13

298 11 0
                                    

*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*


*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

               *Z.W.F.🏝️*

*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*

       *Marubuciyar*

*Ƙawar ƴata ce*
*Umarnin saurayi*
*Ƙawaye ne sanadi*
*Auren biyayya*
*A chating muka haɗu*
                 And now
    *Mijin Babata ne*


*NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFI DAGA FARKONSHI HAR ƘARSHE ZUWA GA MASOYIYATA KUMA ƳAR UWATA MUMY KULSUM, (Zakiyya).*


*SHAFI NA 13*

        

           Asalin labari.

Malam Bashar shene Mahaifin Hansa'u, Sunyi aure da Mumy wato  Yasira cikin so da ƙaunar juna, Malam Bashar Malamine a wajan Yasira wato malamin su ne na islamiya, malam Bashar mutumin kirkine kowa nashi ne haka yasa kowa ke ganin girmanshi, bayan sun dai-dai ta da yasira yaje ya sanar da Mahaifiyar shi ya samu matar aure, da yake mahaifinshi ya jima da rasuwa, Hajiya Sa'a tace yanzu Bashar kai da baka da baka gama gini ba, ina kai ina wani zanci ka fitar da matar aure, nuna mata yayi shi ba yanzu za'a aure ba, kawai yana so ne iyayenta su san dashi dan kar ayi mata miji, ba yadda Hajiya Sa'a ta iya haka taje ta samu ƙanin mahaifinshi yaje ya nemar masa auren Yasira wajan ƙanin Mahaifinta, dan ko ita mahaifinta ya jima da rasuwa.

Bai sha wuya wajan bashi Yasira ba, Saboda kowa yasanshi mutum ne wanda yasan darajar mutane kuma ya iya zama da mutane.

Haka Malam Bashar da Yasira suka cigaba da soyayar su har zuwa wani lokaci , ƙanin Mahaifin Yasira ne ya aikowa Iyayen Bashar yace yana so ya aurar da ƴarshi idan har Bashar bai tashi ba shikam ya tashi aurae da ƴarshi sai dai yayi haƙuri zai bawa wani, shi kuma Allah ya haɗashi da wata.

Bashar najin haka sosai yashiga tashin hankali shida Yasira, da mahaifiyar taga haka ta bashi shawar tonda yana son Yasira ya je ya ɗauke haya zuwa shekara ɗaya dai-dai ya ida ginin gidanshi sai ya koma.

Haka kuwa aka Hajiya Sa'a tasa mishi hannu har ya samu aka ɗaura mishi aure da Yasira.

Wani ƙaramin gidane yasamu haya amma Yasira tace shi take so ba komai nashi ba, dan haka koda aka kaita gidan bata damu ba suka cigaba da zamansu cikin so da ƙaunar juna.

Sai da yasira ta shakara ɗaya sannan ta samu ciki mai wahala ga kuma laulayi, ko yaushe ba lafiya, suna cikin haka kuɗin haya ya ƙare mai gida yace tabbas sai sun bar masa gidanshi idan basu bashi kuɗi ba, kuma dai-dai wannan lokaci Bashar bashi da kuɗi ga ɗawai niyar iyali kuma gashi koda yaushe suna asibiti saboda cikin bai bawa yasira lafiya ba.

Irin walaƙanci da yasira taga mijinta anayi mishi ne yasa tace bari ta sayar da kayan ɗakinta suje a gina mata ko room and parlour da toilet yafi musu shan walaƙanci, bayan ta gayawa iyayenta shima ya gayawa mahifiyarsu ne aka sayar da kaya yayi gini sannan suka koma ciki abin sai wanda ya gani.

Koda suka koma ko katifa bata da ita, haka suka riƙa bacci a ƙasa har cikin Yasira ya tsofa.

Lokacin da cikin ya cika wata tara Allah ya azurtasu da samu ƴa mace, sosai sukayi farin ciki da kyautar da Allah yayi musu.

Bayan suna Bashar ya tashi tsaye wajan nema, ko kafin Yasira ta dawo wanka ya saya mata kayan ɗaki irin na zamani, sosai tayi farin ciki da haka, haka suka cigaba da zamansu cikin rufin asiri har Yasira ta kai shekara huɗu amma babu wani labarin samun wani ciki dan haka suka cigaba da kula da ita, dan ko makaranta ta kuɗi mahaifinta yasa ta, Shekar Hansa'u sha huɗu Allah yayi wa Malam Bashar rasuwa, mutuwar da ta gigita ala'uma da ƴan uwa musamman ita kanta yasira, dan ba wata jinya yayi ba motace ta kaɗeshi.

MIJIN BABATA NEWhere stories live. Discover now