INDO A BIRNI

179 13 0
                                    


            👸🏻  *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
  Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*••••••3️⃣7️⃣ ➡️ 3️⃣8️⃣

"Mamy na rasa ya zanyi, mustapha baya saurarata, ko kiran sa nayi, sai ya faɗa min baƙar magana, kafin ya kashe kiran."

Cikin faɗa Mamy take cewa RAUDA.

" Nifa RAUDA na gaji !! na gaji !! Da lamarin ki da mustapha, akan me kullum abu ɗaya yaƙi ci yaƙi cinyewa, keba mace bace, da bazaki jawo hankalin Saba, maganin ma, dana baki kin kasa Zuba masa, to yaya kike so na miki, zuwa zanyi na jawo sa, nace dole ya soki, RAUDA ki saurareni da kyau, idan zaki tashi ki nemo soyayyar mustapha to ki tashi, domin kuwa, nunawa mustapha da kike a Soyayyar ki, a fili, bazai kaiki ba, dole sai kin rage shigar masa, ki daina nuna masa maitarki a fili, ki kama Class ɗinki, cikin kirsa zaki samu ki sawa mustapha wannan maganin abincin sa, domin kuwa idan yaga kin fita harkar sa, to fah dole zai ɗauke Idonsa a kanki, sai ke kuma kibi wannan hanyar ki, samo kansa, ina fatan kin fahimce ni."

" Eh Mamy na gane, kuma insha Allah zanyi amfani da Wannan shawarar taki."

" Yauwa koke fah, yanxu yaushe zasu dawo daga ƙauyen?"

  " Bansani ba, amma Momy tace, idan sun dawo zata kira ni."

" Shi kenan hakan ma yayi, yanxu ki tashi kije, ki ɗaura mana abinci, ni bara naje na gyara ɗakin Abban ku."

  " To Mamy." RAUDA ta amsa tare da tashi tayi kitchen."

  Misalin ƙarfe biyu na azahar, su Indo suka shigo cikin gidan, bayan sunyi parking ne, kowa ya fito, kalle kalle Indo take, cikin ƙauyanci, baki buɗe take kallon fulawin dake, zagaye ƙofar gidan, da gudu tayi gun fulawin tare da taɓa su, tace.

  " Lah !! Innah kinga wasu Abu masu ado, Innah sun miki kyau kema, nidai aradu sun min kyau."

Duban ta, itama INNAH takai wajen, tace.

  "Sunyi kyau sosai ma, ikon Allah!! Wani abu sai birni, ki duba yanda aka shuka waɗannan Adon kamar zama aka zo duniyar ba za'a mutu ba, yayi kyau."

  Mustapha ne yaja suka da ƙarfi tare da hararar ta, ita kuwa Indo ko a jikin ta, bata sanma yana yiba, domin kuwa, ta bada hankalin ta, gabaki ɗaya, wajen wannan fulawin, murmurshi daddy yayi sannan yace.

  " Sharifa, maza jeki ki jira Indo, idan ta gama kallon fulawin, sai ku shigo tare, Innah mu shiga cikin gida, zasu taho da sharifa."

  Kallon sharifa Innah tayi tace.

INDO A BIRNI Where stories live. Discover now