40

180 6 0
                                    

✨💫✨💫
*SHAHEED*
✨💫✨💫
*1442H/2021M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:- HIJJART ABDOUL*

*SADAUKARWA GA:-* FANS

*TUKUICI GA:-* SWEETHEART

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 40📑*

*__________📖* NIGERIA.

Shima Sagir hakura yayi ya tafi amma zuciyar sa be so ba, ace duk jiran da sukayi basu zo ba, to ko de sai gobe zasu zo? wannan tunanin da yayi ne yasa shi tafiya, koda yaje gida dariya sukayi masa sosai akan ai da ya kwana a can.

Da asuba jirgin su ya sauka, Sabir da yasan da zuwan su shine ya ɗauke su yayin da suke kallan ko ina da komai ya canza musamman Kawu da yake gani garin kamar ba garin da yasani ba komai ya zama sabo a gare shi ga wani irin cika daya ga garin yayi masa, sosai yake ji wata irin nutsuwa na ratsa shi sai kuma ya tuna da matar sa, ya saki wani lallausan murmurshi daya tuna farkon haɗursu. Sai da aka fara kai su Daddy nasu gidan da aka zuba wasu securities na tashin hankalin fiye dana farko sanda yana nan domin wannan kullum wasu zasu ke zama anan sannan kuma wasu zasu ke bin sa da na gadin yaran sa ga wasu motoci suma da aka ajje masa ko na meye oho. Gidan an gyara shi amma ba'a wani sake kayan dake cikin sa ba kawai ƙura aka kaɗe aka gyara share aka gyara ko ina ko ina tsab kamar da mutane a ciki.

Su Mama kuwa suna zuwa Abba su Abba na dawowa daga masallaci da wani irin uban gudu Sagir yayi kan Mama ya rungume ta saura ƙiris su fadi ƙasa Allah ya rufa asiri, ihun da Sagir yayi ne yasa su Hassana da Khadijah suma fitowa da gudu sukayi kan ta suma suka rungume ta itama Umma kasa haƙuri tayi taje akayi group hug din da ita suna ta murna abun su, yayin da Abba ya rungume ɗan uwan sa, sai hawaye kuma ya share yana kallan sa, murmurshin yayi masa tare da girgiza masa kai sannan suka sake rungume juna, Sabir komawa gefe yayi yana yiwa Aliya video dan jiya da suka koma bata jin daɗi bama tasan ya fito ba dan masallaci sukayi da ita zai tafi, wato shine ya taho. Sai kiran ta yayi yace ta kunna data daga haka ya kashe wayar sa ya masa ta a plane mood dan kada ta kira shi. Yayin da yake tsaye yana kallan su yana murmurshi.

Ibrahim kuwa kasa zuwa yayi wurin Baban nasa kan sa a sunkuye ƙwalla na neman zubo masa, sai shine ya ƙara sa wurin sa ya rungume ɗan sa dan yasan babu inda ya rabo da halin Mahaifiyar sa tun yana yaro ya lura da hakan bare kuma yanzu da ya girma wannan abun da yayi ne ya ƙara tabbatar masa da hakan, ganin ya rungume shi yasa shima rungume mahain nasa ya saki kuka bubbaga bayan sa yayi alamar a'a fa, Abba na murmurshi yana kallan su, sannan ya koma kallan matar sa da har yanzu basu sake ta ba sai wani zagaye ta wannan yace kaza wannan yace kaza, girgiza kan sa yayi kawai ya shiga ciki.

Umma tace, "to ya isa haka wata ƙila ko sallah basu yi ba ma ko?"

"Kai Umma?"

Hassana ta faɗa, sai kuma ta juya wurin Kawu, da shima lokacin ya juyo shikam de bazai iya cewa Khadijah ce ko Hassana ba ko ma wata be sani ba. Yayin da Mama ta kalli Fati dake kusa da ita babu ma wanda ya lura da ita ta kama hannun ta, sai anan Sabir ya lura ma da ita yaje ya riƙe ta sosai yana kallan ta kafin yasa ta a jikin shi cike da kulawa da kuma tausayi.

Khadijah tace, "Kawunah".

Tare da zuwa ta rungume shi, shima rungume ta yayi tare da yiwa Hassana alamar tazo aikuwa ta ƙara sa ta ringa Baban ta, sai da suka gama sannan suka shiga ciki yayin da Ibrahim yace yazo suke wajen Mommy.

SHAHEEDWhere stories live. Discover now