33

167 10 3
                                    

*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*


*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

               *Z.W.F.🏝️*

*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*

      

*SHAFI NA 33*

Kasa magana Hauwa tayi saboda maganar Ahamd ta dakar mata zuciya, zufa ce ta fara zubar mata a hankali ta buda baki  tace,

" Ahamd dan Allah ka ne mi wata ka aura dan Allah ba dani ba".

" Saboda me Hauwa zakice haka?  bari kiji,  wallah ina son Binta har cikin raina, a halin yanzu raba ni da ita abu ne mai wahala, shiyasa muka yanke shawar gwara muyi aure, ina so ki zauna ki natsu ki duba wannnan lamari, insha Allah kuma abinda kike tunani bazai faru ba".

Kanta ta ɗago ta dube shi kana ta sauke ajiyar zuciya tace,

" Tau Ahamd zanyi tunani akai, ina roƙon Allah ya tabbatar da abinda yafi zama alhairi".

Da ameen suka karɓa sannan suka ɗauko wata fira sunayi, daga baya kuma Ahamd ya ta fiyarshi.

Da dare bayan sallah isha'i suna zaune suna fira da lkiram sai ga yaron Hauwa ya shigo gidan da gudunsa, wajan da take ya nufa haɗi da faɗawa jikinta yana mata dariya.

Dagashi tayi tace,

" Kajimin yaro, kashigo gida ba sallama bare ka gaishe da mutane".

Ikirman tace,

" Ai yaro na yafishi kirki dashi ne zai gaishe mu".
Ta faɗi haka murmushi ɗauke a fuskarta.

"A'a lkiram ɗan Mamarshi ai yafi kowa kirki".

Tafaɗi haka tare da jawoshi jikinta tana masa wasa kana tace,

" Kai da kuka zo cikin daren nan?".

Sai da ya turu baki sannan yace "nida Babana yana waje yana kiranki".

Tun kafin ya rufe baki lkiram ta hau guɗa haɗi da tashi tsaye tafara rawa kana tace,

" Aunty tashi ki sauya kaya kizo nayi miki kwaliya na ɗauramiki ɗan kwali dan Allah, gaskiya yau ranar farin ciki ce garemu".

Murmushi Hauwa tayi kana ta tashi tashiga ɗakin ta ta sauya kayan jikinta haɗi da feshi jikinta da turare mai ƙamshi, tana cikin haka lkiram tazo tace tabari tayi mata kwaliya tace,

"A'a lkiram bari zuwa wani lokaci yanzu bamu san da me yazo ba kiyi haƙuri".

" Tau Aunty, amma tunda kika ga yazo to tabbas wajanki yazo, amma ko a haka kinyi kyau matuƙa".

Godiya tayi mata kana ta ɗauko mayafi ta yafa sannan ta kama hanyar fita, tafiya take amma duk sai jinta take wata iri saboda rabonta da tayi shiri irin haka har ta manta bare azo  ga zancin turare, wajan da wata mota take taga yaron ta ya buɗe motar yashiga, dan haka itama ta ƙarasa wajan motar batare da tashiga ba, a hankali ta duƙar da kanta ƙasa cikin murya mai ɗaukar hankali tace,

" Daddy su ka ƙaraso daga ciki".
Tafaɗi haka a ɗan shagwaɓe.

Girgiza kai ya yi yace,

" Kishigo  ciki nan ma ya isa".

Sai da ta numfasa sannan ta buɗe mota tashigo saboda bata son yi masa jayayya.

Bayan tashiga ta zauna haɗi da gaishe shi sannan yace,

" Sai da aka jamin aji za'a fito?".

Murmushi tayi masa haɗi da dayi masa wani kallo mai riƙitarwa tace,

MIJIN BABATA NEWhere stories live. Discover now