3

130 10 2
                                    

✨💫✨💫
*SHAHEED*
✨💫✨💫
*1442H/2020M.*
*1NOV/SAFAR15*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:- HIJJART ABDOUL*

*SADAUKARWA GA:-*FANS

*TUKUICI GA:-*SWEETHEART

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

INA MIK'A GAISUWA GA DUKKAN MASOYANA DA HADIN KAN DA KUKE BANI SAI DAI KUMA WANNAN NOVEL DIN DA NA FARA POSTING ZAI ZAMA NA SAU DAYA A SATI SABIDA MAKARANTAR DA NA KOMA IN SHA ALLAH A SANNU SANNU ZAMUJE HAR INDA MUKE SO MUJE FATAN MU ALLAH YASA MU GAMA LAFIYA YARDA MUKA FARA LAFIYA DANI DAKU DUKAN MU.

love you all😘

*SHAFI NA 3📑*

*__________📖* "Babana ka tashi mana tun d'azu nake tashin ka amma baka tashi ba, gashi har su Khadija sun tafi".

Juyi yayi ya kuma jan bargo abin sa, zuwa tayi taje ta bud'e windown sa rana ta fito ta daki fuskar sa amma a banza Dan m dad'in ranar yaji sabida sanyi ne hakan yasa k'ara jin dad'in baccin nasa.

Zuwa tayi ta bubbuga bayan sa da k'arfi.

Tace, "zanje na cinye wainar da kasani nayi ko na bayar ta".

Ai Kamar a mafarki yaji tace ta cinye wainar Munneera dan jiya ma daddare daya dawo daga yawon sa shabiyu da wani abun sai da ya tuna mata dan duk dare bata bacci sai taga dawowar sa.

A wani zabure ya tashi ya mik'e zaune yana wulli da bargo ganin tana masa dariya yasa shi tsayawa yana kallan ta.

Yace, "Mamanah dagaske?"

"Idan de baka tashin ba zan cinye".

Kafin ma ta fita shi ya shiga toilet a sittin girgiza kan ta tayi sannan ta hau gyara masa d'akin tana yi tana tunanin yaran ta da shi kadai ne namiji data haifa,yana fitowa ya zura uniform d'in sa kafin ta kawo masa breakfast har ya fito a hanya suka had'u yana zura rigar sanyi.

Tace, "Babana saurin fa?"

"Mamanah ina so mu had'u da ita ne".

"Ka tsaya kayi breakfast da waya ce ma makara".

"Mamanahhhh...."

"Babanaaaahh".

A tare suka saki dariya abin su, be lura da Abba dake parlour ba sai da yazo zai d'auki flash d'in da yasan anan ta saka wainar a ciki sannan ya kalle shi murmurshin dake fuskar sa ya k'ayata ya kalle shi tare da tsugunnawa har k'asa.

Yace, "Abba ina kwana".

"Lafiya".

Yaci gaba da latsa remote d'in sa.

Mama tace, "Bazade ka ci abinci bako?"

"Mamanah zanci fa idan naje".

"To kaci dayawa kaci sosai, Allah ya kiyaye Allah bada sa'a ya dawo min da kai lafiya".

SHAHEEDWhere stories live. Discover now