INDO A BIRNI

224 12 0
                                    


             *I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
                      💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

               *Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

  *(մʍʍմ ηαςʍα)*

            👸🏻  *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
  Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*WLH DA NIYATA NA DAINA RUBUTA WANNAN BOOK ƊIN, DOMIN KUWA AN ƁATA MIN RAINA FIYE DA TUNANIN KU, IDAN HAR KA TAMBAYI MUTUM BOOK TA PRIVET SAI KIYI HKR, KI JIRA WATAƘIL BATA ONLINE WATA ƘIL KUMA MESSAGE NE SUKA MATA YAWA SHIYASA BATA MAYAR MIKI AMSA BA, AMMA TSABAR RAININ HANKALI ZAKI WANI CEMIN WAI INA DA GIRMAN KAI, IDAN MA NA KUƊI NE NA FAƊA MATA ITA ZATA IYA BIYA KO NAWA NE, TUNDA TAGA YANZU WRITER'S KUƊI MUKA SAKA A RANMU MUN MAIDA SOCIAL MEDIA KASUWANCI, SAI KI FAƊA MIN WAYE BAYA SON KUƊI KO KUMA A INANE BA'A NEMAN KUƊI, DA KIKE WANNAN MAGANAR WACE WRITER'S KIKA TAƁA SAWA DATA, IDAN BOOK ƊINA MA NA KUƊI NE INA RUWANKI SAI YA MIKI KI SAYA, BABU KOMAI KANKI KIKA YIWA KIJE GABA ZAKI HAƊU DA DAI-DAI KE NA BARKI DA ALLAH*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*•••••••5️⃣9️⃣ ➡️ 6️⃣0️⃣

"Naji zafin mutuwar Inna sai dai kuma nafi jin Zafin rashin ganawar da ba muyi ba da ita har ta koma ga mahaliccin ta, shekara 6 rabona da nasa mahaifiyata cikin idanuna, hakan ne idan na tuno nake jin zafi cikin zuciyata, nasan mutuwa rigar kowa ce, jiranta yake sai dai naso ace nasa Inna cikin idanuna koda sau ɗaya ne, Allah ya jiƙanki da rahama Inna yasa can yafi miki nan" ta ƙarasa maganar tana goge hawayen cikin idanunta, Aunty Hindu ta bawa kowa mamaki domin kuwa tafi kowa ɗaukar ƙaddara, da dauriya.

Wunin Ranar Aunty Hindu tare suka yisa dasu Mama Momy kam dama bata cika shiga cikin su ba, Indo kuwa ɗaki ta wuni cikin tunani, lokaci ɗaya tayi wani irin faɗawa idanunta su faɗa suma, hawaye kuwa har yanzu yaƙi barin idanunta ba.

Yau Litinin akayi sadakar bakwai ɗin Inna, kowa yayi haƙuri ya dangana ya barwa Ubangijin sa lamarin sa, haka Indo itama ta haƙura amma har yanzu taƙi sakewa jikin a sanyaye yake, su Mama sai haɗa kayan su suke zasu koma ƙauye gobe, Indo ce ta shigo cikin ɗakin tana ƙarewa kayan Inna kallo, wani zanin Inna ta hango, sai ta tuno, randa Ilu ya biyota da gudu ta faɗa gidan Inna, itama Inna ta bi bayan ta da gudu tana sababi har Indo take cewa ( lafiya Indo kike gudu kodai yauma macijin ya sake biyoki.

yanzu ke Inna idan macijin ne sai na tsaya har ki iso ban rufe ƙofa ba, ai wlh kafin ki ƙaraso na juma da rufe ƙofar nan sai dai kuma kisan tayi.

Amsa Inna ta mayar mata da cewa.

"Amma dai ke Indo akwai ja'irar yarinyar yanzu dan baki da mutunci sai ki rufe ƙofar ki barni a waje wato idan ma kasheni macijin zaiyi ke baki damu ba, *to bari muga idan na mutu ina zaki dinga samun taliyar turawa kina ci, naga kuma wanda zai dinga karɓa miki faɗa tunda gani nane baƙya ƙaunar yi ina numfashi a duniya*)

INDO A BIRNI Where stories live. Discover now