👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻
*Marubuciyar*
*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka**D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*
*Aunty fauza ƴar Amana*
Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*
*Aunty Hauwa Maman Uswan*
Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________*P*•••••••2️⃣1️⃣ ➡️ 2️⃣2️⃣
" *Wayyo Allah daɗi kashe ni, ya Mustapha na, Aradun Allah ina sonka, kibiyar sonka ta soke ni, kaji wani irin daɗin da naji kuwa da ya Habibu yace ga mustapha na*.
Jin shurun da tayi ne, yasata kallon Habeeb tace.
Ya Habibu banji yayi magana ba, fah.Mustapha bai kashe wayar ba, shuru yayi yana jin su, domin kuwa yana jin sanda Habeeb yake, cewa Indo gashi mustapha ne kiyi Magana, shiyasa yayi shuru ba tare daya kashe wayar ba, yana jiran Habeeb ne ya karɓi wayar ya masa rashin mutunci.
Karɓar wayar Habeeb yayi tare da dubawa, cikin mamakin ganin mustapha bai kashe wayar ba, kuma bayan yaji Muryar Indo, sa wayar yayi a kunnen sa, tare da cewa.
" Bros ya kuma kayi shuru kana jin masoyiyar ka, tana sanar dakai yanda kifiyar sonka yake sukan ta kayi mata banxa.
Murmurshi mustapha Yayi cikin jin takaicin yawan wasan Habeeb, shi dai komai zai iya yiwa mutum wasa akansa, koda kuwa mutum yana cikin Halin da baya buƙatar wasa.
" Hmm to Uban ƴan neman magana, naji sai kuma akayi yaya, Sarkin ƴan neman magana na duniya, Kuma bari kaji na sanar dakai daga yau baxan ƙara neman ka a waya ba, har sai kabar wannan ƙauyen, Kuma karka Ƙara nema na, dan ko ka kira baxan ɗaga ba, tunda kaima kana son biye wannan shashashar ku zama iri ɗaya.
Murmurshi Habeeb yayi, cikin serious ya cewa mustapha.
" Bros naji abunda ka faɗa min kuma na ƴarda, sai dai ina son kasan Wani Abu guda ɗaya, kallon Indo yayi da ta mayar da hankalin ta wajen sa, ficewa yayi daga ɗakin Innah yayi nasa yana cewa.
*Duk yanda mutum yake, bai kamata ka wulaƙanta shiba, domin kuwa, gobe baka san mai zai zama ba, sannan aini a tunanina, shi mai Sonka yafi maƙiyin ka, kuma bai cancanci wulaƙanci daga gare kaba, Amma kai Bros........*" Enough Habeeb bana buƙatar wani magana daga gare ka, cikin tsawa yace, *akan me zaka bawa wannan shashashar Iblis ɗin wayata, yarinyar data gagari Uban kowa cikin wannan ƙauyen, ƙazama marar Hankali da lissafi, idan har kaima ka koma shashasha, toni ban koma ba, da nawa hankalin a jiki na*
Yana gama faɗin haka ya kashe wayar.Zuciyar Habeeb idan tayi dubu to, ta ɓaci domin kuwa yaji zafin maganar da mustapha ya faɗa masa, duk da yasan halin zafin zuciyar mustapha, zai iya yiwa kowa ihu idan ranshi ya ɓaci, sai dai baiyi tunanin, dan ya bawa Indo waya, ranshi zai ɓaci haka ba.
Shigowar Indo ne, ya katse masa maganar zucin daya ke yi.
YOU ARE READING
INDO A BIRNI
Romancelabari ne akan wata yarinya fitinanniya wacce ta gagari ƙauyen su hatta iyayen ta, ta GAGARESU acikin labarin akwai ban DARIYA akwai Soyayya mai ratsa zuciyar mai karatu, ga kuma tausayi tare da nadama uwa uba kuma bak'ar ƙiyayya, shin ya rayuwar wa...