9

71 5 0
                                    

✨💫✨💫
          *SHAHEED*
                  ✨💫✨💫
             *1442H/2020M.*
             *1NOV/SAFAR15*
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-HIJJART ABDOUL*

*SADAUKARWA GA:- FANS*

*TUKUICI GA:- SWEETHEART*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

https://my.w.tt/3eo3ijuMybb

*SHAFI NA 9📑*
  

*__________📖* Sai dai kuma sam ya kasa ƙara sawa kusa da ita ƙafar sa yaji tana wani irin sanyi ji yayi kamar zai faɗi sakamakon fuskar sa da ya gani a hankali ya kai har gaban gadan yana sauke ajiyar zuciya akai akai kafin ya lumshe ido ya buɗe akan ta, lokacin ta buɗe idan ta tana kallan shi, murmurshin yaƙe ya sakar mata sannan ya taimaka mata ta tashi ganin tana neman tashi ya zauna a gefen ta yana cigaba da murmurshi, murya a sanyaye.

Yace, "Ya sunan ki?"

Kamar bata so fuskar ta a haɗe.

Tace, "Munneerah Umar Nasir".

Murmurshin takaici yayi sannan ya shafi fuskar ta.

Yace, "shekaran ta ki nawa?"

Sai da ta yatsine fuska.

Tace, "am 7".

Murmurshin ya kuma yi.

Tace, "kaine zaka min aikin da aka ce idan aka min zan sami lafiya?"

"Ehh nine".

Ya fad'a da murmurshi a fuskar sa.

Tace, "Shine kake dariya ko?"

Wannan karan ta bashi dariya tun daga zuciyar sa, duk da wani iri yake ji amma da tayi wannan maganar sai da yaji daɗi.

Yace, "Ai babu abinda zai faru in Sha Allah, kiyi addu'a kinji ko?"

"Ni bana so".

"Kinga Maman ki na so ki sami lafiya".

"Ba Mama nake cewa ba Ummi nake cewa".

Wato de duk wata Munneerah tana da surutu Munneerah uku kenan, yana san duk masu sunan sabida Munneerahn sa, sosai yayi murmurshi.

Yace, "Kina so ki zama ƙawata?"

Sai da ta kalle shi.

Tace, "Zaka kawo min cookies?"

"Ehh zan kawo maki kuma zan kawo maki friend".

"Dagaske?"

Ta faɗa tana murmurshi, murmurshin da tayi sai yaga kamar Munneerah sabida munafikin  dimple ɗin da ya loma irin na Minneerahn shi hakan yasa shi ƙara jin wani iri gami da kewar ta ta taso masa, acikin second ɗaya farin cikin da ya yaji na kasancewa da Munneerah Nasir sai ya zama ya ɓace abin da yaji da farko ya dawo masa, yaƙen murmurshi kawai yake yi shi kaɗai yana kallan ta.

Yace, "Eh dagaske, itama sunan ta Munneerah".

"Should I say thanks?"

Ta faɗa tana murmurshi murmurshi dariya dariya ta alamar taji dadi tana kuma miƙa hannun ta marar carnular.

SHAHEEDWhere stories live. Discover now