43

169 8 0
                                    

*🤦‍♀️🤦‍♀️MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*

         *Tsarawa da Rubutawa*
       *(UMMU JA'AFAR)*


*SHAFI NA 43*

Zama ya yi kan kujerar da ke kusa da ita, saboda bai ji zai iya tashe ta ba, saboda shima idan yana bacci baya son a ta she shi, ya jima zaune yana dannar waya kafin wayarshi ta fara rura.

Cikin bacci taji waya na ƙara, da sauri ta tashi sai famar juyayi take tana so taga ta inda ƙarar waya ke fitowa.

Ido suka haɗa dashi, kallo ɗaya ya yi mata ya maida hankali kan wayarsa da ke rura, ɗauka ya yi haɗi da karawa a kunninshi.

Mamaki ne ya kamata, yaushe yashigo bata sani ba, sam ta manta yadda take sai kallonshi take ɗauke da mamaki a fuskarshi.

Sai da ya gama waya ya jawota jikinshi sannan ta dawo duniyar tunanin da ta tafi.

Kallon ldo cikin ido sukayi wa juna, da sauri ta kawar da idonta saboda wani kwarjini da taga ya yi mata, bata ankara b ya haɗi bakinsu waje ɗaya, ƙoƙarin cire mata tawol ɗin da kirjinta ya farayi, sai a lokacin ta tuna daga ita sai tawol take, da sauri ta fara ƙoƙarin tashi daga jikinshi, shi ko yana ganin haka ya ƙara haɗeta da jikinshi yana faɗar,

" Ashe ba da gaske kike ba da kika ce kinyi kewata".
Ya faɗi haka yana kifeta da ido.

Baki ta turu gaba, tana shirin yin magana ya sake haɗi bakinsu.

Sun jima yana wasa da ita har suka manta a ina suke, sosai yake jin sonta na ratsashi, ji yake kamar ya ɗauketa ya tafi da ita gidanshi, saboda sosai yake buƙatar matarshi.

Suna cikin haka can suka fara jin kamar muryar Mumy na sallama.

Basu samu damar ƙarɓawa ba saboda sunyi nisa cikin kogin soyayyar.

Mumy data ji basu ƙarɓa ba sai ta ƙi shiga ɗakin, hajab ɗinta ta cire kana ta cigaba da aikin da ke gabanta, saboda wasu itatuwa ne na gyaran jikin aka bata ta dafawa Hansa'u yau ake son tashi har zuwa gobe.

Hansa'u da taga abinshi zai wuce gona da iri da sauri ta fara ƙoƙarin tashi daga jikinshi, ƙin sakin ta ya yi haɗi da yimata wani kallo da idonshi da suka koma kalar ja.

Kukan shagwaɓa ta samasa kana tace,

" Dan Allah Habibi kabari wallahi Mumy ta dawo karkasa naji kunya dan Allah".
Ta faɗi haka kamar zata zubar da hawaye.

Ba dan ranshi yaso ba ya saketa ta tashi tashiga ɗaki ta saka tufafinta kana ta fita ta gaishe da Mumy.

Amsawa Mumy tayi tana mai ci gaba da aikinta.

Kujera Hansa'u ta ɗauko dumin ta zauna ta taya Mumy aiki, Mumy na ganin haka tayi sauri ta ɗago da kai ta dubeta haɗi da dallamata harara, nunu tayi mata da ta koma ɗaki, ba dan taso ba haka taja ƙafa ta koma ɗaki.

Koda ta shiga yana ƙoƙarin fitowa, kallon shi tayi tace,

" Ba dai har ka tashi ba?".

Jawota jikinshi ya yi haɗi da matsita sosai a jikonshi kana yace,

" Zan tafi koma sai kin zo saboda in har zan ganki, to bashakka bazan iya haƙura ba, to kinga da azo aji kunya gwara na haƙura har zuwa jibi".

A jiyar zuciya ta sake haɗi da shaƙar turarinshi mai ƙamshin daɗi.

Maganar da baiji tayi ba ne yasa ya raba jikinshi da nata ya kama hanyar fita.

Zama tayi kan kujera tana sauke ajiyar zuciya a hankali-ahankali.

MIJIN BABATA NEWhere stories live. Discover now