20

88 5 0
                                    

✨💫✨💫
            *SHAHEED*
                       ✨💫✨💫
*1442H/2021M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:- HIJJART ABDOUL*

*SADAUKARWA GA:-* FANS

*TUKUICI GA:-* SWEETHEART

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

   

*SHAFI NA 20📑*

*__________📖* "Kamar yadda kasani mu ƴan Adamawa mahaifin mu bafulatani yayin da mahaifiyar mu ta kasance banufiya, mun taso bama iya faɗar fulatanci amma muna ji sosai sai ɗan abinda ba'a rasa ba mahaiyar mu kuma bata mana Yaren su sabida tana ganin cewan Mahaifin su ba banufe bane akan me to zata mana haka de muka taso abin mu cikin so da ƙauna har muka fara Makaranta kasancewar Baban mu ɗan kasuwa ne hakan yasa Yayun mu ke binsa kasuwa wani lokacin ma daga can suke wuce wa. Ranar da su Asma'u suka zo ga gidan mu ga gidan su gidan mu suka fara shigowa anan muka saba da su, su kuma su biyu ne a wurin Maman su ita da ƙauwar ta, dani da ita ba sa'anni bane sannan ba sa'ar Yaya ta bace sai dai mutuncin dake tsakanin mu da ita sosai hakan yasa muka fi shaƙuwa da ita yayin da Yaya ta Zaliha suka fi sabawa da ƙauwar ta Saratu alaƙar mu sosai ta ƙullu fiye da tunanin mai tunani gashi makarantar mu ɗaya sai ya zamana kamar gidan mu ɗaya dasu ko wasu ƴan uwa na kusa, Yaya ta bata cigaba ba aka mata aure, sanda na gama nace zanci gaba da karatu Mahaifin mu kuwa ya yadda duk da sai da aka kai ruwa rana sannan Hajja Mahaifiyar mu ta yadda ya nema min Zaria nake yi duk hutu ina zuwa gida har nayi shekara ɗaya lokacin Asma'u ta gama itama tace inda nake zatayi sai dai ita nata mahaifin ne be yadda ba akayi akayi yace a'a fa idan baza tayi anan ba ta bar karatun tayi aure ai ba dole bane, sai da Mahaifin mu ya same shi yayi bayanin sannan ya yadda shine muka taho makaranta tare, tana level one ina level two".

Shiru tayi tare da goge ƙwallan dake zubo mata, jin tayi shiru yasa shi ɗagowa ya kalle ta, ta sakar masa murmurshi.

Yace, "wannan labarin na ɗan san wani ni bashi nake so ba".

Ya faɗa yana turɓune fuskar sa, doke masa ƙeya tayi.

Tace, "ina kai ne ai, idan baka san ji na mayar da abuna".

"A'a ina so mana".

Ya faɗa yana sake kwanciya a cinyar tare da maƙale ta, ci-gaba da shafa kan sa nasa tayi.

Tace, "Ranar da muka zo a tasha a ranar muka haɗo Bashir Baban Tijjani kenan".

         

     

           LABARI 

ZARIA.

Bashir ne zaune ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya a bench yana zaune yana ganin kowa hanci a ɗage yana wani hurhurawa hango mata biyu da yayi tubarakallah yasa shi sauƙe ƙafa ɗaya yana kallan su ganin sun jan kaya zasu fita daga tashar yasa shi saurin tashi ya nufi wurin su cike da yaƙe baki.

Yace, "ƴan mata da kun kawo na taya ku".

Fa'iza tace, "a'a mungode sosai taxi zamu ɗauka".

Ta faɗa suna wucewa.

Yace, "a'a baza'ayi haka ba kude kawo na taya ku ko nan da bakin titi ne sai ku hau taxi ɗin".

Asma'u tace, "munce maka fa bama so mungode sosai".

SHAHEEDWhere stories live. Discover now