✨💫✨💫
*SHAHEED*
✨💫✨💫
*1442H/2020M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:- HIJJART ABDOUL*
*SADAUKARWA GA:-* FANS
*TUKUICI GA:-* SWEETHEART
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*SHAFI NA 12📑*
*__________📖* Sanyin da akeyi ne yasa ta farkawa kasancewar anyi ruwa, gaba ɗaya wuyan ta ya ƙage sai da ta farka ta ga mutum a jikin ta ya shiga cikin hijabin ta ya naɗe ita kuma ta takura mata, ajiyar zuciya ta sauƙe sannan ta nemi gyara kwanciyar ta sai dai kuma hakan ya gagara gashi an maido da nepa tana so ma ta tashi ta kashe wutar amma ina haka ta haƙura tasa pillow a wurin kanta wani bacci yayi gaba da ita, koda asuba ita ce ta fara tashi sai dai bata san yarda za'ayi ta tashe shi ba, yanzu kam ba laifi yana ƙoƙarin tashi da asuba duk da watarana yana makara yau de anyi sa'a ya tashi a jikin mutum ya ganshi hakan yasa shi sakar murnar shi kaɗai kafin ya fara kokawar cire hijabin gaba ɗaya ya takura mata, sai da ya cire sannan ya kalle ta.
Yace, "Shine harda su ɓoye a hijab? sai kace wani ɗan ki?"
Ya faɗa yana wani ya tsine fuskar sa, kawai kallan sa tayi kallan irin kai kasani sannan ta yin ƙura zata tashi yayi saurin danne hijabin yana miƙa irin be sani ba dawowa tayi ta zauna tana kallan sa.
Yace, "Kallan fa?"
Bakin ta kawai yaga ya motsa ya bita da kallo.
Yace, "wai ke dan Allah haka kike? aka ce maki ni malamin karame ne or what? ko kuma ca aka ce maki na iya reading lips ɗin mutane".
Ajiyar zuciya ta ajje tare da lumshe ido, ko be Faɗa ba alamar ya dame ta ne hakan, murmurshi yayi sannan ya tashi ya tafi itama tashi tayi ta tafi, yana dawowa daga sallah ɗakin ya shiga a ƙasa kuwa ya ganta hakan yasa shi zuwa inda take yana kallan ta kafin yasa hannu ya ɗaga ya ɗaura kan gadan yana nishi sosai kamar wanda ya ɗaga bahun gero.
"Tafiye nauyi, wai!"
Buɗe idan ta tayi ta kalle shi, wa kuwa waro idan sa.
Yace, "Ohh! Daman ba bacci kike ba? kika sani ɗaga ki? yarinyar nan ko?"
Ita dariya ma ya bata irin ca tace ya ɗaga ita ɗin nan.
Yace, "Ehh dole ki kalle ni mana kin samin ciwon jiki, kinsa na kwana a parlour ga sanyi ga ga ga ga ɗin ma tayi yawa".
"Ka demeni".
Ta faɗa a hankali, da muryan bacci.
"Idan nace baza kiyi baccin nan ba baza kiyi ba".
Bata san sanda ta furta.
"Sai ka hanani ai".
"Haka kika ce? na hanaki ko?"
Ɓata fuska tayi ta juya masa baya, batayi aune ba kawai ta jishi a bayan ta, ya juyo da ita.
Yace, "Maimaita".
"Kayi hakuri".
Sakin ta yayi sannan.
Yace, "Kina so na barki kiyi bacci?"
YOU ARE READING
SHAHEED
Aléatoire"Mamanah ya za'ayi ace kina fad'ar haka? kidena Mamanah bana so kinsan yarda nake ji ne? kinsan yarda naci burin rayuwa dake shine zaki kike fad'ar wanna maganar?" "Idan bata fad'i maganar da zata sa ka shiryu ba. Me kake so ta fad'a maka? idan har...