🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻
*Marubuciyar*
*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*D̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞I̸͟͞C̸͟͞A̸͟͞T̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*
*Aunty Fauza ƴar Amana*Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*
*Aunty Hauwa Maman Uswan*
Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya🙏🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________*Ina ƙaunar ku masoyana*
Na gode sosai da ƙaunar ku gareni, kwana biyu kawai da banyi typing ba, kun damu sosai, har ta privet masoya ke min magana, wasu kam ma bansan group ɗinsu ba, gaskiya na gode sosai, hakan ya nuna min yanda kuke ƙaunar wannan book ɗin.
*P*•••••1️⃣5️⃣ ➡️ 1️⃣6️⃣
Yana shiga ɗakin nasa wanka ya faɗa, Bayan ya fito daga tollet ɗinne ya mulke fatar jikin sa, da mai da turare, sannan yasa gajeren wando Wato 3cutter da best sannan ne ya faɗa saman gadon sa, tare da jawo system ɗinsa, ya buɗe, yana jin shigowar, Habeeb bai ɗago kansa ba, shima dai Habeeb bai kulasa ba, saima shigewa wanka da yayi, bayan ya shirya ne, ya dawo saman gadon nasu ya faɗa, tare da rufewa, mustapha system ɗinsa, sai a lokacin mustapha ya ɗago ya kalle sa, yace.
" Ya haka Malam, da rufe min system?
" Saboda Magana nake so muyi dakai.
" Okey ina sauraron ka, Allah yasa mai amfani ce, nasan Halin ka, da zolaya, domin itace ɗabi'ar ka.
Murmurshi Habeeb yayi, tare da cewa.
" Wannan maganar mai muhimmanci ce, mustapha.
"Okey ina sauraron ka." meyasa kake nunawa kamar baka san RAUDA na Sonka ba? Wannan yarinyar fah tayi nisa a cikin Sonka, amma kai nunawa kake bakasan tanayi ba, Bayan kuma nasan Kasan tana Sonka, ka sani fah walaƙanta ɗan adam baida amfani duk mai Sonka yafi maƙiyin ka, ko yaya yake, komai kuma muninsa, bare kuma RAUDA bata da wani muni daga fuska har dirin jikin ta.
Why mustapha, Please Answer my Questions?Cije lips ɗinsa yayi, wanda ya zama masa jiki a rayuwarsa, yana son cije lips ɗinsa, magana ya fara.
" Saboda bana sonta, bata min ba, nifa kaga RAUDA bata daga cikin kalar matar da nake bukatar aura, sannan kuma bata da aji tunda har zata iya furtawa namiji cewar, tana sonsa, mace mai aji neman ta, ake ace ana sonta ba, ita bace zata nema tace tana son.
Da kake maganar diri, koka manta da cewa shi so Babu ruwan sa, da kyau ko muni, idan kana son mutum baka ganin munin sa dan haka ni kyan mace ko munin ta, baya daga cikin ra'ayina nafi son mace mai kamun kai da nutsuwa tare da ilimin zamani dana Addini, idan har na samu mace mai wannan suffar komin munin ta, zan iya Auren ta, idan har ina sonta, sai amsar tambayar ka, ta ƙarshe itace, bani nace ta soni ba, bare kuma har tayi zurfi cikin soyayya ta, wannan damuwar tace ba tawa ba, idan kana tausayin ts mai zai hana kai ka Taimake ta, ka Aure ta, ai ina ga kamar Babu banbanci tsakanin mustapha da Habeeb, dukan su Abu ɗaya ne, kaga kuwa duk wanda yaso mustapha dole zaiso Habeeb, kodan tsantsar kaman dake tsakanin mu.
YOU ARE READING
INDO A BIRNI
Romancelabari ne akan wata yarinya fitinanniya wacce ta gagari ƙauyen su hatta iyayen ta, ta GAGARESU acikin labarin akwai ban DARIYA akwai Soyayya mai ratsa zuciyar mai karatu, ga kuma tausayi tare da nadama uwa uba kuma bak'ar ƙiyayya, shin ya rayuwar wa...