32

73 4 0
                                    

✨💫✨💫
            *SHAHEED*
                       ✨💫✨💫
*1442H/2021M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:- HIJJART ABDOUL*

*SADAUKARWA GA:-* FANS

*TUKUICI GA:-* SWEETHEART

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

 

*SHAFI NA 32📑* 

*__________📖*Yana zuwa yayi sallahn Ishan yana shigowa ana fara kira kafin ya ƙara so kuma wasu masallanta sun idar. Zama yayi a Parlour ta kawo masa ruwa da abinci tana mai murnar ganin ɗan uwan ta duk da zuwan dare yayi sai da ta gama sannan ta zauna, yayin da shi kuma ya fara bude abincin da yaci.

Tace, "Kai yanzu ka kawo min Matar taka amma shine ka wani zo min babu ita, ni wallahi nazaci tare kuke".

"To kinga ai ba tare muke ba sai kiyi shiru".

"Uhm nayi shiru kafin ka faɗo mun magana".

"Better".

Shiru sukayi sai kuma ta fara tambayar sa mutanen gida yana faɗa mata sai da suka kuma yin wani shiru lokacin ya kammala cin abincin sa.

Yace, "Ina mijin ki?"

"Ya fita Sallah be dawo ba".

"Shine ya fice ya bar min ke a gidan?"

"Kai naga tare kake tafiya da taka matar ai".

Ta faɗa yana ɗan hararan shi, murmurshi yayi mai kyau zai kuma magana aka shigo tare da sallama kallan sa Shaheed yayi shi raban sa ma dashi yana ga tun bikin su be ƙara ganin sa hakan kuma be dame shi ba, amma shi mijin nata ya san shi sosai da sosai kodan labarin sa ma da ake bashi ga kuma bugu da ƙari hotan sa dayake gani a wayar matar sa, kuma sosai Shahed ke burge shi. Da fara'ar sa ya taho hakan yasa shima tashi yaje sukayi musabaha sannan suka ƙara so tare zama sukayi.

Yace, "ya hanya? Da fatan de anan zaka kwanan ko?"

Dan sosa kai yayi bece komai ba.

Aliya tace, "bade kunya ba ko?"

Sai da ya faki idan mijin ta ya zabga mata harara.

Tace, "uhm maida wuƙar".

Murmurshi kawai Sabir yayi yana kallan su, kafin.

Yace, "Ya mutane gidan?"

"Alhamdulillah lafiya lau suke".

"Sai kuma mukaji kayi hijira".

"Idan hijira ce ma ai da sauki ɓata zaka ce yayi, ni nazaci ma kidnapping nashi akayi yana min bacci wannan yaron?"

Ajiya ta faɗa tana nuna shi da yatsa.

Sabir yace, "anya kuwa bakya bacci?"

Shaheed yace, "ai daman ban yarda ba rabu da ita so take na sheƙa taci gado".

"Me kake dashi da zanci gado, wallahi yaron nan ya mugun renani".

"Kunfi kusa".

Ya faɗa yana shan ruwan dake gaban Shaheed.

SHAHEEDWhere stories live. Discover now