✨💫✨💫
*SHAHEED*
✨💫✨💫
*1442H/2021M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:- HIJJART ABDOUL*
*SADAUKARWA GA:-* FANS
*TUKUICI GA:-* SWEETHEART
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*SHAFI NA 22📑*
*__________📖* Shaheed kuwa takalmin ma be gama zurawa ba ya fice, tsabar sauri da ɓacin rai da kuma gudu yake driving babu abinda yafi ɓata masa rai irin rasuwar Mahaifinyar sa me yasa sai shi? anya ma kuwa ba karya yayi masa ba? dade tunani haka ya ƙara sa gida itama motar har ƙofar part ɗin su ya kai ta yana zuwa ya danna kai babu kowa a ciki bema bin ta kan da akwai mutum ba ko babu burin sa kawai yaje ɗaki, yana zuwa kuwa yayi wani irin rufda ciki ya zura ƙafar sa a ƙasa ya lumshe ido.
Mimi tana toilet tana wanka tana fitowa taga mutum ganin ya juyar da kan sa gefe sai taga kamar yana bacci ga wannan kwanciyar da ta hana shi ya ƙi hanuwa, girgiza kan ta kawai tayi ta nufi wurin sa, ta sunkuya kaɗan da niyyar cire masa takalmin sa ƙaramin towel ɗin da take tsane ruwa ne ya faɗi a kan sa hakan ya bashi tabbacin mutum na kan sa a hankali ya buɗe idan sa ya gan ta maimakon ta cire ɗayan takalmin kamar yadda ta cire ɗayan sai yaga ta tsaya kawai tana kallan wurin ita ba ida cire takalmin ba ita kuma bata bar masa ba. Kallan sa tayi kaɗan taga shima ita yake kallo, ajiyar zuciya ya sauke sannan ta wuce toilet ta ɗauko first aid box ta jawo stool ta zauna tana kallan shi ganin haka yasa shi tashi zaune yana kallan ta.
"A'ina kaji ciwo?"
Rufe idan sa yayi ya buɗe, dan wani irin azabar ciwo kai yake ji.
"Tambayar ka fa nake".
Kallan ta yayi irin ba wasan nan, hakan yasa shi shanye duk wani abu daya maƙure masa maƙoshi.
Yace, "tunda ba zuwa za'ayi a ramin ba, ba shikenan ba?"
"Ina tambayar ka kana min wani magana?"
"Ai ba ramin ɗin ba zakiyi".
"Kana gani fa kwalba ka taka fa".
"Idan kuma dole aka min fa".
"Kana baƙar zuciya de kaje ka taka tunda ai ko takalmin baka gama sawa ba ka taho".
Kallan ta kawai yake yadda take masa faɗa kamar wata Maman sa wato ma har tasan yana da zuciya, gashi ita faɗan ma ba shi take kallo ba ciwon take kallo tana nuna wa da yatsa, be san ya akayi wani irin ya kwace masa ba, haɗa idan da sukayi ne yasa shi saurin gimtse dariyan sa, harara ga wulla masa.
Tace, "dariya ma kake ko?"
Girgiza kan sa yayi yana gimtse dariyan sa, ƙwafa tayi ta maida kan ta ga ciwon sai da ta cire kwalban sannan ta yi masa dressing wurin, sai dai tana yi tana tsoron taɓa wa amma data kalle shi taga alamar dariya sai kuma ta ƙara gimtse fuska a haka aka gama, tana gamawa ta zura hijabi ta fita sai ganin ta yayi da Plate ɗin abinci tun daga nesa ya fara mata kallan nifa bance zanci abinci ba, bata kula shi ba ta matso kusa da shi ta tamke fuska tamau tare da ɗaukowa a spoon ta nufi bakin sa.
YOU ARE READING
SHAHEED
Diversos"Mamanah ya za'ayi ace kina fad'ar haka? kidena Mamanah bana so kinsan yarda nake ji ne? kinsan yarda naci burin rayuwa dake shine zaki kike fad'ar wanna maganar?" "Idan bata fad'i maganar da zata sa ka shiryu ba. Me kake so ta fad'a maka? idan har...