💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻*Na*
*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*
*(մʍʍմ ηαςʍα)*
👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻
*Marubuciyar*
*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka**D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*
*Aunty fauza ƴar Amana*
Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*
*Aunty Hauwa Maman Uswan*
Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻
Masoyana na gode sosai da Addu'ar ku gare ni, kuma ina sa tsammanin Ubangiji zai amshi Addu'ar ku gare ni.
Masu min magana akan book ɗin Ruɗanin zuciya biyu, kuyi hkr dan gaskiya ba yanzu zan fara posting ɗin sa ba, Saboda bani da full times ɗin da zanke posting book biyu, kuma kunga bazan karɓi kuɗin kuba nazo bana muku typing akan lokaci, dan haka ina ga sai na gama wannan book ɗin na Indo a birni, ga waɗanda suka min magana cewa zasu turo kuɗin su, kuyi hkr har sai randa zan fara sakin book ɗin, dan gaskiya bazan karɓi kuɗin ku yanxu ba, ban fara posting ɗin book ɗin ba.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________*P*••••••••4️⃣9️⃣➡️5️⃣0️⃣
Shan gaban motar RAUDA tayi tana cewa.
" Koda kuwa kullum zaka dinga yankan naman jikina ne bazan taɓa bijirewa Auren ka ba, sai ma farin ciki da zanyi masoyina shike yankan naman jikina, ba kuma zanji zafin wannan yanka ta da kake ba, Saboda tsantsar soyayyar da nake maka, ina sonka me yasa ba zaka soni ba? a tunani na, nice macen da nafi dacewa ka Aura ka Kuma soni iya iyawar ka."
Dariya sosai Mustafa keyi yana nuna RAUDA da hanu.
Cikin ƙula da jin haushi RAUDA tace." Meyasa kake min dariya bayan ni ba mahaukaciya bace?"
Cikin dariyar Mustafa yace mata.
_"To kuwa tabbas kin haɗa jini da mahaukatan, domin kuwa muddun ke ba mahaukaciya bace, ba zaki dinga furta waɗannan munanan kalaman naki ba, ke mahaukaciya ce, ta gaske ma kuwa mai shirin zuwa turu ma'ana (gidan mari) idan ba mahaukaci ba babu wanda zaiyi ƙoƙarin shiga inda aka tsane sa, ki kauce ki bani hanya! Tun kafin nabi kanki da wannan motar, kuma nabi kan banza, kinga sai na huta da wannan tsinannan nacin naki dangin Mayu_."
Kaucewa RAUDA tayi daga gaban motar tasa, idanunta na tsiyayar da ruwan hawaye.
Murmurshi yayi tare da cewa." Ba yanxu ya kamata ki fara zubar da wadannan hawayen naki ba, ya kamata ki adana su domin kuwa gaba zasu miki amfani mussaman ma idan kika shigo cikin gidana hawayen da zakiyi kukan ma sai kin rasa su, domin suma hawayen daɗi ne yake sawa suzo duk sanda Azaba tayi Azaba to ba'a ganin hawaye a fuskar mutum " yana gama faɗin haka yaja motar sa, tare da bule ta da ƙura, RAUDA Zama tayi daɓas tana hawaye tare da cewa.
YOU ARE READING
INDO A BIRNI
Romancelabari ne akan wata yarinya fitinanniya wacce ta gagari ƙauyen su hatta iyayen ta, ta GAGARESU acikin labarin akwai ban DARIYA akwai Soyayya mai ratsa zuciyar mai karatu, ga kuma tausayi tare da nadama uwa uba kuma bak'ar ƙiyayya, shin ya rayuwar wa...