✨💫✨💫
*SHAHEED*
✨💫✨💫
*1442H/2021M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:- HIJJART ABDOUL*
*SADAUKARWA GA:-* FANS
*TUKUICI GA:-* SWEETHEART
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*SHAFI NA 18📑*
*__________📖* Suna zaune suna hiran su a bayan part ɗin su, su biyu suna mul-mula ƙullisuwa ita da Khadijah duk da cewan ita kaɗai ce kawai take hiran nata kawai ɗaga kaine da murmurshin da girgiza kai shine kawai amma a haka suke ganin cewan hira suke dan jarida dariya ake yi, Hassana ce tazo wucewa tana tattaka ƙafar ta takan yi idan bata fita ba yau ma jin ta gaji da zama kuma tayi karatun tana san ta ta huta yasa ta fitowa ganin su da tayi yasa ta ƙarasa wurin su tare da jan kujera guda ɗaya bayan ta musu sallama.
"Ina wuni?"
Mimi ta gaida ta.
"Rufa min asiri kada mijin ki yaji kina gaida ni".
"Dalili?"
"Ya girmeni yake cewa dukda de bansan wane yafi wani ba nida shi amma ina tunanin na fishi".
Murmurshi tayi kawai.
Hassana tace, "kinga kece Yaaya bani ba nice zan gaida ki".
"Shi kika fi bani ba dan ni Yaaya zanke ce maki".
"Taab dakwa kin haɗa faɗa ai rigimamman mijin naki?"
"Shi ina ruwan sa to?"
"Wannan ai komai da ruwan sa Sarkin kanzagi kenan".
"Idan yazo ki gwada faɗa kiji yadda za'a kwashe da shi".
"Shi ɗin?"
"Kina mamaki ne? kinga Yaya Khadijah nan fa Yayar sa ce fa amma ƙarfi da yaji ta koma ƙauwa".
Ware ido tayi tana kallan Khadijah ta gyaɗa mata kai alamar tabbatar wa.
Tace, "kinsa naji kunya, kiyi hakuri wallahi bansani ba".
Girgiza mata kai tayi alamar bakomai.
"Yaaya Khadijah.."
Ware ido tayi jin wani Yaaya data laƙaba mata.
Tace, "aikuwa haka zanke ce maki".
Hassana tace, "Kina wasa ne yanzun zaki ja mana magana a wurin wannan mutumin ba kunya ce ta ishe shi ba".
"Ke Hassana tunda daga can nake jiyo muryan ki kinzo kin sami mata a tsakiya kina koya mata surutu".
Kallan sa dukan su sukayi yana daga can amma dan neman magana yake magana ita kuwa ko ta ɗaga murya taya muryan ta zata kai har haka, kafin ya ƙaraso.
Hassana tace, "Wannan yaran ko? ya rena ni".
"Aikuwa zaiji wannan".
kafin tayi magana ya ƙara so ya shima yaja kujera ya zauna kusa da matar sa.
Yace, "Kin wuni lafiya?"
Ya faɗa yana kallan Mimi bataje ga bashi amsa ba Hassana tayi saurin cewa.
YOU ARE READING
SHAHEED
Random"Mamanah ya za'ayi ace kina fad'ar haka? kidena Mamanah bana so kinsan yarda nake ji ne? kinsan yarda naci burin rayuwa dake shine zaki kike fad'ar wanna maganar?" "Idan bata fad'i maganar da zata sa ka shiryu ba. Me kake so ta fad'a maka? idan har...