30

74 6 3
                                    

✨💫✨💫
            *SHAHEED*
                       ✨💫✨💫
*1442H/2021M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:- HIJJART ABDOUL*

*SADAUKARWA GA:-* FANS

*TUKUICI GA:-* SWEETHEART

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

 


*SHAFI NA 30📑* 


*__________📖* Ganin su tayi sun tsallako titi da gudu hannun su riƙe dana juna suna zuwa suka wuce ta alamar basu ganta ba, kallo ɗaya zaka musu kasan hankalin su a tashe yake ga wata irin gigita dake tare da su, tunda ya gansu ta tsaya cak da abinda take har suka ƙara so taga sun wuce ta lura da hakan da tayi ne yasa ta bin bayan su a sanyaye ta gansu sun tare wuri ɗaya suna ganin ta suka taho da gudu suka rungume ta tare da sakin wani irin marayan kuka kasa yin komai tayi banda ƙasa da tayi tana kallan su kafin ta haɗa su ta rungume itama ta saki hawayen.

"Yaushe zamuga Ummi?"

Abinda Affan ya tambaya kenan, sakin su tayi tana goge hawayen ta.

Tace, "Zamu ganta amma ba yau ba, ba gobe ba, muyi ta hakuri kunji ko?"

Tace,"ina kuka je?"

"Wasu ne suka zo zasu tafi damu, har sun ɗauke mu nida Affan Ameer ya jefe su a ɗaya ba ido ɗaya a goshi shine suka sake mu har mukaji ciwo shine kuma muka gudu sukayi ta bimmu shine wannan mutumin nan ya ɓoye mu wanda muka haɗu dashi ɗazu shine yanzu muka gudu Anty Yunwa mukeji".

"Anty kinga inda naji ciwon hannu na sai ta ciwo yake kuma sa zafi".

"Nima kinga nawa".

Ta faɗa tana nuna mata kamar yadda Affan ya nuna mata bayan ta. Wani irin kuka ne ya ci ƙarfin ta sosai kawai ta ƙara rungume su sai da sukayi mai isar su sannan ta rarrashe su, ta nemo ledar abincin da tazo dashi ta basu da lemu suna ci tana bawa Jahshin da daman da yunwa kukan nasa, suna ci tana kallan su tare da tuna yadda rayuwar su take ada da kuma a yanzu wai sune ke cin abinci haka?

"Anty kici".

"A'a kuci idan kun ƙoshi zan ci".

"Idan muka cinye fa?"

Affan ya tambaya tana kaɗa kai irin abincin ya masa daɗi ko jimawa be samu bane oho.

Tace, "zan ci".

Haka kawai tace masa bata kuma cewa komai ba, sai da suka gama sannan tasa su sukayi alwala sukayi sallah tare da shimfiɗa suka kwanta, Washegari da safe tare da ita su ta tafi wurin aikin ta suka zauna a ɗakin da akwai ƙaramin gado sai ƴar ƙaramin wardrobe ɗakin yayi kyau sosai duk da ƙarami ne sosai suka baje yayi musu daɗi wurin ta kawo musu abinci suka ci.

A haka rayuwar su ta fara canzawa daga marar daɗi zuwa mai ɗan daɗi dan kuwa a wurin suke kwana suke tashi har tasa su a makaranta, suna kuwa ta canza musu shi sun tashi daga ƴaƴan Umar Nasara zuwa Abdullah. Tun suna damunta gami da iyayen su har suka dena musamman Affan ya dena kuma ya ƙara wayo, abu kaɗai ke damun su yarda Yayar ta su be wuce yarda ta dena kula su ba sai dai kawai ta koya musu assignment da karatun Quran shikenan abinda ke haɗa ta dasu sai kuma idan sunyi laifi ta tsawatar musu.  Bata kuma yarda tayi magana da kowa daman can ba mai magana bace sai kuma wannan ƙuncin da ya same su kullum be wuce yarda zasu ga Mahaifiyar su ba dan ta san anrigada ankashe musu shi.

SHAHEEDWhere stories live. Discover now