✨💫✨💫
*SHAHEED*
✨💫✨💫
*1442H/2020M.*
*1NOV/SAFAR15*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-HIJJART ABDOUL*
*SADAUKARWA GA:- FANS*
*TUKUICI GA:- SWEETHEART*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*https://my.w.tt/3eo3ijuMybb
*SHAFI NA 6📑*
*________ 📖* A hankali ya fara tuna wani abu sanda tazo gida tana exams idan zata tafi kamar bata so sai yana mata tsiya sab'anin siblings nasa sa idan suka zo bama sa so su kwana sabida suna k'aunar mijin su amma ita da zaran ance weekend d'in nan tayi to jikin ta har b'ari yake haka ma last zuwan da tayi ya tuna sanda zata tafi.
Yace, "Wai ke Sweetie duk karatun ne yasa ki ramewa kome?"
Murmurshi tayi masa kawai.
Tace, "Da karatu da kuma fargaban abinda zai je ya dawo".
"Ke kika sani ke kam baki da aiki sai wani fargaba ni kinga nayi nan Allah ya kiyaye hanya".
Tace, "Sweetie bazaka tsaya ba kaji maganar da zamuyi?"
"Yaudara zakiyi tunda kika ce haka cuta ce zalla zaki min".
Ya fad'a yana juyo bayan sa yana tafiya da baya da baya kafin ya juya ya manna gudu yana jin ta ta biyo shi amma kafin ta kama shi har fice a lokacin besan meke damun ta..."
Be gama tunanin sa ba sakamakon abinda 'yar aikin yaji tana fad'a.
"Kullum sai ya dake ta, musamman ace tayi laifi koda duka yake mata na tashin hankali dukan da tunda nake ban tab'a ganin anyiwa koda dabba bane bare kuma mutum d'an adam kuma ma ace matar sa tsoron sa take ji bata so ace taji sallamar sa ma bare kuma ya mata magana, maganar sa tsawa ce baya magana cikin sauki sai tsawa..."
Wani banza kallo ya wurga mata hakan yasa ta yin shiru, muryan sa cike da b'acin rai.
Yace, "Kin iya magana haka, amma baki iya zuwa ki Kai shi gaba ba".
"Mahaifin sa baya san laifin sa, kuma yamin gargad'i da cewan duk sanda na fad'awa wani nima irin abinda zai min kenan, ina tsoron na fad'awa wani na rasa aiki na".
"Meyasa kika fad'a min yanzu".
"Kaine Shaheed naga hotan ka a wurin ta tana yawan bani labarin ka".
Tsaki yaja ya maida kallan sa gare su, har yanzu be dena dukan ta ba sai dai yanzu baya gano ta sabida ta lafe a jikin lungun kujera sai ihun ta da yaje ji da kukan ta mai cike da tausayi, shikuma sai zabgar ta yake a hankali ya k'araso parlourn idan sa akan Mijin nata.
Hannu yasa ya d'aga ta, yana kallan ta cak Mijin ya tsaya yana bin hannun da kallo yana huci har ya sauke shi fes a kan Shaheed, Hassana ma hannun tabi da kallo tana cigaba da kuka ta sauke su a kan Shaheed, Shaheed kuwa yana d'aga ta beyi wata wata ba ya kifa mata mari yana mata wani iri kallo da mamaki mijin yake kallan sa haka ma 'yar aikin da ta saki baki tana kallan ikon Allah, Hassana bata ji mamaki ba tasan zai iya haka ma dan haka kanta ta saukar k'asa ta dafe wurin da ya mareta k'wallar na zuba a idan ta ga wata year zufa da ta had'a kai ba d'ankwali tayi wani wujiga wujiga da ita, kallan Shaheed yake ran sa ya b'aci sosai.
YOU ARE READING
SHAHEED
Random"Mamanah ya za'ayi ace kina fad'ar haka? kidena Mamanah bana so kinsan yarda nake ji ne? kinsan yarda naci burin rayuwa dake shine zaki kike fad'ar wanna maganar?" "Idan bata fad'i maganar da zata sa ka shiryu ba. Me kake so ta fad'a maka? idan har...