23

73 8 2
                                    

✨💫✨💫
*SHAHEED*
✨💫✨💫
*1442H/2021M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:- HIJJART ABDOUL*

*SADAUKARWA GA:-* FANS

*TUKUICI GA:-* SWEETHEART

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*




*SHAFI NA 23📑*


*__________📖* Ta maimaita cikin sigar tambaya gami da mamaki, sai da ya goge hawayen sa.

Yace, "Shine, shidai da kika sani kuma kinsan me?"

Be jira amsar taba.

Yace, "ina san Matata duk da shine yace na nemi soyayyar ta, mun fara soyayya tiryan tiryan da ita har ta kai ga aure amma sai ca yace wai kada taji daɗin aurena, Umma Hassana na da kirki, tana da biyayya bansan wanne ya zan fassara maki ba amma haka mutumin nan yace wai cikina ba nawa bane na Yayan ta ne dan kawai bama jituwa dashi kuma shi Baban sa be san sa amma Umma wallahi nasan cikin jikin Hassana Umma wallahi nawa ne".

Shiru tayi masa tana kallan sa, kafin tace.

"Meyasa zakayi haka?"

"Umma shine ya sani fa, sometimes har tausayi take bani, Umma ina san ta".

"Kasan kana san ta meyasa ka biye masa?"

"Umma, haka yace Mahaifin ta kafin ya rasu ya cuce shi shine yake so ya rama akan ƴar sa yace sune suka talauta shi suka raba shi da kowa nasa shine abin ya bani haushi nima nake azabtar da ƴar ta amma a yanzu Umma na fara gane ƙamshin gaskiya".

"Wacce gaskiya?"

"Yana ɓoye min abu dayawa sannan ya raba ni dake".

Wani irin murmurshin takaici tayi mai cike da ma'ana.

Tace, "Tijjani, Mahaifin ka wani irin mutum ne mai riko, mai rama abinda aka masa komi ƙanƙan tar sa, baya da hakuri be san kalmar hakuri ba, gashi kuma rikitacce, ya rabani da kai tun kana ƙaramin ka a ganin sa faɗan da nake ma da kuma ɗan bugun da nake ma duk a ganin sa bana san kane ba, besan cewan kwaɓar yaro tana koyar da tarbiyya bane idan yayi abinda ba dai-dai ba, Tijjani dalilin ka yasa muka rabu da Mahaifin ka kasan da haka?"

Beyi magana ba ta cigaba.

Tace, "Dole akwai wani abun da wannan familyn ɗin suka masa ba kuma sune suka raba shi da ƴan uwan sa ba mugun halin sa ne yasa mahaifinsa korar sa daga gida daga baya kuma ya mahaifin nasa ya dawo dashi gida ganin zai iya lalata rayuwar sa, dawowarsa gida befi da watanni ba ya gudu daga gidan nasu bayan ya sace kuɗin Mahaifin sa, kaji yadda ya bar gida ya dawo Zakirai sai ya zama mutumin arziki a idan kowa sai ya fara neman yadda zaiyi ya zama wani mai faɗa a ji hakan yasa kaf mutanen garin suke ganin girman sa har sanda ya aure ni sannan na gane halin sa".

"Iyayen sa suna da rai har yanzu?"

"Sun rasu bayan yaje ganin su gida lokacin tare muka je, kana ƙarami sanda muka je yana tsaninin ciwo kwanan sa ɗaya ya rasu da kwana uku matar sa itama ta rasu sai ya tattara sauran dukiyar sa duk da yana da ƙani sai kawai ƙanin ya bashi a cewar sa shi baya so shine muka dawo".

SHAHEEDWhere stories live. Discover now