32

155 9 1
                                    

*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*


*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

               *Z.W.F.🏝️*

*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*

*SHAFI NA 32*

Bayan sun gama bikin makaranta haka kowa ya dawo gida ciki da jimamin ɗan uwansa, sosai suka ji zafin rabuwar su, kuma wasu shekenan aure zasu yi, wasu za su cigaba da karatu, cikin masu cigaba da karatu harda Hansa'u.

  Cikim ƙanƙanin lokaci ta samu gurbi a Usuman dan fodiyo university, bata ɗau lokaci ba ta fara zuwa makaranta ranar zuwan ta na farko ne ta haɗu da wasu ƙawaye masu kirki, lokaci ɗaya jinsu ya huɗu ba ɓata lokaci suka kulla ƙawance, sosai suka fahinci junan su saboda basu da matsala a yadda ta karance su.

Haka taci gaba da zuwa makaranta ita da ƙawayen ta, gaba ɗaya yanzu jin take kamar bata da aure, saboda yanzu ko part ɗinta ta daina zama ta koma na Mumy ɗakinta na da da zama saboda gani take zama wancan part duk ta kurane, shiyasa yanzu take shige kamar yadda ƙawayenta Aysha da Zainab da Safiya keyi, yanzu haka  tunda Yayan Zainab yaga Hansa'u yaji ta kwanta mishi arai, a dai idan Zainab tace ya kawo ta makaranta kamar ya dake ta, amma yanzu har shi ke cewa shi zai kawo ta, ita ma da ta fahinci Hansa'u yake so taji daɗi sosai dan tasan yayanta yayi dace mata, dan Hansa'u akwai kirki da kuma daraja muta ne.
Ana cikin haka bikin Safiya ya tashi, kuma su Hansa'u sune ƴan mata, dan haka koda aka tashi bata koma gida ba, gidan su Safiya suka tafi har yamma bata dawo ba, Yayan Zainab na zuwa ɗaukarta itama tace zata gida ko napep tashiga saboda ba'a zo ɗaukar ta ba, Zainab tace a'a sai da sutafi a ajeyeta sai su tafi, haka kuwa ta kasance.

Sallama sukayiwa Safiya tayi musu rakiya har ƙofar gida sannan ta dawo.

Gidan gaba Zainab ta buɗewa Hansa'u tace tashiga tace,

" A'a ki shiga bari na koma gidan baya tunda nice za'a fara saukewa".

Zainab bata bi takan Hansa'u ba tashiga gidan baya, Hansa'u da taga babu yadda zatayi dole tashiga gidan gaba cike da jin kunya.

A hankali suka tafiya har suka kawo anguwarsu, dai-dai bakin get ɗin gida sukayi packing, dai-dai lokacin wata kyakyawar muta fara sol tafito gidan, motar da ke tsaye bakin get ɗin gidan yabi da kallo, Hansa'u yaga tafito cikin motar lokaci ɗaya gabanshi ya faɗi, itako a tunaninta Daddy ne shiyasa ko sallama bata yi musu ba tashigo gida jiki na karkarwa.

Shima Yayan Zainab bai tsaya Zainab ta dawo gidan gaba ba ya ja mota suka tafi.

Tsaki yaje haɗi da jan motar da gudu ya hau ti-ti, har ya yi nisa kaɗan sai kuma mi ya tuna ya juyo kan motar ya dawo gida.

     ******
Ƙarfe huɗun na dare Mumy ta faraka ta ɗaura alwala ta fara fabatar da sallar nafila, har akayi kiran sallaha, bayan tayi sallah asuba ta koma bacci, yanzu gaba ɗaya Kabir mamakin Mumy yake saboda ta canja masa ba kamar da ba.

Bayan ta tashi ta ɗaura musu abin kari sannan ta nemi izini zata tafi gida taga mahaifiyar ta.

   Ba ɓata lokaci Ahamd yazo gida, koda ya zo Hauwa sai safa da marwa take tsakar gida ita dai lkiram ta rasa mi akayiwa Hauwa take haka.

Lokacin da Ahamd ya zo gidan wata sassanyar ajiyar zuciya ta sauke kana tace,

" Ka k'araso Ahamad?".

Nuna masa kujera tayi tace ya zauna bayan ya zauna tace,

" Ahamd wai da gaske abinda naji ance aure zakayi kuma har ka kawo matar da zaka aura wajan Mama?".

Murmushi ya yi mai ɗauke da tsantsanr farin ciki kana yace,

" Da gaske ne, daman abinda yasa ke ban kai ta wajanki ba nasan kin santa shiyasa nace yau zamuyi maganar".

Gaban Hauwa ne ya faɗi tace,

" Kar dai ace wadda nake zargice ka ke nufi aure?".

Murmushi ya yi yace,

" Hajiya Binta ce koma nace ƙawarki ce....kayimin shuru Ahamd, kana hauka ne! Karasa wazaka aura sai Hajiya Binta, sannan kan kane ba sai na gaya maka asalinmu ba, kuma duk wanda ke cikin a halin irin namu neman sauyi yake , muna cikin neman sauyi zaka ɗauko muna wata ɓata gurbi, dan haka nake shawartar ka da tun wuri ka aje zancin ta, kasamu wata amma ba ita ba".

Wani kallo ya bi Hauwa dashi kana yace,

"Wannan wace irin magana ce Hauwa, ƙawarki ce fa, kuma ke kika haɗani da ita, kin san ɓata gurbice sannan zaki haɗani da ita, kuma yadda kike so mu sauya rayuwa haka itama take so, shiyasa tace muyi aure saboda mu gyara farnar da muka aikata....





*Commen and share*

*SUMMY M NA'IGE✍️*

MIJIN BABATA NEWhere stories live. Discover now