16

156 6 0
                                    

*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*


*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

               *Z.W.F.🏝️*

*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*



*SHAFI NA 27*

Haka ya bar Mumy ba ko ƙwandala yaje ya kashewa matar sa ya saya mata kayan ƙarin jini, dan yace itace ke buƙatar abubuwan ƙarin jini ba Mumy ba.

Da ƙarfinshi ya shiga gida sai jin daɗi yake ya kawo mata abin mutsa baki, tun a ƙofar ɗaki ya fara kiran,

" Summy nah, zo gani na dawo".

Kwance take kan kujerar falo amma tayi masa banza har ya gaji ya shigo ɗakin da kanshi.

Ledar dake hannusa ya aje kana ya ƙarasa gareta yana faɗar,

" Lafiya dai ko? ba dai wani abu ke miki ciyo ba?".

Sai da ta  yatsani fuska sannan tace,

" Lafiya nake, ina abinda nace ka sayo min dan wallah idan har baka sayo min abubuwan gina jiki  wallahi gidan ubana zanje, na gaji kullum kaina babu , kamar gareka aka halaci babu".

Jiki na rawa ya bata ledar da yazo da ita kana ya bata haƙuri haɗi da faɗin  ,

" Kiyi haƙuri Summy nah, nasan nan gaba komai zai dai-dai ta".

Harara ta galla masa tace,

" Ni katashi kabar wajannan bana son warin turarinka amai zai sani".

A sanyaye ya tashi ya shiga bedroom itako ta buɗe lada tana cin abinda ya sayo mata.

Haka Kabir da Summy suka cigaba da raino ciki har ya kai watan haihuwa, kuma har yau gidanta yake kwana, amma saboda bala'in ta ko baccin kirki baya yi, in har yana so ya yi bacci, to idan ya fita gidan Mumy zai je susha soyayyar su sannan yaci ya ƙoshi, saboda ita Mumy bata damu da Kabir sai ya kawo ba a'a yanzu haka sana'a take tana rufama kanta asiri, wani lokacin wajanta ne Kabir ke samun na kai wa Summy.

Yau ma kamar haka Kabir ne yazo wajan Mumy saboda kuɗi ya ke so ya saye ragon suna tun kafin a haihu, shiyasa yanzu ko da yaushe yana gidan Mumy yana kashe ta da soyayya, itako sarkin son soyayya sai wani daɗi take ji tana farin ciki.

Suna kan gado sun lule a duniyar ma'arata, wayar Kabir ta fara rura, bai kula ba har sai da akayi masa kira bakwai sannan ya ɗauka, yana ɗauka yaga sunan Yayarshi, da sauri ya ɗauka, tun bai yi magana ba tace,

Kazo gamu asibiti Summy ta haihu ansamu ƴa mace".

" Yaya me kika ce, an haihu".

Asibitin da suke ya tamɓaya kana yayi wanka yasa jalabiyarshi yafice, har ya fita ya dawo yacewa Mumy ta bashi wani abu yatafi asibiti yasan dole idan yazo ayi masa zanci kuɗi kuma wallahi bai dasu".

Abinka da so hana ganin laifi sai taji duk ya bata tausai, ɗaki tashiga ta ɗauko masa dubu biyar ta bashi, ko godiya bai yi mata ba ya fice.

Tunda Kabir ya ɗaura idonshi akan ƴarshi yaji duk duniya ba abinda yake so sama da ita.

  ****************
Tunda Ahamd ya fita bai dawo gida ba sai dare.

Koda ya shigo gidan lkiram ya fara cin karo da ita tsakar gida tana bawa yaronta no-no, gaishe dashi tayi ya karɓa sannan ya tambaye ta ina  Mamarsu.

Mama najin ya ambace ta ta fito daga ɗaki jiki ba ƙwari tace,

" Ahamd ka dawo? ina kaje tun ɗazo yau ko abinci rana baka ciba".

"Mama bana jin yunwa".

" Tau Ahamd dan Allah kuyi haƙuri da yadda ƙaddara tazo muku, wallahi haka ta faru ba dan son raina ba.....kuka ne ya kuɓuce mata, dan haka Ahamd yazo yace ta daina kuka, kowa baya wuce kaddarar sa, haka dai suka fahinci juna har ta shirya da yaranta, koda mijinta ya dawo ta gaya mishi yayi haƙuri ya daina zuwa gidanta har ƴar ta gama wanka jego sannan ya dawo, yace wallahi bazai yadda da haka ba, dan shi yana buƙatar hakkinsa.

Ikiram da ke jin duk abinda yake wakana tace ita ko zata koya masa hankali kafin ta gama wanka tunda shima ba gidan ubansa ba ne.
      ................................

Matashiyar budurwace ya gani tana masa murmushi irin nasu na ƴan duniya, kallo ya ƙara mata tsaf, lokaci ɗaya kuma sai ranshi ya ɓaci, ai wannan  rainin wayu ne, mace tazo tana lalubar sumar kan ka.

A zuci ya buɗa baki yana mata wani kallon walaƙanci yace,

" Lafiya kowa?".

Murmushi ta ƙara yimasa haɗi da kashe masa ido ɗaya. jikinshi ta ɗan kwanto kaɗan har suna jin saukar numfashi juna, lokaci ɗaya ranshi ya ƙara ɓace, basan lokacin da ya tun kuɗeta haɗi da wanke ta da wani gigitacin mari  wanda saboda bala'in marin bata san lokacin da takai  ƙasa ba.

Nunin ta ya farayi da ɗan yatsa yana cika yana batsewa, kasa magana yayi kwai ya ɗau kye ɗin mutarsa ya kama hanyar fita.

Tana ganin zai fita itako tayi sauri ta tashi cikin azama tashiga wani ɗaki, ba ɓata lokaci sai gata tafito ita da wasu samari su huɗu, kallo ɗaya zakayi musu ka gane cewa imaninsu ragagge na, hanyar da yabi suka bi cikin azama.

Babu inda abokanshi basu nemeshi ba, amma baya nan kuma sun kira wayarshi kashe, dan haka suka yanke shawarar kowa yayi tafiyarshi, duk lakacin da ya gadama ya dawo yashiga wajan amaryarshi shi kaɗa.

Tunda aka shigo da Hansa'u ɗakin take kuka har bacce yayi awon gaba da ita babu Abdulrazaka babu labarinshi.

Tajima tana bacci sannan ta tashi ta gyara jikinta sannan ta je wajan Hajiyar Abbanta, koda taje zaune ta sameta tasa maganin mata gaba tana sha.

Kallon ta Hauwa tayi sama da ƙasa kana tace,

" Hajiya wai me zakiyi da waɗannan kayan mata naga kullum nazo sai naga kina shan su".

Wani kallon tayi mata na baki da hankali, sai da Hajiya ta ɗan sha sannan tace,

" Mijina nake shama kayan mata tunda ke kin fison ki zauna baki da aure".

Tsaki Hauwa tayi haɗi faɗin,

" Anyi asara wallahi mutum da tsofansa amma sai jaraba".

Ta faɗi haka ƙasa-ƙasa ta yadda Hajiya bazata ji me tace ba.

Hajiya tace,

" Mike kace?".

"Ban ce komai ba, mamaki nake yaushe kikama samu miji da zaki ce mijinki kika shama?".

"Ke yarinyar nan ban son sakarci fa, jiya aka ɗaura min aure, kuma idan kinyi musu kije ki tambaye liman ɗin unguwar nan jiya bayan sallar Jumu'a aka ɗaura min aure".

Tsaki Hauwa tayi tace,

" Hajiya miyasa baki gajiya da aure dan Allah, ke gaki kullum aure?".

" Ke ubanki shegiya, tunda ke bazakiyi ba wallahi bazaki hana min ba, gwara na mutu da aure na yafimin dana mutu mussai".

Tsaki Hauwa taje tace,

" Naji, wai ina ne gidansu Ahamd?"'.

Kwatancin gida Hajiya tayi mata sannan ta fito tare da faɗin asha amarci lafiya.

Kai tsaye Hauwa gidansu Ahmad ta nufa....

*Comment and share*



*SUMMY M NA'IGE✍️*

MIJIN BABATA NEWhere stories live. Discover now