👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻
*Marubuciyar*
*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*D̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞I̸͟͞C̸͟͞A̸͟͞T̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞ T̸͟͞O̸͟͞**Aunty fauza ƴar Amana*
Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni, domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*
Aunty Hauwa Maman Uswan ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya.🙏🏻
😄😄😄😄 Sara da Sassaqa fan's kuyi hkr wlh ban manta daku ba, ina nan ina typing ɗinsa, za kuma kuga posting, gobe insha Allah.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________*P*•••••••9️⃣ ➡️ 1️⃣0️⃣
Tsawa Mama ta dakawa INDO tace,
" Maza ɗauki buta kije kiyi Alwala kiyi Sallah maxa, sannan ki ɗauko uniform ɗinki, na boko ki wanke gobe Litinin kuna da makaranta, Anjuma kuma zakije makarantar Allo.
" Nifa Mama Babu wani wanki da zanyi, haka zansa uniform ɗin, ni bokon ma ba wani damuna tayi ba.
Tanimu dake jifan Indo da mungun kallo ne ya tashi ya fice daga cikin gidan, domin Wlh ji yake kamar ya shaƙe wuyan ta, sai dai babu damar yin hakan sakamakon hanasa da Mama tayi.
INDO tana haɗa rai haka ta ɗauki buta tayi alwala, bayan tayi sallar ne, ta ɗebo uniform ɗin bokon nata, ta wanke su, tas kuwa ta wanke, domin Indo badai iya wanki ba, sai idan bata ga dama ba, tayi jiƙa jiƙa.
Jummalo ce ƙanwar INDO ta shigo cikin gidan hanun ta ɗauke da ledar shinkafar da Mama ta aike ta, ta siyo mata shagon ɗan tasi, da Sallama jummalo ta shigo, amsawa Indo tayi, tare da cewa." Zona aikeki jummalo ɗakin Mama ki ɗauko min ɗankwalin uniform ɗin nan.
Babu musu jummalo ta shige ɗakin Mama, tana sallah ta same ta, ajiye ledar tayi tare da duba cikin kayan wankin Indo, da ƙyar jummalo ta samo ɗan kwalin, ficewa tayi ta miƙa mata, cikin neman faɗa Indo ta fara cewa jummalo.
" Wato ke kuma jummalo tsabar baƙar mugunta, shine jiya kika wanke uniform ɗinki ko ki haɗa da nawa ki wanke, kinyi Asara ai ke kam, *mai shegen wariyar Launin fata*,
To gashi ai na wanke yanxu banga abunda ys ya cinye ni ba." Kiyi hkr na duba uniform ɗin naki ne ban gani ba shine yasa na wanke nawa kaɗai, Amma ai kinsan kullum nice nake wanke mana uniform koh.
" Kuma haka ne, kinsan nifa idan ana min abu kullum Rana ɗaya banga ammin ba, ji nake kamar ba'a taɓa min ba, shikenan jeki, nima na gama gari zan shiga dan wlh ba xanje makarantar Arabbi ba yau.
Ita dai jummalo shigewar ta tayi ɗakin Mama ba tare da ta tankawa INDO ba.
Washe gari da safe jummalo tayi shirin makarantar ta, kunu da ƙosai taci, sannan tayiwa Mama sallama ta tafi, ita ko Indo bata da Alamar, zata makarantar ma, dan ko karin kumallon ma batayi ba, tana zaune, kawai tayi shiru.
Mamace ta dube ta tace." INDO baxaki makarantar bane, jummalo har ta juma da tafiya, takwas fah yanxu, ko karin kumallo baki yiba.
" Zani mana, nafi son sai sun gama wannan tsayuwar tukunna, mema yake da suna, asandabilyu, ko Assambly, oho sai sun gama tukunna.
YOU ARE READING
INDO A BIRNI
Romancelabari ne akan wata yarinya fitinanniya wacce ta gagari ƙauyen su hatta iyayen ta, ta GAGARESU acikin labarin akwai ban DARIYA akwai Soyayya mai ratsa zuciyar mai karatu, ga kuma tausayi tare da nadama uwa uba kuma bak'ar ƙiyayya, shin ya rayuwar wa...