✨💫✨💫
*SHAHEED*
✨💫✨💫
*1442H/2021M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:- HIJJART ABDOUL*
*SADAUKARWA GA:-* FANS
*TUKUICI GA:-* SWEETHEART
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*SHAFI NA 39📑*
*__________📖* Farin cikin da yake gani a fuskar ta wanda be taɓa gani ba, farin ciki ne mai tattare da wani irin nishaɗi, sai yaga ma kamar ko yaushe a cikin damuwa take amma ganin ta a haka sai yaji duk wani damuwar ta tafi. Yayin annashwar fuskar ta ke sashi nashaɗi ya koma gefe kawai yayi ya naɗe hannun sa yana kallan duk wani motsi nata yana murmurshi, kawai kallan ta yake yadda take dariya cike da farin ciki sai yaji daman duka siblings nata suna nan ina ma yana da kuɗin da zai ce dukan su su zo da ya kawu su domin su dawo da rayuwar su wacce suka bari sai dai kuma beda adadin sannu kuɗin.
Yayin da gefe kuma yana kallan Maman sa da kamar ita ce mahaifiyar ta ta domin wani irin tattalata take suna hira kamar da can sun saba sai dai ita bata wani saki jiki da ita ba sabida kunyar da take fama da ita.
Ganin dare yana yi yasa Daddy cewa.
"To ya kama ta ku tashi mu tafi haka nan kuma dare yana yi".
Kawu yace, "ko ace dare ma yayi".
Ummi ta kalli Mama.
Tace, "Hajiya mu tafi ko?"
Shaheed yace, "Mamanah anan zata kwana".
"Kamar ya anan zata kwana?"
Sunkuyar da kan sa kasa yayi bece komai ba irin abin tausayin nan, sannan ya kalli Mimi dake kallan sa jin abinda zai ce Allah Allah take yaji yace ta bisu kamar kuwa yasan me take nufi.
Yace, "Meeemeenah ki bisu kije ki kwana".
"Wanne irin ta bimu?"
Daddy ya fada.
Kawu yace, "kawai taje sai da safe".
Hakan yasa shi yin shiru duk da shima kawaici kawai dan gani yake kamar an takura sune amma tunda har ya faɗa ai shikenan.
"Fati fa?"
Ta faɗa tana kallan ta, dake bacci akan kujera.
"Ki barta kawai".
"Har ƙofa ya raka su inda sojoji ke tsaye suna faman jira kallan su yayi ganin alamar ko gajiya babu a tare dasu, ya jinjina kansa a zuciyar sa yace, "ba dole yarinya tayi gadan jarumta ba". ya faɗa yana ƙare musu kallo ganin yadda suka wani sara masa sannan aka zo aka buɗe masa ƙofa yana daga tsaye har motocin su suka wulla. "Nan da nan ma sai an tafi da securities".
Kawu yace, "Sabida tsaro".
Besan ma maganar ta fito fili ba sai da ya bashi amsa kallan sa yayi tare da murmurshi sannan suka wuce. Direct Kan cinyar Mama ya zauna yana wani jin nishaɗi da annashwa na musamman yana samun sa. Sun jima suna hira basu sukayi bacci ba sai da sukayi asuba daga can ya raka Kawu hotel shi kuma ya dawo sanda ya dawo ɗin kuwa Mama na bacci akan carpet ɗin dake ɗakin tasa pillow ta rufa da blanket, murmurshi yayi dan daman haka tace bazata hau musu gado ba sai kace wata uwar shegu Fati ce kawai akan gado . Shima kwanciya yayi a gaban ta yana ƙudundunewa a cikin bargon kamar wani ƙaramin yaro dandannan bacci ya dauke shi.
YOU ARE READING
SHAHEED
Random"Mamanah ya za'ayi ace kina fad'ar haka? kidena Mamanah bana so kinsan yarda nake ji ne? kinsan yarda naci burin rayuwa dake shine zaki kike fad'ar wanna maganar?" "Idan bata fad'i maganar da zata sa ka shiryu ba. Me kake so ta fad'a maka? idan har...