34

181 19 4
                                    

*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*


*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

               *Z.W.F.🏝️*

*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*

      

*SHAFI NA 34*

" Mumy kece!".

Mumy kasa magana tayi cikin sauri ta rugumeta, lokaci ɗaya wasu hawayen farin ciki suka fara zuba a idonta cikin muryar kuka tace,

" Ki yafemin Hansa'u, nayi ba dai-dai ba, dan Allah ki yafemin ki dawo gareni wallahi bani da kamar ki a rayuwata".....tun bata rufe baki ba Hansa'u tace,

" Haba Mumy miyasa zaki faɗi haka? Ina mijinki hala?".

Jikinta ta ƙara sakata hawayen baƙin ciki na zuba a idonta gashi ɗiyar ta ma tana mata tambayar da ba dai-dai ba, da bata ai kata haka ga ƴarta ba, ai bazata faɗa mata haka ba.

" Ina kike da zama kuma suwa ye kuke tare dasu?".
Mumy ta faɗi haka tana share kwalla.

Saboda hawayen da taga na futa a idon Mumy yasa ta sanar da ita sunan unguwar da suke  haɗi dayi mata kwatancin gidan da suke, a hankali Mumy ta buɗa baki zuciyar ta na ƙuna tace,

" Ashe kina cikin garinnan amma ki kasa zuwa wajena Hansa'u? ashe laifin dana miki mai girma ne, ina roƙonki da Allah ki yafe min, kuma ki  bari na naje naga gidan iyayenki kuma nayi musu godiya".

" A'a Mumy ki bari gobe kizo kinji saboda yanzu mijinki bai san zaki je gidanmu ba, amma gobe ko baki zoba ni zan zo , insha Allah".

Da ƙyar Mumy ta yarda suka rabo da Hansa'u batare da taje taga gidansu ba.

Jikin Hansa'u a sanyaye haka suka koma gida, koda suka sauke ta har tashiga gida bata haɗu da kowa ba, kai tsaye ɗakin Mumy ta nufa ta gaya mata cewa ta dawo.

Har zata fito ɗakin Mumy sai Mumy tace,

" Anjima idan Yayanki ya dawo kije ki bashi haƙuri sabida kin fita batare da izinin shi ba, kuma naga kamar ranshi ba daɗi".

Duƙar da kai tayi kana tace,

"Tau Mumy insha Allahu zanje".

Tana faɗar haka ta fice tana tura baki gaba.

Yana fita yaje gidan hutawarshi ya rufe shi kaɗai ya kwanta zuciyarshi na ƙona, ya za'a cewa yarinya ta riƙa fita son ranta babu neman izini kamar wadda bata da aure.
Haka ya riƙa tunani har bacci ya yi awon gaba dashi.

Sai da ya yi sallah isha'i sannan yafice, kai tsaye wajan da abokan shi ke haɗuwa anashan shayi atayi nan yazo shima suka fara fira anayi ana shan shaye mai ɗauke da haɗe-haɗe na ƙarfen maza, sosai ya sha shayen saboda ya yi masa daɗi sosai, dan haka ya buɗe ciki yasha son ransa.

Sune basu tashi ba sai ƙarfe goma sannan suka tafi gidajin su wajan iyalan su.

Kai tsaye gida Abdul ya dawo, da shigar shi part ɗunshi ya shiga bai shiga wajan Mumy ba, ita ko Mumy tunda taga ya jima bai dawo ba tasan cewa yau ranshi a ɓace yake, dan haka tana ganin ya dawo ta tashi ta nufe ɗakin Hansa'u, zaune ta sameta tana karatu saboda sunyi kusan fara jarabawa.

Da sallama Mumy ta shiga, bayan Hansa'u ta amsa sannan Mumy tace,
" Hansa'u tashi ki kaiwa Yayanki abinci tun ɗazo bai dawo ba sai yanzu".

Kamar bazata tafi ba kuma sai tace,

" tau Mumy".

Hijab ɗinta tasa sannan suka fito tare da Mumy.

Yana shiga ɗakinsa kai tsaye ban ɗaki ya nufa ya yi wanka sannan ya kwan ta saboda yana son hutu duk da ba bacci yake ji ba.

MIJIN BABATA NEWhere stories live. Discover now