41

164 10 4
                                    

*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*



*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*

      

*SHAFI NA 41*

Yana ganin number bai tsaya ɓata lokaci ba yasa kira, Mumy na waje tana haɗa musu abin kalaci sai taji wayar ta na ƙara, kamar bazata tashi ba kuma sai ta tashi taje ta ɗauko wayar,  number ce ba suna, ɗauka tayi tare da yin sallama, karɓawa ya yi yana sun kuyar da kansa ƙasa kamar yana gabanta. gaishe ta ya yi kana ya sanar da ita ko waye.

Amsawa tayi ciki da fara'a tace,

" Abdurazak ne? ya kake kuma ya aiki?".

Amsawa ya yi ciki da girmamawa yace,

" Alhmdullah Mumy. ya mai jiki?".

Ƙarɓa masa tayi tare da faɗar "Alhmdllh bari na bata".

Tun bai yi magana ba Mumy ta ƙaraso wajan da Hansa'u ke kwanci ta bata wayar batare da ta gaya mata ko waye ba.

Karɓa tayi bacci bai ida sakinta ba, wayar ta kara a kunninta tare da yin sallama, karɓawa ya yi tare da faɗar,

" Ke baki iya kiran mijinki ki gaishe dashi kin ji shi shuru, wai kowa kin iya kula da miji ?".

Baki ta turu gaba har ta buɗa baki zatayi magana kuma sai ta fasa, sai da ya sake mai-matawa kana tace,

" To ni banda number shiya sa, kuma baka neme ni ba".
Ta kai ƙarahin zan ci tana tura baki gaba.

" Dole ki faɗi haka tunda ita Mumy kina da number ta kuma kina kiran ta".

Ya jima yana janta da fira har dai ta ɗan saki jiki  suka yi fira harda dariya, daga ƙarshe yace ta fara shiri saboda satin nan zai dawo kuma da ya dawo zan ɗauke ta su tafi  Germany .

Tace,  "a'a ni karatu nake ba inda zan je".

Murmushi ya yi kana yace,

" Karki soma faɗar wannan maganar gaban Mumy, yasin idan haka ta faru kuma tace bazaki jeba zanyi tafiya ta, wataƙila idan na tafi zan jima ban dawo ba, ke kilama na samu yar yarinyar na aure".

Kukan shaguwaba tayi masa tana faɗar
"Wallahi yaya karka saki faɗar haka, dariya yayi mata, bayan sun gama fira ya yi mata sallama  haɗi da katsi wayar.

     ******

Kabir na isa gidanshi, bai tsaya wata shawara ba ya ɗauko ta karda ya rubutawa Mumy saki, wanka ya yi kana ya shirya batare da yacewa Matarshi komai ba ya kama hanyar zuwa gidan iyayen Mumy.

Bayan Innar Mumy ta fito ba ko gaisuwa ya bata takarda, lnna Mumy ciki da mamaki tace,

" Kabiru kai ne? baza shigo cikin gidan ba?".

" Dama ba dan na shigo nazo ba" . ta karda ya bata sai da ta karɓa sannan tace a ba Mumy takardar sakinta ce.

Sai lnnar Mumy tace,

" Kaje ka kaimata da kanka, saboda lokacin da kukayi aure bani na ɗaura maka ita ba da har zaka wanke ido ka kawo min takarda !".

Bai tsaya ya bata amsa ba ya yi tafiyarshi ya koma gidansa.

Bayan tafiyarshi lnnar Mumy ta shigo gida ta ɗau waya ta kira Mumy ta gaya mata rashin kunyar da Kabir ya yi mata, ajiyar zuciya mai nauyi Mumy ta sauke lokacin da ta gama jin abinda mahaifiyarta ke gaya mata tace,

" Inna karki wani damu, haka Allah ya ruburamin tawa ƙaddara, kuma ina roƙon Allah yasa haka shine mafi alhairi gareni".

Da ameen lnna ta ƙarɓa sannan sukayi sallama akan sai tazo.

Mumy na kammala waya da lnnarta ta cigaba da aikin da take batare da ta gayawa Hansa'u halin da ake ciki ba.

          ********

Yau Kabir kwanan shi biyu da rabuwa da Mumy, kwance yake sai baccin da yasaba yake, ita kuma matarshi yau koda suka tashi babu abinda za su ci, ga ƴarta sai famar kuka take mata, ɗaki ta shiga dan  ta ƙara gayawa Kabir basu da abinci, kwance ta sameshi sai famar bacci yake abinshi.

Wani irin baƙin ciki ne ya rufe ta, dan haka ta je inada yake kwance ta yaye mayafin da ya yi rufa dashi tace,

" Dan Allah katashi, tun shekaranjiya kanan kwance kuma kasan bamu da abinda zamuci, ai wannan zalunci ne! kasan baka da ƙarfi kaci da iyali amma ka kawo mutum ya zauna yunwa ta kashe shi, wallahi bazan iya ba, in har bazaka tashi kaje nema ba to wallahi gidanmu nayi yanzu idan katashi zaman aure dani ka sameni gidan ubana !".

Tana gama faɗar haka ta saɓa yarinya a baya tasa hijab zata bar gidan.

Da sauri ya tashi yace,

" Haba Summy dan Allah karki tafi wallahi ina sonki kiyi hakuri ki irin ƴan dubarun nan naku na mata dan Allah kinji ƴar albarka".
Ya faɗi haka kamar ya durƙusa gabanta.

Wani kallo ta watsa masa kana tace,

" Kutumar uban so, idan ka iya ka mutu kwance".

Tana gama faɗar haka ta kama hanya ta bar gidan.

Yana ganin ta fice ya ɗaura hannu akai to ya zaiyi, ina zai je ya samu kuɗi, ai ita Yasira ko bai kawo ba dafawa take su ci, ko dan ita Summy taga yana sonta ne.....

*SUMMY M NA'IGGE✍️*

MIJIN BABATA NEWhere stories live. Discover now