✨💫✨💫
*SHAHEED*
✨💫✨💫
*1442H/2021M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:- HIJJART ABDOUL*
*SADAUKARWA GA:-* FANS
*TUKUICI GA:-* SWEETHEART
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*SHAFI NA 26📑* Shaheed kam ba ƙara dan marin ya shige shi ko kaɗan, gashi yana ganin Abba ba sauƙi. Cike da zafin ran da yasan Abba yana da shi sai dai na yau yafi na kullum dan harda wasu irin rikitattun kallo yake watsa masa.
Yace, "Yaya ina ka tafi? Ina ka tafi Yaya? kasan baka san yarinyar mutane ka aurota? ance maka auren hauka ne?"
Yarda ya daka masa tsawa yasa Shaheed tsayawa cak yana kallan Abban, yadda yake masifa yana nuna inda Mimi take.
"Ka tafi kwana da kwanaki baka gida".
"Kabar mutane da a cikin kewa da tashin hankali dan ka rena mu, musamman ma ita".
"Abbaaaaaahhh".
Shaheed ya faɗa hawaye na zubo masa.
"Kar..."
Be ƙarasa abinda zai faɗa ba sakamakon wata irin wawar runguma da Shaheed yayi masa, tuni hawayen idan sa yayi hawaye kuka yake sosai bilhaƙƙi da gaskiya ya kuma rungume Abba sosai, zare glass ɗin sa Abba yayi tare da share abinda yaji idan sa na zubowa kafin a hankali yasa hannu ya shiga bubbuga bayan sa yana yi yana kallan hannun sa is like irin am I the one din nan?
Gaba ɗayan su kowa kallan sa suke, kowa da abinda yake saƙawa a ran sa. Sai da yayi kukan mai isar sa, sannan ya sake shi yana kallan sa bayan ya riƙe masa hannu yana kallan sa da hawaye shabe shabe a fuskar sa yana murmurshi tsantsan farin ciki zaka ga gano a cikin idan sa wanda har ya nuna a fuskar sa duk da yana kuka yana kuma murmurshi sai dai su sun san murmurshin sa ko wanne hali ake ciki zai iya sakar murmurshin sa ba ruwan sa hakan yasa basa gane wanne irin emotion yake ciki.
"Abba kana sona daman?"
Hannun sa ya zare daga cikin nasa guda ɗaya ya bashi ƙaramin mari.
Yace, "Ka taɓa ganin uban da be san yaran sa?"
Murmurshi Shaheed ya kuma yi hawaye na zubo masa ya riƙe hannun sa.
Yace, "Abba kayi hakuri da duk abinda nayi Abba wallahi ni ba mutumin banza ne ba Abba Abba Please try to understand me Abba".
"Abba..."
Rungume shi Abban yayi tare da fara shafa kan sa cike da kulawa, shima ƙanƙame shi Shaheed ɗin yayi yana sakin kuka sun jima a haka har sai da Abba yaji Shaheed ya dena kukan ya dawo ajiyar zuciya kuma ya sake shi suka zauna, tare ɗaura kan shi a kafadar sa.
Umma tace, "Abban Sagir?"
Ta tambaya kamar irin dagaske ne? Kallan ta Abba yayi sannan ya maida kallan sa ga duk mutanen wajen yaga sai kallan sa.
Yace, "Ni ake gani ko kuma shi ake gani? idan nine a dena kallo shi ɗin ma a dena kallan sa".
"Ikon Allah".
YOU ARE READING
SHAHEED
Random"Mamanah ya za'ayi ace kina fad'ar haka? kidena Mamanah bana so kinsan yarda nake ji ne? kinsan yarda naci burin rayuwa dake shine zaki kike fad'ar wanna maganar?" "Idan bata fad'i maganar da zata sa ka shiryu ba. Me kake so ta fad'a maka? idan har...