7

66 5 2
                                    

✨💫✨💫
*SHAHEED*
✨💫✨💫
*1442H/2020M.*
*1NOV/SAFAR15*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-HIJJART ABDOUL*

*SADAUKARWA GA:- FANS*

*TUKUICI GA:- SWEETHEART*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

https://my.w.tt/3eo3ijuMybb


*SHAFI NA 7📑* Da wani irin gudu yabi motar ganin yarda lokaci guda wuta ta tashi, Ibrahim ne da Fahad suka je da gudu sosai suka kama shi hakan be hana shi ƙara komawa ba dan gaba ɗayan sa ya fice a hayyacin Sa babu abinda yake kira sai Mamanah Mamanah kana gani zaka san zai iya aikata abinda ƙwaƙwalwar sa tace batare da tunanin komai ba, hakan yasa suka ƙara riƙe gam suna kokawa dashi sun wahala shi kuwa ko a jikin sa bema san yana yi ba kawai kuka yake yana afkin kiran Mamanah, daƙyar suka danna shi a mota suka kulle sai a lokacin masu kashe wuta suka zo, banda ƙaurin gobara da kuma wani irin ƙauri na ƙonewar mutane babu abinda wurin yake mutane da daman sun tsaya suna kallan wannan al'ajabi musamman wanda abin ya faru a gaban su.

Abba kuwa yarda ya fito daga cikin mota ya tsaya ne motsa ba zuciyar sa ke wani irin dukawa gaban sa na faɗuwa, be samu damar ƙara motsawa ba sai da aka fito da gawar mutane biyu gaba ɗaya jikin su yayi wani irin ƙuna baka gane komai, an ɗaura su a gado tare da rufe su, a hankali ya fara tafiya har yazo gaban gadan yana kallan ta Kafin ya kalli mutumin dake kusa dashi bakin na rawa yana nuna ta da yatsa.

Yace, "Bazaku kaita asibiti ba?"

Girgiza kansa yayi mutumin cike da tausayawa.

Yace, "Allah ya jiƙanta mata".

Umma data ƙara so itama cike da tashin hankali tana girgiza kai.

Tace, "Me kake nufi da hakan? wanda suka mutu ake faɗawa wannan maganar ita kuma fa Germany za'a kaita kuyi sauri ake a kaita mana".

Girgiza kan sa yayi dai-dai lokacin saura suka ƙaraso kowa na kuka ko ba'a faɗa musu ba sun san ta rasu.

Umma tace, "amma kai baka san aikin ka ba, kake kallan mu haka".

Mom ce tayi bashi hakuri, ganin yarda Umma tayi, haka ma Abba dole ya jajurce kada azo a rasa wanda zai tsaya a gaban ganin duk sun sa kuka harda kuwa Ibrahim shima sosai zuciyarsa ta karye musamman idan ya duba Shaheed duk sai yaji ina.

Mom tace, "Mariya sai fa hakuri Asma'u ta riga mu gidan gaskiya, addu'ar mu tafi buƙata".

Shiru tayi tana kallan su.

Tace, "Muje a shirya ta a kai ta kada a jinkirta".

Mom ce kawai ya jajurce aka kai ta har gida, sannan suka bi bayan ta mutane da daman kuwa sun juya alaƙar tafiyar su zuwa ga wannan jana'izar be ban al'ajabi, koda aka je aka shirya ta, aka kira Shaheed dan ya mata addu'a kasawa yayi sai ma wani kuka da ya saki yayi kan ta zai rungume ta aka riƙe shi saboda yanayin ƙunar dake jikin kasa mata magana yayi kawai sai kuka da Mamanah ya fice a hayyacin sa, bashi ya sami nutsuwa ba sai da aka zo za'a yi mata sallah danna ya sami nutsuwa aka sallace ta dashi sannan ya sami nutsuwar yi mata addu'a.

Mutane da dama sunji mutuwar ta, babu wanda kuma ake jajantawa kamar Shaheed duk wanda yasan ta to yasan ɗan ta Shaheed haka duk wanda yasan Shaheed yasan Mamanah a bakin sa, kowa shike yiwa gaisuwa hatta Khadijah itama bata tausayin kanta shi take tausayawa tasan shaƙuwar da sukayi da Mama batayi kamar yarda ya shaƙuwa da ita ba. A haka har akayi bakwai sai da akayi bakwai sannan mutane suka lafa, a washegarin ranar kuwa ƙaruwar ta suka shirya tafiya da duk wani nata na kusa.

SHAHEEDWhere stories live. Discover now