34

70 7 0
                                    

✨💫✨💫
*SHAHEED*
✨💫✨💫
*1442H/2021M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:- HIJJART ABDOUL*

*SADAUKARWA GA:-* FANS

*TUKUICI GA:-* SWEETHEART

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*


*SHAFI NA 34📑*

*__________📖* Koda safe da ya tashi kasa zuwa ya faɗawa Mama cewan an kwantar da Baba a asibiti to yace me? hakan yasa shi kawai shiryawa ya fice zuwa Zakirai ba tare da ya faɗawa Maman ba. Sanda yaje ya kira Baba mai gadin shima baya nan ya koma gida da safen hakan yasa shi faɗa masa inda aka kwantar dashi.

Yana kwance yana bacci ƙafar sa an ɗaɗɗaure da bandage haka ma kan sa har zuwa hannu kallan sa kawai yake kallo irin na tausayin nan da kuma mamakin be ya same shi haka har ta kai shi ga kwanciya, be tsaya ba ya fita wurin likita dan jin bayani sai dai kuma likitan be zo ba hakan yasa shi komawa yana mai kallan sa tare da samun kujera ya zauna.

A hankali ya fara buɗe idan sa har ya ware su fes akan gudan jinin sa dake kallan sa sai dai a zahiri babu wani abu da yake nuna yana jin tausayin nasa fuskar sa a daure tamau kamar ba ɗan sa ba da yake sashi yana yin abu amma ganin sa a haka sai yasa jikin sa yayi sanyi, hakan yasa shi lumshe ido ya rufe yana ƙara ware su akan shi.

"Be ka aikata haka?"

Yaji tambayar a bazata instead ya tambaye shi ya jiki amma shine yake masa tambayar mai ya aikata.

"Taya kake tunanin na aikata wani abu, bayan abinda aka aikata min?"

Murmurshi yayi sosai.

"Ka manta me kayi kenan ko? ka manta abinda kasa akayi mata ko?"

"Ni kuma? wa? mema nasa aka mata?"

"Nima bansani ba".

"Wai kana nufin Hassana?"

Wani munafikin murmurshi yayi.

Yace, "tabbatar ma kake so nayi da ita nake nufi?"

Numfashi yaja ya sauke cike da takaici ya rufe idan sa.

"To bata ji komai ba, ta kuma haihu lafiya shima yaron ta lafiya an kuma sa masa Shaheed".

Kallan shi yayi kallo na irin mamaki yayin da ya jinjina masa kai alamar tabbatarwa.

"Ehh, ba yarda ka so ba ko Baba? Uhmm Allah sarki haka rayuwar take daman kana naka Allah yana nashi".

Mayar da kan sa yayi sama yana kallan silin.

"Baba kayi hakuri nima ba yin kaina ne ba abinda zuciya ta ke faɗa kenan, duk da cewan kaine mutum na farko da ka nuna min so fiye da na Mahafiya kai ya kamata ace na so fiye da kowa sai dai kuma kash na rigada na farka daga mummunan mafarkin da nakeyi domin kuwa babu wanda zai so ka fiye da Mahaifiyar ka gashi kuma kayi katanga tsakani na da ita".

Murmurshi yayi.

Yace, "Amma na raba katangar da ka mana, a yanzu muna rayuwa ne a cikin inuwa ɗaya kuma tana nuna min son da baka nuna min ba tana nuna min son da babu algus a cikin sa. Ina de ace kafin na kai haka nagane".

SHAHEEDWhere stories live. Discover now