24

73 6 0
                                    

✨💫✨💫
            *SHAHEED*
                       ✨💫✨💫
*1442H/2021M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:- HIJJART ABDOUL*

*SADAUKARWA GA:-* FANS

*TUKUICI GA:-* SWEETHEART

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

 

*SHAFI NA 24📑*

*__________📖* A hankali ta janye idan ta daga kan Abba jin wani irin zafi dake jikin sa har ratsa ta yake, taja hannun sa bata ce komai ba har sunje bakin ƙofa, ta juyo ta kalli Abba da ita yake kallo yana mamaki wanne wacce irin yarinya ce marar tarbiyya haka? sai kuma ta juya bata ce komai ba taji Abba.

Yace, "Irin matar da ka auro kenan?"

Tsayawa ta kuma ta kalli Shaheed da yake lumshe ido sannan ta kalli Abba sai kuma ta maida kallan ta ga ƴan ɗakin, taga babu abokan sa su kuwa tun sanda Abba ya mare shi, suka bar wurin bazasu iya ganin abinda Abba ke masa ba zuciyar su a kusa take zasu yin abinda be dace ba kuma yayi fushi dasu baza su yi ba gwara su tafi su bar masa wurin. Daman Sadiq ne ya kawo ta yana kawo ta kuma ya koma. Ganin babu wani bare yasa ta ƙara kallan Abba tayi wani irin murmurshi.

Tace, "Ban taɓa tsammatar haka daga gare ka ba Abba".

Haka kawai tace tayi gaba, tana rike da dashi, shikuwa har wani ƙara lafewa yake ta, suna fita tayi office ɗin sa dashi, cikin office ɗin ta shiga ta ajje shi a doguwar kujera tare da kwantar dashi zata tashi ya riƙe ta tana kallan ta da idan sa da yake lumshe yana buɗe wa.

Yace, "Ina zakije?"

Harara ta zabga masa, cike da masifa.
Tace, "Inda na fito zan koma".

Lumshe idan sa yayi yayi murmurshi ya kara jan hannun da ya riƙe duk da bawani riƙo yayi mata ba na kuzo mu gani dan shi de be da wani ƙarfi a yanzu haka kada jan hannun da yayi ne yasa ta ƙare wa kayan jikin sa kallo yadda sukayi squeezing sannan ta maida kallan ta gare shi.

Tace, "Dambe kayi aka maka duka ko?"

Badan be jin dadi ba, da sai ya dara Sosai sai dai hakan ma sai da yayi murmurshi sosai dan yadda tayi maganar ne yayi mugun bashi dariya wai dambe.

"Dariya ma kake".

Ta ƙara faɗa fuska a cunkune, be dena murmurshin ba ya kuma sakin wani murmurshi yana sakin hannun ta, ƙwafa tayi ta fita, Office ɗin Sadiq ta Kira shi akan yazo ya duba shi, daga nan ta fita ta samo masa abinda tasan zai iya ci ta haɗo da fruit ta dawo. Lokacin har ya sama sa drip ya fara bacci,kallan shi ta tsaya yi kafin ta ajje abinda ke hannun ta ta zauna a ƙasan carpet ɗin tana cigaba da kallan shi a hankali ta kai hannu ta fara shafa fuskar sa tana jin tausayin sa sosai, bata san sanda ƙwalla ta fara fita a idan ta tana tunanin lalle dole komai ya zo ƙarshe bazata iya juran ganin sa ba yana cigaba da zama haka ba, a hankali ta kifa kan ta a jikin shi itama bacci yayi gaba da ita.

~~~~~

Umma tace, "Ni banga komai ba dan yasa sunan sa".

Abba cike da daci rai.

Yace, "Ni nagani, ko kina san kullum nake cewa bana san shi? ada halin shine bana so amma a yanzu shi ɗin ne Bama nasan gani".

Shiru yayi yana kallan Hassana.

SHAHEEDWhere stories live. Discover now