10

89 5 1
                                    

✨💫✨💫
*SHAHEED*
✨💫✨💫
*1442H/2020M.*
*1NOV/SAFAR15*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-HIJJART
ABDOUL*

*SADAUKARWA GA:- FANS*


*TUKUICI GA:- SWEETHEART*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

https://my.w.tt/3eo3ijuMybb


*SHAFI NA 10📑*


*__________📖* Sosai take kuka bayan ta kwanta a kan gado tayi rufda ciki kuka take na fitar hayyaci kamar ita ce wacce abin ya faru da ita dan ita a ganin ta gani take kawai ita da shi har abada tunda Abba yasa masa wannan dokar idan har bata faɗa masa abinda ke damunta yanzu ba sai yaushe zata faɗa masa? idan beyi maganin abin ba sai yaushe ne zaiyi? shin a haka abin zaiyi ta tafiya? a haka zata yi ta gama? har ta mutu?

Hassana ce ta shigo ganin tana kuka a haka yasa ta ƙara sawa kusa da ita itama tana kukan jikin ta a mugun sanyaye ta zauna tana kallan ta cikin kuka.

Tace, "Khadijah, wallahi bamu da laifi bamu aikata komai ba ki yarda dani..."

Da sauri ta tashi ta rufe mata tana girgiza mata cike da kuka ta kasa furta magana ta fahimtar da ita ba wannan kukan take ba ganin bazata fahimta ba yasa ta sassauta kukan ta.

Tace, "Ba haka bane, na yarda fa ina kukan rashin sa ne shikenan yanzu fa sai dai a hanya idan mun haɗu?"

Rungume juna sukayi suna kuka,sun jima a haka jin hannun ta yana ciwo yasa ta kwantar da kanta a cinyar ta tana sauke ajiyar zuciya tare da tunanin ko wanne hali yake a yanzu?

Shaheed kuwa yana shiga ɗaki ya zauna idan sa cike da hawaye taf abubuwa sun masa yawa rashin Mama, rashin Munneerah, Khadijah, Tijjani, bayajin Abba abinda yayi be dame shi ba be wuce damuwar sa da be bari yayi magana da Khadijah ba be bari ta faɗa masa abinda zata faɗa masa ba gashi yanzu ya raba shi da ita sannan Hassana.
Kwanciya yayi yana kallan silin ɗin dake ɗakin sa yana tunanin mafita bacci ne ya sace shi a haka ba tare daya sani ba, washegari da sassafe ya shirya ya fice yana zuwa yayiwa Munneerah Nasir aiki suna fitowar ya kuma shiga wani aiki yana fitowa ya wuce dan cin abinci yayi Sallah dan damuwa bata kashe shi ba batare da ga gama abinda yasa a gaba ba, bashi ya dawo ba sai dare sanda ya dawo ya tabbatar da kowa yayi bacci hakan yasa shi shigewa shima ya kwanta har ya kwanta ya tashi zaune tare da ɗauko hanky ɗin data yar yana kallo sannan ya tsaya yana dubawa dakyau kafin yayi tunanin wani abu yaja tsaki ya mayar ya ajje.

"Allah yasa ba mijin ta bane".

Yaji ya faɗa a ran sa, yana kwanciya sai kuma bukut ya kuma tashi zaune.

Yace, "to ai banga fuskar taba anya ita ce kuwa?"

"Amma ita kaɗai ke cemin Jasin".

"To kode Ameeran tace?"

"Ameeran ce zata girma haka?"

"Eh da wannan kuma, kuma ai Ameeran ma bazata ɗauka mata abinta kawai ba".

"Idan kuma girma tayi fa sannan ita ta bata?"

"It means fa kenan sun dawo 9ja".

"To ina soldiers ɗin?"

SHAHEEDWhere stories live. Discover now