28

68 7 0
                                    

✨💫✨💫
*SHAHEED*
✨💫✨💫
*1442H/2021M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:- HIJJART ABDOUL*

*SADAUKARWA GA:-* FANS

*TUKUICI GA:-* SWEETHEART

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

Ina Yaya al'ummar musulmi Murnar yin Sallah lafiya Allah ya maimaita mana Allah ya jikan wanda suka rigamu gidan gaskiya ya kai rahama kabarin su. Allah yasa mu cika da kyau da Imani. Ameen ya Allah 🙏
Allah ya dawo damu zamu ɗaura daga inda muka tsaya.

Naga duka comments naku musamman Queen Abeedatu Shaheed yana gaida ki sosai da sosai yace kuma yayi missing naki sosai da sosai amma kada Minneerah taji 🤭 to nima de ba ruwa na a ciki.
Love You all 😘



*SHAFI NA 28📑*



*__________📖* Tunda suka dawo suke faman jiran ta, ta dawo amma shiru sunci abinci sunyi sallah sunyi wanka fir suka ƙin kwanciya bacci hakan yasa kowa ya ɗauko assignment nasa tana kallan kowa yayin da ita kuma take tunanin inda Ummi ta tafi bata dawo ba, sai ga Jahshin an kawo mata shi yana kuka daga gidan renon da ta kai shi bayan gidan su babu nisa nan take kai shi idan zata fita.
Goya shi tayi yayi bacci taje kwantar dashi kenan taji ana danna door bell hakan yasa ta tasowa tasan de ba Ummi bace tana fitowa daga ɗaki Ameer yazo da gudun shi.

Yace, "Kinga ana dannawa mun leƙa munga mutane dayawa ne".

"Dayawa kuma?"

"Ehh to ai ta ƙasan nan inda mage ke shigowar nan ta nan nida Ameera muka leƙa muka ga ƙafan mutane dayawa".

Kallan shi sai kuma ta ƙara saurin tafiyar nata taje ta buɗe a hankali ta buɗe ƙofar ko kaɗan gaban ta ne faɗi ba ganin sojoji haka a gaban ta sai ma murmurshi da ta ɗaura fuskar ta, shima wanda yake gaba murmurshin yayi mata.

Yace, "Maman ki nasan ganin ku".

Da murmurshi a fuskar ta.

Tace, "tana ina?"

"Military".

"With our Dad?"

Wani murmurshin yayi mata mai kyau tare da girgiza mata kai alamar bansani ba. juyowa tayi ta kalli Ameera.

Tace, "ɗauko min vail ɗin ki zamu fita".

Tura baki tayi gaba.

Tace, "Ni a haka zan fita kinga fa da hula a kai na".

"Ni makauniya ce ai banga hulan ba nace kije ki ɗauko".

Ta faɗa mata tana zabga mata harara, sum sum ta wuce taje ta ɗauko ta dawo suka fita. Buɗe musu ƙofa akayi suka shiga motar da aka ware domin su, taje zata shiga, mutumin da yayi mata magana.

Yace, "ki sauke shi".

Juyowa tayi ta kalle shi jin Hausa sosai a bakin sa, murmurshi yayi mata kawai bece komai ba, batayi musu ba ta sauke shi ya karɓe shi ya riƙe shi ta zaci zai bata data shiga sai kuma taga ya shiga wata motar daban dake bayan su, babu wanda ya kawo komai a unguwar bare kuma daman ansan cewan Baban ta sojanne ko ma ba soja bane su ba ruwan su kowa harkar gaban sa yake.

SHAHEEDWhere stories live. Discover now