25

71 5 0
                                    

✨💫✨💫
*SHAHEED*
✨💫✨💫
*1442H/2021M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:- HIJJART ABDOUL*

*SADAUKARWA GA:-* FANS

*TUKUICI GA:-* SWEETHEART

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 25📑*

*__________📖* Shaheed kuwa airport ya wuce dan sam be ga amfanin zaman sa a nan ba, idan har bazata iya faɗa masa wacece ita ba ya jima jikin sa na bashi cewan Minneerahn sa ce, shiyasa karan farko yana ganin ta yaga kamar ya san ta, wacce yake nema tana kusa dashi, kusanci mafi girma amma be sani, ba ita ce kuma ta bashi shawaran zuwa yaje ko zai same ta. Amma batayi trusting ɗin shi ba tunda har zata ɓoye masa sunan ta bayan wanda iyayen ta suka mata.

A hankali ya jinginar da kan sa a jikin kujeran da yake kai kafin ya tashi ya fito dan be taho da komai ba bare kuma ya shiga ciki yana fitowa yaga mai adaidaitan da ya kawo shi hawa kawai yayi bece masa ƙala ba, shima ganin yanayin sa yasa shi ƙin tafiya ya jira shi dan kuwa shima mutumin sa ne, tambayar duniyar nan yayi masa amma be bashi amsa ba haka ya haƙura ya rabu da shi, inda zai kaishi ma wannan karan be faɗa ba, be zarce ko ina ba shi kuwa inda su Babba suke kwana ganin haka yasa shi ce masa.

"Ba nan ba".

Hakan yasa shi juya adaidaitan sa ya tafi gida yayi parking a ƙofar gidan su.

Yace, "Idan kaga dama ka fito idan baka gani ba ka mutu anan ba ruwana".

Sabida iya ƙuluwa ya ƙulu, ganin haka yasa Shaheed bin bayan sa ya shiga ɗakin sa dake zauren gidan shi kuma ya wuce cikin gida.

Kwanciya yayi yana kallan fankar dake ɗakin, shi kan sa be san tunanin da yake ba kawai de yasan yana hango ta ne a cikin idan sa daga nan kuma be sani ba sabida abubuwan sun masa yawa duk shi kaɗai a ƙwaƙwalwa, a cikin lokaci ƙanƙani sai ciwon kai daman gashi ba wani gama warkewa yayi ba ƙarfin hali ne kawai irin nasa da kuma ganin cewan ta damu dashi ga wani irin zogi da ƙafar sa ke yi tun ƙwalban da ya taka da tayi masa dressing ya tashi ya ɗaure sabgar sa da zata sake ma guduwa yayi wai ta warke bata kula shi sai dai da safe ya tashi ya ga ta sake masa dressing ɗin wurin amma hakan ba zai hana shi taka ƙafar ko zama a gida wayon sa ke zuba wa san sa abin sa, to yau ji yayi jin wurin yayi yayi masa zafi dayawa ga zafin da jikin sa ke yi ga ciwon kai ga zafin ciwo uwa uba ga kuma zafin da zuciyar sa ke masa, babu abinda yake ɗaga shi daga inda yake sai shiga toilet da yin Sallah be taɓa tunanin akwai abinda zai hana shi cin abinci ba sai gashi yau sam bama yasan cin abinci sabida tururin da zuciyar sa ke masa.

~~~~~~

Mimi kuwa bayan ɗakin su ta tafi inda suka taɓa zama sanda yayi mata tsawa anan ta zube ta kwanta tun tana yin kuka mai ƙarfi har ta dawo kuka da shashsheka ce kawai sai hawayen da suka ƙi daina zuba, gashi ta ƙudundune a wuri ɗaya tana faman abu ɗaya, kukan da ta keyi ne ya harda ta sa mata ciwon kai da zazzaɓi gashi kuma ba ita kaɗai bace ba, jinin dake zuba a kan ta kuwa tuni yayi zubar sa ya gama ya bushe duk ya ɓata mata kaya bata san ma yana yi ba, abinda ta sani shine Jasin ɗin ta yayi fushi da ita.

Sadiq yace, "Ba naje na dubo shi ko zan gan shi".

Girgiza masa kai tayi alamar kada yaje, ya wuce gida kawai.

SHAHEEDWhere stories live. Discover now