31

74 7 1
                                    

✨💫✨💫
            *SHAHEED*
                       ✨💫✨💫
*1442H/2021M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:- HIJJART ABDOUL*

*SADAUKARWA GA:-* FANS

*TUKUICI GA:-* SWEETHEART

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

 

*SHAFI NA 31📑* 

*__________📖* Kwanciya yayi yana hango ta daga kan gadan har bacci ya ɗauke shi kamar yarda ya ɗauke ta, basu suka tashi ba sai 10 koda suka tashi gani sukayi an ajje musu abincin su ganin haka yasa ta saukowa ta fara cin abincin ba wanke baki bare kuma brush haka kawai ta hau cin abincin ta, hankali kwance kuwa.

Kallan ikon Allah kawai yake wato ita ko a jikin ta ma ɓatan da yayi kenan ko? shi yana can yana kasa cin abinci amma ita ashe cin abincin ta take hankali kwance, duk da yaji ba dadi amma be nuna ba tunda de yasa shine da laifi, besan ita ma ba cin abincin take ba ganin shine yasa ta dawowa normal duk da tana fushi da shi kuma tasan fushin da take yi dashi dan yazo ya bata hakuri ne da be bata hakuri ba da kuma ace be zo ba to bazata iya sukuni ba.

Tana cikin cin abincin ta taji an dauke plate ɗin da cup cuno baki tayi tare da haɗe fuska tamau ta zabga masa harara, marairaicu fuska yayi.

Yace, "am sorry Minneerah".

Rufe ido tayi tana tuno farkon haduwar su. Ƙara hararan sa tayi zata kuma zuba wani abinci. Yayi saurin dauke flask ɗin.

Yace, "Haba mana ina ta baki hakuri ina ta baki hakuri ina ta baki hakuri ina ta yi amma sam baki hakura ba, kin ga Manzon Allah yana san masu hakuri kuma kinga Allah yana tare da masu hakuri kuma ma kin sa wani abu? na faɗa maki da bakya nan nayi ta tunanin ki amma ke ko tuna ni bakiyi ba shine kika zauna har da cin abinci kuma ma ni ina naje ni naga wata yarinya mai tsabta ba irin ki ba me ƙazanta daga tashi daga bacci kice zaki ci wani abinci kinga ki dena abin da kike nidai na baki hakuri ki hakura kawai shine mafita ato kuma ma ko..."

Kallan da yaga yana an tayo masa ne yasa shi sakin wani irin murmurshin yaƙe ya fara sosa ƙeya.

Yace, "To yanzu de kinga nima yunwa nake ji kiyi hakuri muci tare ko?"

Ƙara haɗe fuska tayi tana siɗe hannun ta dan ji tayi abincin ya mata daɗi na musamman sosai ya mata daɗi barin ma dan romo data ta fara sha, gashi yazo ya ɗauke mata ya rage mata jin daɗi.

"Meeemeenah".

"Magana fa nake, Haba Minneerah naaaaaaahhhh".

"Munneerah".

Ta faɗa tana gyara masa duk da tasan ba faɗa ba zaiyi sai dai ma ya kara batawa.

"Ohhhh! Ashe fa Monneerah".

"I SAID MUNNEERAH".

Ta faɗa da tsawa tsawa, sosa ƙeya yayi.

Yace, "Ohhh! Manneeerraaahh, Yes na faɗa daidai babu mistake haka ne ko? Manneeerraaahh yo Ashe ba Minneerahn bane ba".

Harara ta ɓalla masa.

Tace, "bani abinci na naci".

"To kice kin hakura".

SHAHEEDWhere stories live. Discover now