22

184 13 1
                                    

*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*


*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

               *Z.W.F.🏝️*

     *MARUBUCIYA*
*UMMU JA'AFAR✍️*


*SHAFI NA 22*

Shirye-shiryen aure kawai su Mumy keyi ba kama hannu yaro, Mumy da kanta taje dubai ta haɗu lefe nagani na faɗa wadda za'akai gobe, Abdulrazak naganin haka hankalinshi ya tashi dan haka ba wani ɓata lokaci yaje yasanar da Kakarshi wato Mahaifiyar Daddy Hajiya Ayya, koda yaje ya sanar da ita wannan lokacin ko kollo bai isheta ba, dan Daddy ya gaya mata halin da yake so yaje fa kanshi, dan haka itama tayi na'am da ayi masa aure, sosai tayi masa faɗa wannan lokaci sannan tace ya tashi ya bar mata gidanta yaje shima ya gayama abokansa su fara shirin aure.

Babu yadda zaiyi dan haka ya zubawa sarautar Allah ido, dan wallahi har ga Allah ba son wannan yarinya da za'a aura masa yake ba, amma ba yadda ya iya tunda sunƙi saurarishi, dan haka ko anyi aure dole wannan yarinyar tayi haƙuri dashi.

Yau aka kai lefe akasa sati biyi masu zuwa za'ayi aure, part ɗaya Dady ya gyara masa na cikin gidan da suke yace ya fara zama zuwa wani lokaci idan yaga yanayin zaman nasu sai ya tare gidanshi da yagama gini.

Baice da Daddy komai ba dan shi wannan auren baya gabanshi, Mumy da Hansa'u sai hidimar biki suke, duk da yanzu Hansa'u bazama takeyi ba saboda Daddy ya mayar da ita makaranta, da tadawo makarantar boko batawani tsayawa ɓata lokaci zata je islamiya, yanzu Hansa'u ta ƙara girma da kyau, ba namijin da zai ganta baiji zai sota ba.

Komai na biki Mumy tayiwa Hansa'u, idan kaga Hansa'u da Mumy kace itace ta haifeta saboda hasken da ke da Mumy sai haskensu yaso yazo iri ɗaya.

   ====================

Duk inda hankalin Mumy yake to ba shakka ya tashi ga wannan lamari na rashi ganin mijinta, yau ta yanke shawara ko bai zo ba zata je nemanshi gidansa saboda bata san halin da yake ciki ba, tana cikin wannan tunani sai taji an shogo gidan, da sauri ta ɗaga kai taga ko waye, shi tagani tsaye sai aika mata harara yake, da sauri ta tashi ta isa gareshi haɗi da rungumishi tace,

" Sannu da zuwa ango".

Ko kallonta baiyi ba ya fara tafiya har ya karaso ɗiki, zama yayi jiki na rawa taje ta kawo masa ruwa ta aje gabansa, saman cinyarshi ta tafi ta  zauna sai yayi sauri ya dagakatar da ita yace,

" Ya haka! yanzu kin san dai ba huruminki bane ki zauna saman jikina ko?  yana da kyau ki haɗiya duk abinda kikeji har nadawo gareki, yanzu hurumin amarya ne".

Jiki a sanyaye ta samu waje ta zauna kana tace,

" Kayi haƙuri bazan sake ba, amma kasan bakayi min adalci ba, ace yau kusan kwana huɗu bansaka a ido ba, kuma ba wani aiki da kayi min?".

Sai da ya watsa mata harara kana yace,

" Na zo nayi miki me? ranar da kika je biki kin tsaya har aka kawo amarya ko kinje ganin amarya ne? aikuwa kinga baki nemi na zo gidanki ba".

Ido ta kifa masa kana tace,

" Ai gani nayi ita amaryar ya dace ta zo ta gaishe ni ba ni ba, tunda itace ƙarama".....tun bata rufe baki ba yace,

" Ni bawani zancin kece babba ko itace ƙarama ni duk ɗaya na ɗauke ko, dan haka muddin kina neman zaman lafiya ni dake dole ki zo ganin amarya".

Yana faɗar haka ya tashi ya aje mata ɗari biyu ya kama hanya zai fita, da sauri ta tashi tace,

" ɗari biyu namiye ka aje min?".

Kisamu abinda zaki ci, kuma kar rana ta faɗi baki je ganin amarya ba, sai in nuna min zakiyi kinyi baƙin ciki da aure na".

Yana faɗar haka yafice batare da ya tsaya yaji mi zata ce ba.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta tashi ta fara gyaran gida, cikin lokaci kaɗan ta gama shirin ta na zuwa ganin amarya dan so take yau har gidan Hajiya Sa'a Kakar Hansa'u taje taga ko Hansa'u na lafiya.

   Koda aka isa asbiti da Inna ko numafashi batayi gaba ɗaya jikinta ya saki, taimakon gaugawa aka bata, cikin ƙanƙanin lokaci aka samu numfashin ya dawo dai-dai.

Koda Hauwa ta isa asibiti ansamu ceto ran mahaifiyarta, dan haka kai tsaye inda aka kwantar da ɗanta ta tafi, tafiya take kamar wata zararriya, yau da zata samu hawaye sufita idonta data ji daɗi, ashe ko hawaye rahama ce.

Dai-dai wannan lokacin ta isa ɗaki da akace ɗanta yake, mahaifinshi tagani shida ƴan uwanshi tsaye, da sauri ta ƙaraso garesu tana tambayar ina yaron yake yajikin nashi, ido mahaifinshi ya ɗago ciki da ƙwalla yace,

" Miyisa zaki damu? wanda ke son yaronshi ko ƴaƴanshi shi zai damu idan aka ce wani abu yasame ƴaronshi, dan haka ki gaggauta barin wajannan tun ban shukka miki rashin mutunci ba, yaro ne Allah ya ƙarɓi abinsa, sai kizoba ruwa a ƙasa kishi".

Yana faɗin haka hawaye na fita a idonshi.

Itama tana ganin haka lokacin ta durgusa gabansa tana kuka mai taɓa zuciyar mai sauraro, a halin yanzu Hauwa tayi nadama babba wadda take gani bata da anfani, saboda ita gani take lokacinta ne yayi.

Hashim wato mijin Hauwa a da, yana jin tafara kuka ya bar waja haɗi da ɗaukar gawar yaroshi suka tafi gida suka barta durkushi sai kuka take babu mai rarrashin ta.

Tana cikin haka ta tuna da lnna, miƙewa tayi kamar ba Hauwa ƴar wanka ba ta kama hanya tana tafiya kamar zararriya.

    Sosai Mamar Ahamd tayi Kuka haɗi da dana sani, tunin yadda zata gayawa waɗannan yaran cewa ba ta aure aka haifesu, abinda iyayenta suka gujemata ita ko lokacin idota sun rufe bata ji bata gani in har bata tare da Abbas.

Fura suke sayarwa, fura mai kyau da daɗi, to idan ba'asar cikin gida ba takan fita da ita cikin unguwa ta kai gidaje, amma ko cikin unguwa layinsu kawai akace tashiga ta kai, watarana tafito wani gida sai ga Abbas zai bi ta hanyar ya koma gidanshi na hutawa sai yaga fura da yake shi masoyin furar ne kuma ko fura irin wannan ta gida, dan haka ya tsaya ya saye, tun wajan yasha yaji tayi masa sosai dan haka yacewa yarinyar dan Allah tashigo mota ya nuna mata gidanshi kullum yana so ta kai masa ta ɗari biyar, ita kuma jin ya ambaci kuɗi maso yawa ne yasa tashiga motar ciki da farin ciki dan taga gidan nashi, bayan layensu ne yake gaba kaɗan, bayan taga gida ya bata kuɗi yace taje tashiga napep ta koma gida gobe war haka yana jiranta ta kawo masa, haka ta koma gida ciki da farin ciki tagayawa lnnarta wani gida sunci arika kai musu fura har ta ɗari biyar.

Sosai lnna taji daɗi dan haka tundaga lokaci kullum  sai ta kai masa fura yasaye.

Ranar koda taje yana cikin ɗaki yana cin naman gaza yana kallon , sallama tayi kai tsaye yace tashigo, bata kawo komai a rantaba tashiga, sosai taji kunya irin yadda ta sameshi daga shi sai ƙaramin wando, kai ta sunce ƙasa har ta bashi fura, shiko tunda tashigo yakifata da ido yana kallonta, a hankali ya baɗe baki yayi mata magana yace kuma sai taci naman kazar, tace a'a itakam ta koshi yace tabbas sai taci in basu take ranshi ya ɓaci ba, itako ganinshi babba yasa taji baza ta iya tsayawa ja inja dashi ba, dan haka ta fara ci a hankali shima yana ci, bata ci da yawa ba na tashi ya bani kuɗi har da na napep na dawo gida, tundaga lokacin idan na kaiwa Abbas fura sai munci nama da madara, tun ban sababa har nazo nasaba nasaki jiki dashi har takai zai iya ɗaura hannu ajikina muna wasa, wasa-wasa mukayi sabo da Abbas har maganar aure tashiga tsakaninmu, ina son Abbas so na gaskiya haka yasa nabashi kaina, ban ankaraba sai da naganin ɗauke da ciki, nayi kuka har nagaji musamman da iyayena suga gane ina da ciki, nasha duka nashaga wani hali sosai wallahi ban taɓa tunani ciki zai zauna ba a yadda nasha wahala, tundaga lokacin aka hanani fita koda soron gidane har nazo na haife Ahamd, iyayena suka ɗauke ni muka tafi gidanshi aka kai yaron, sai matarshi tace bazata karɓa ba, dan haka mukaje wajan mahaifiyarshi itace tace sun yarda wannan jininsu ne kuma za su bashi kulawa har dashi kanshi Abbas haka yace, akayi yarjejeniyar zai aureni, dan haka iyayena suka aminci naci gaba da shayar da Ahamd, to haka da'akayi ne yasa Abbas ya fara zuwa gidannmu har yana ɗaukana da mota muna fita, tun yana nemana ina ƙi har yasamu na aminci masa idan yazo ko cikin motane sai yadda yagadama dani haka yake , Ahamd na da wata goma sai ga cikin ya bayyana a jikina na, to tunda Abbas ya gane ina da ciki ya daina zuwa wajena gaba ɗaya na nemeshi narasa har na hafi lkiram bai sani ba, bayan na haihu ne mahaifina ya koreni daga gidanshi yace na farko ya ɗaukeshi a matsayin kaddara amma wannan ba kaddara bace dan haka ya barwa duniya ni....


*Commen and share*



*SUMMY M NA'IGE✍️*

MIJIN BABATA NEWhere stories live. Discover now