42

170 14 4
                                    

*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*


*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*

      

*SHAFI NA 42*

Ajiyar zuciya ya sauke, to shi wani aiki zai je ya yi ya samu kuɗi, gaskiya shi kam duk aikin da zaiyi sai yasha wahala, amma bari ya je yaga ko zai samu mashin ya riƙa acaɓa ko tanan zai iya ci da matarshi da ƴarshi.

Tashi ya yi yaje wajan abokinshi dan ya yarakashi wajan mai gidanshi ya bashi mashin yariƙa acaɓa kullum ya riƙa biya har mashin ɗin yazama nashi.

Abokinshi ya dubeshi kana yace,

" Hala ina Hajiyarka da zaka tafi wani waje neman mashi, bayan idan ka gaya mata tabbas zata sake baka kuɗi kasayi wani, dan nasan irin son da take maka".

Harara Kabir ya afkamasa kana yace,

" Kace dai ina tsohowata, ai na san kallon ɗan iska ko ke min tunda na aureta, to bari kaji wallahi na gama da ita dan ba komai acikin auren tsohowa sai wahala da jarabar tsiya, ni yanzu na fi son na zauna da Matata yarinya da ita kuma sabon jini".

" Shan kana nufin kun rabo da Hajiya?".
Haka abokinshi yace dashi a taƙaice.

" Eh murabu,  kawai ku tayani murna na kuɓuta daga hannun jarababba".

" Wallahi Kabir in har ka rabu da Hajiya to tabbas kayi asara, kuma asara bayyananna, bari kaji yanzu sau tari maza matasa sun fisun su aure irin Hajiyoyin nan, ka ga na ɗaya a baka kulawa mai girma, a mutuntaka, a mutunta danginka, ko ka kawo ko baka kawo ba dafawa ake aci batare da kowa ya sani, kuma sun san salon soyayya ta ƙin ƙari, kai bari gaji yanzu haka abokin mu Yusuf wata Hajiya zai aura har anyi komai wallahi gaskiya kayi asara, shawara zan baka tun wani bai rigaka ba kaje ka mayar da auren ka ".

Wata harara Kabir ya afkawa abokinahi kana yace dashi,

" Kasan Allah Mansur, muddin kana son mu zauna lafiya to karka sakiyi min maganar da tayi kama da wannan in ko ba haka ba, wallahi zamu samu saɓani".

Kayi haƙuri abokina, tonda baka so wallahi bazan sake ba, kuma naga shawara ce na baka, amma kayi haƙuri na daina, tashi muje tun kafi Alhaji ya fice".

Kabir bai ce dashi komai ba ya tashi suka tafi, koda suka je Alhajin baya nan dan haka suka dawo zuwa dare su koma, roƙon abokinshi ya yi da ya bashi taɓa kalasa yaje ya samu abinda za'a ci gidanshi, ba dan Mansur ya so ba ya bashi haɗi da gaya masa kar ya jima. Karɓa ya yi ya tafi.

        *******

Sosai taji daɗin wayar da su kayi da Abdul, ko ba komai yau ya nuna mata ya kula da ita, ga baki ɗaya ta nemi ɓaccin ran da take ciki ta rasa, dan haka ta tashi taje wajan da Mumy ke aiki ta tasa hannu ta taya ta suna hira.

Mumy sosai taji daɗin ganin ƴarta ta daina fushin da take wanda ita bata san fushin mi takeyi ba.

Mumy ta kai dubanta ga Hansa'u tace,

" Yaushe Abdulrazak zai dawo?".

Sun kuyar da kai Hansa'u tayi ƙasa kana tace,

" Satinnan yace".

Murmushi Mumy tayi kana tace,

" Allah ya dawo dashi lafiya".

Cikin ranta ta karɓa da ameen ya rabbi.

Bata koma ɗaki ba sai da suka kammala aiki suyi wanka sannan ta koma ɗakinta.

Tundaga wannan rana Mumy da ƴarta kullum cikin farin ciki suke, komai za suyi tare suke yinshi, ko fita Mumy zatayi tare da Hansa'u take fita, sosai Mumy ta jawo ƴarta jikinta tana nuna mata yadda ya kamata ta kula da mijinta, kar ta bari kunya tayi mata tasiri har ya kai da tana cutuwar mijin ta, kuma yadda Mumy ta fahinta ƴarta na ɗaukar darasi dan yanzu koda yaushe suna waya da Abdul.

Wannan abu ba ƙaramin daɗi ya kewa Mumy ba, gani ƴarta cikin farin ciki yasa ta manta dawa ni Kabir, dan tabbas idan ta tunashi ita kanta haushin kanta take ji.

      Bayawan kwana biyar.

Abdul ne zaune shida Mumy da Dady shi suna fira saboda jiya da yamma ya dawo, to bai samu damar zama suyi fira ba sai yanzu.

Bayan sun gama kalaci kana ya kai duba  ga mahaifinshi yace,

" Daddy hutuna ya ƙare, sati na sama zan koma Germany, ina son dan Allah ku yarda na tafi da Hansa'u, saboda yanzu idan na tafi zan jima ban dawo ba".

Har Mumy ta buɗa baki za tayi magana sai daddy yace,

" Ai matarka ce, sai ka tambaye mu, duk inda ka ke so katafi da ita ba wanda zai hanaka a cikin mu, daman ko lokacin da za'a tafiya da ita na gaya musu cewa da ka dawo za'a baka matarka, to yanzu ka dawo dan haka ki gayawa mahaifiyarta gobe ko jibi a dawo masa da matarsa".

Ya kai ƙarshin zanci yana dubin Mumy.

Hajiyar zuciya Mumy ta sauke kana tace,

" Alhaji ban katsi hanzarinka ba, amma yarinyarnan karatu take, taya yaro nan zai tafi da ita tana karatu, kuma gobe ko jibi kila basu shirya ba, mi zai hana a basu ko kwana biyar ne da gaya musu".
Ta faɗi haka kanta na ƙasa.

Wani shu'umin kallo Daddy ya afkawa Mumy kana ya miƙi tsaya tare da faɗar,

" Nariga nagama magana ba acanjamin tsari".

Yana gama faɗar haka ya tashi ya bar waja.

A jiyar zuciya Mumy ta sauke haɗi da yin ƙasa da kanta.

Abdul na ganin haka ya ƙaraso wajan Mumy ya dubeta da kyau kana yace,

" Mumy dan Allah ki kwantar da hankalinki, wallahi nayi miki alƙwarin zan bar Hansa'u ta koma makaranta idan na tafi da ita, koma zan kula da ita fiye yadda bakiyi tunani ba".

Ɗago da kanta tayi tace " tau,  Allah yayarda".

Da ameen ya karɓa, sun jima suna fira daga baya ya yi mata sallama ya fita.

Yana fita ta ɗau waya ta kira Mumyn Hansa'u ta gaya mata halin da ake ciki, Mumy tace wallahi Hajiya babu komai daman ni ina tasa ido naji kunsa lokaci amma shuru, Allah ya kaimu lokaci.

Da ameen Mumy ta karɓa daga baya sukayi sallama.

Suna gama waya da Mumy Mumy Hansa'u ta dube Hansa'u dake kwance saman dogowar gojera, tunda suka gama aiki tayi wanka take kwance ta kasa tashi tasa tufafin ta tace,

" Jibi zaki koma gidan mijinki, dan haka bari yanzu nayi wanka naje na tambayo miki kitso da kunshi, sai kije can inda lnnata gobe ayi miki".

Kunya ce ta rufe Hansa'u dan haka bata samu damar cewa komai ba.

Mumy ma bata bi ta tata ba, ta tashi tashirya ta fice.

Mumy na fita ta itama ta kwanta bacci ya yi awon gaba da ita.

Tunda ya bar ɗakin Mumy part ɗinshi ya nufa ya yi wanka,  haɗi da fashi jikinshi da turare kana ya kama hanyar gidansu Hansa'u.

Koda ya isa gidansu Hansa'u bai samu yaron da zai aika ba, waya ya ɗauko yakira Mumy ta sai ta shaida mishi cewa bata gida, amma yashiga Hansa'u kadai ce a gida.

Godiya ya yi mata sukayi sallama ya fito daga mota ya shiga gidan kai tsaye.

Sai da ya gama kallon gidan tsaf sannan yace Mumy kema nan gaba kaɗan zaki bar unguwar nan.

Yana kowowa nan ya ƙarasa cikin ɗaki.

Yana shiga parlour idonshi ya sauka akanta, kwanci take sai famar bacci take hankali kwance, kallo ɗaya zakayi mata ka tabbatar da haka.

Sanye take da wani ƙaramin tawol wanda bai ida rufe jikinta ba, saboda tunda suka gama aiki tayi wanka ta kwanta saboda jiya Mumy bata barta tayi baccin dare ba, cewa tayi ta tashi ta gayawa Allah buƙatunta, duk mutum mai hankali da tunani baya bacci har gare ya waye sannan ya tashi, ba dan taso ba haka ta tashi, shine yanzu take ramakon bacvi.

Sai da yagama kalleta tsaf sannan ya fara tako ya isa inda take kwance..


*SUMMY M NA'IGE*

MIJIN BABATA NEWhere stories live. Discover now