ta jima acan sannan ta dawo ta shiga cikin gida suka gaisa da Umma taje wurin su Khadijah anan suka sha hiran su Sadiq ne ya zo shida Munneerah suna zuwa su Neera na zuwa sai aka haɗu aka fara ƙinji duk da wannan shine karan farko da Munneerah tazo gidan amma sosai ta ware dasu kai kace sun saba tun Sadiq ma mata maganan har ya gaji ya zuba mata ido.

Da sallamar sa ya shigo Parlour yana wani haɗe fuska dan yasan Sadiq na nan tunda yaga motar sa, kallan sa yayi ya wurga masa harara.

Yace, "meye zaka wani zo mana gida?"

"Wurin matata nazo ko zaka hanani?"

Taɓe baki yayi.

Yace, "ka cika baki yanzun nan zan hana ka auren ta badai shine kake wani taƙama kana da Abba ba? To Abba ma sai da izinina zai bayar da ita".

"Ƙwarai ga Baban ta ko Yaya babba".

"Kada ka cika baki Sadiq?"

Ya faɗa da wani irin murmurshi mugunta na irin kada ka kuma, shiri Sadiq yayi yana kallan shi kawai sannan ya ɗan harare shi.

"Ke ina matata?"

Ya faɗa yana kallan Hassana, banza tayi dashi ko kallan sa batayi ba, zuwa yayi ya ɗauki Boy yana masa wasa.

"Ke dan raini ya shiga tsakani na dake ko? dan kinga kin haifi ɗa kin haihu wato bari kiyi abinda kikaga dama ko? to ni ɓalla ki zanyi bansan wannan ba, ai ɗan nawa ne ba naki ba baki da wani iko da shi ato".

Sadiq yace, "Kai dai Shaheed Allah kadena abinda kake, kowa sai ka masa baka ƙyale kowa ba".

"Ban ƙyale ɗin ba kuma bazan ƙyale ɗin ba".

"Allah ya baka haƙuri".

"Better".

Ya faɗa yana maida idan sa kan su Munneerah sannan kuma yayi inda suke suna wasa yaje ya zauna suka fara. Fahad ne ya shigo shima da sallama zuwa yayi suka gaisa.

Yace, "Fahat kwana dayawa".

Ranƙwashi ya sakar masa.

Yace, "Ka kiyayeni sunan nan ya fita a bakin ka taam".

SHAHEEDWhere stories live. Discover now