INDO A BIRNI

190 11 1
                                    

   👸🏻  *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞I̸͟͞C̸͟͞A̸͟͞T̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞ T̸͟͞O̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar amana*

Uwa mabada mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
  Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

Aunty Hauwa Maman Uswan, ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya🙏🏻.
 

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________

Masoyana bani da bakin da zan muku godiya, na gode na gode sosai, da ƙaunar ku gare Ni, yanda kuke Son book ɗin *INDO A BIRNI* abun ba'a cewa komai, waɗanda suka min magana ta privet cewa na sasu a group ɗin *INDO A BIRNI* suyi hkr dan Allah wlh group ɗin ya cika, ku nema a  wani group nasan baxaku rasa ba.🙏🏻

*P*••••••1️⃣1️⃣ ➡️ 1️⃣2️⃣

Kauda kanta RAUDA tayi cikin ƙunar rai, ta rasa menene ya gaxa a jikin ta da mustapha yake mata wannan wulaƙancin, gashi Dai Mamy tace mata malamin ta, ya  tabbatar mata cewa Mustapha zaiso ta, amma har yanzu shuru, sai ma uban wulaƙanci da take fuskanta a wajen sa, yau dai ta ƙudurce a ranta, dole sai ta koma gida, kodan Mamy tasan halin da ake ciki, domin kuwa baxata iya Rayuwa Babu mustapha ba, shine numfashin ta, taya to rayuwa zata kasance Babu numfashi, dole ma sai ka soni mustapha, dole ne.
  Maganar da Habeeb ke mata shine ya dawo da ita daga duniyar tunanin data faɗa.

  " Dan Allah Sis RAUDA anjuma ki haɗa min Abinci, mai kyau, ai kinsa abubuwan da nafi buƙata.

  " Ba komai ya Habeeb zan haɗa maka insha Allah, adawo lfy.

  " Habeeb ne kawai ya amsa da Ameen shikan mustapha, kallo ma bata isheshi ba, bare kuma ya amsa sai ya dawon ta.

  Sallama sukayi wa Momy sannan suka wuce wajen daddy kasuwa.

  RAUDA kallon ta, ta mayar wajen Momy tace.

  " Momy bari na haura sama na ɗan miƙe, kafin Anjuma na sauƙo na ɗaurawa ya Habeeb girki.

  A fito lfy ta mata, sannan ta haura sama.
  Kwanciya RAUDA tayi akan gadonta tare da ɗaukar wayan ta ta dannawa mamyn ta Kira.

   Da sallama Mamy ta Amsa, tace RAUDA lfy naji Muryar ki kamar wacce taci kuka.

  " A'a Mamy ba kuka nayi ba, kawai raina ne yake ɓace, Mamy na shiga Uku, ya Mustapha baya sona, Mamy ko kallo na, baya sonyi, ya zanyi Momy, ta ƙarasa maganar cikin kuka mai tsuma Zuciya.

  " Ya isa Haka RAUDA, ki daina kuka, domin kuwa muddun ina numfashi dole sai Mustapha ya durƙusa a gaban ki da gwiwwowinsa yana roƙarsa soyayyar ki, Dani yake zancen, tunda shi butulu ne, baisan Alkairi ba, ai yana da tarihin Halaccin da mahaifin ki yayiwa ubansa, ki kwantar da hankalin ki, zai shigo hanu, sai kin juyasa kamar wainar tanda.

  Cikin farin ciki RAUDA tace.

  " Promise Mamy, wlh ina son ya Mustapha, fiye da yanda nake son kaina,  jiya ma ya Habeeb yake cemin, zasuxo Anjuma su gaishe ki.

INDO A BIRNI Where stories live. Discover now