35

81 6 0
                                    

✨💫✨💫
            *SHAHEED*
                       ✨💫✨💫
*1442H/2021M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:- HIJJART ABDOUL*

*SADAUKARWA GA:-* FANS

*TUKUICI GA:-* SWEETHEART

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

 

*SHAFI NA 35📑* 

*__________📖* Yana farkawa beyi wata wata ba ya tsigi drip ɗin dake jikin sa, ya fice ƙafa ko takalmin babu haka ya bankaɗar ƙofar da iya ƙarfin sa yayi gaba, Sojojin dake jiran sa ne suka biyo bayan shi sai dai kuma basu iya tsaida shi ba bare kuma su cimma basu daman kuma ba wanda zai iya masa magana, yana zuwa ɗakin da aka kwantar da ƴar ta sa yaga yarinya a kwance tana bacci.
   Ajiyar zuciya ya sauke ganin lafiyan ƴar sa ƙalau, yana ƙara sakin wani ajiyar zuciyan ya karasa bakin gadan sai dai be iya kaiwa inda take ba ganin ba fuskar ƴar sa bace da wani irin tsawa.

Yace, "where is my child? Where is my daughter?"

"Dan uban ku daku nake".

Bema tuna basa sun yaren nasa ba wato Hausa sai da yayi maganar ganin de duk sun zubo masa ido yasa shi ƙarasowa wurin su ya cakomo ɗaya.

"Ina daughter na?"

Ya faɗa da Yaren da suka iya.

"Nace tana ina?"

Ya koma wurin ɗaya shima ya cakomo shi, haukacewa ne kawai beyi ba, mari kuwa sun sha yafi ya irga kuma basu da bakin magana gashi kowa ya kasa controlling ɗin sa, gaba ɗaya securities ɗin ya haɗa su ya zaga iya zagi ya tabbatar da wani abun ma besan yana faɗa ba, su kuwa shiru sukayi kowa aikin sa yake ji kada ya kore shi to Allah yasa ma be ambaci aiki ba.

Shaheed kam de yau ya gaji sosai da sosai hakan yasa shi biyowa domin ya duba patient ɗin sa yana dosowa wurin yaga yarda yake bambanci ya cakomi wuyan wani soja yana masa kumfar baki, be kula shi ba ya raɓa ta gefen shi ya wuce ya shiga ɗakin ganin wata ba ita ba yasa shi fitowa yana tambayar ina patient ɗin sa take, shiru sukayi masa babu amsa sai ma dukar da kan su da sukayi, ƙara tambayar da yayi ne yasa Major juyowa da sauri.

Yace, "An sace ta? Wani ya sace min ita shikenan an sace ta".

Ya faɗa yana a zauce kamar wani Mahaukaci.

Shaheed yace, "kamar ya? nace kamar ya an sace ta? duk yawan ma'aikatan nan ace an sace ta ko me? wasa ne wannan sune suka sace ta to su fito da ita".

Gaba ɗayan su zuba masa ido yayi yayin da yayi sha kunu yana kallan su ganin irin kallan da suka zubo masa.

Major daman samun wanda zai ɗora shi yake.

Yace, "Dole kune ma kuka sace ta ku fito min da ƴa ta".

"Kenan basu san aikin su ba, tunda har za'a zo a tafi da Yarinya kuna nan, to me kuke kallo?"

"Dole a kore su a aiki".

Ya faɗa yana huci, ganin ya samu yayi shiru ne yasa.

Doctor Nike matsawa kusa dashi.

Yace, "a bi komai a hankali..."

"A sace ƴar tawa kake cemin a bi komai a hankali? a'ina za'a bi komai a hankali? Bayan anganta ko bayan na kama wanda ya sace ta ɗin?"

SHAHEEDWhere stories live. Discover now