5

114 6 0
                                    

✨💫✨💫
          *SHAHEED*
             ✨💫✨💫
             *1442H/2020M.*
             *1NOV/SAFAR15*
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*

*SADAUKARWA GA:-*

*TUKUICI GA:-*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

https://my.w.tt/3eo3ijuMybb

*SHAFI NA 5📑*

*________ 📖*  Share masa hawayen sa tayi, bata san ganin sa cikin wannan halin tana san duk wani abu da zai faran tawa yaran ta rai batare tunanin komai ba batare da tunanin abinda zai je ya dawo ba batare da kuma tunanin cewan Abban sa baya san halin shi ba ta yanke hukunci da kanta kawai abinda bata so shine wannan kwantatacciyar damuwar da tagani a kwance a fuskar sa ce bata son gani tafi san kullum ganin sa cikin farin ciki da walwala shine burin ta.

A hankali tasa k'ara share masa hawayen da yazo a fuskar sa ya sakar masa murmurshin kwantar da hankali.

Tace, "In Sha Allah zan biya maka kaje kayi karatu acan fatana Allah ya had'a ku da ita".

Ta fad'a tana k'ara share masa hawayen sa, tare da kwantar da kansa a cinyar ta yana kuka sosai mai tsuma zuciya ya kasa furta koda kalma daya ce bare ya furta mata kalmar godiya.

Abba da yazo tambayar inda ta ajje masa wasu takardun sa na kasuwa dayayi lissafi dan har yaje ya manta gashi kuma Ibrahim baya nan bare ya aike shi yara kuma yasan kowa ya kama gaban sa hakan yasa shi dawowa furucin sa da nata na k'arshe yaji kawai dan haka a hankali ya tako ya zauna a kujera batare da sun san ya shigo ba, cikin wata dakakkiyar muryan da take nuna gargad'i, b'acin rai da kuma tsantsar fad'a.

Yace, "Muddin kika biya masa ya tafi wani waje yayi karatu to k'arshen zamana dake ya k'are bawa ke ba koda ace wani naki ne kuwa yayi hakan kuma ki zuba ki gani".

Be jira cewar su ba ya tashi har yaje bakin k'ofa ya juyo.

Yace, "kizo ki d'auko min abinda kika canzawa wuri".

A tare zuciyar su ta buga daga shi har ita ya manta da cewa Mahaifin sa baya san shi, da bazai taba yin wannan maganar ba gashi sanadiyyar shi zata rasa auren ta sabida shi. Mama kuwa ji tayi wani kuka na k'wace mata sosai idan ta ya cika da k'walla a hankali ta ajje kan sa sannan ta tashi tabi bayan sa, tana zuwa parlourn sa ta shiga d'aki ta d'auko ta bashi ganin yana Parlour a zaune karb'a yayi yana k'ara dubawa ita kuma tasa kai zata fice.

Yace, "na fad'a maki idan kuma san d'anki ya rufe maki ido kije kiyi ta bauta masa tunda ni ban isa dake ba".

Hawayen da take mak'alewa ne ya zubo idan ta batare da ta juyo ba.

Tace, "Da'ace shawara ka bani to tabbas zan tsallake ba na karb'i yaro na amma umarni ne ka bani bazanyi hakan ba".

Tasa kai ta wuce, mamaki sosai ya fito a fuskar sa koda labari yaji ko mafarki aka ce zata iya maida masa magana bazai yarda ba zaiyi saurin k'aryatawa ne yace mafarki ba gaskiya ba haka kuma yace Dan Adam yana k'arya za'ata ita iyuwa k'arya ake mata amma yau itace take cewa da'ace shawara ya bata zata iya tsallake shi fa ta tafi to ya godiyawa Allah da Umarni ya bata amma kuma idan ta tafin ba? ko ta biya masa? hakan yana nufin ta zabi d'an ta fiye dashi ne.

SHAHEEDWhere stories live. Discover now