37

139 14 3
                                    

*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*


*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

               *Z.W.F.🏝️*

*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*

      

*SHAFI NA 37*

Tashi ya yi kai tsaye gidan Kakar shi ya nufa, koda ya je zaune take tana saurarin rediyo, da sallama ya shiga , karɓawa tayi kana ya samu waje ya zauna duk ranshi haɗe.
Duban shi tayi da kyau kana tace,

" Kai lafiya ka shigo gida duk ranka haɗa? waya taɓa min kai babban maigida !".

" Hajiya abinda ake min ne a gidan nan ya isheni, ace yarinyar nan duk inda ta ga dama zata fita batare da na sani ba, to miyasa za'ayi min haka, ko ni ba mijinta ba ne !".

" Wace yarinya kenan?".
"Hansa'u ".
Haka yace da ita kai tsaye.
" Kajimin ja'iri, to ba yarinya taga mahaifitar ta, ita tazo ta ɗauke ta da sunan idan taji sauki ta dawo da ita, tunda kai har zaka tsalaka kabar matar ka babu lafiya baka damu ba!".

" Yaushe ta haɗu da Mamarta, ai ni ba wanda ya gaya min Hajiya, tun safe nake tambayar Mumy ina take amma bata kula ni ba, kuma Hajiya tafiya zan sakiyi zuwa ƙasar waje, to kinga wajan da nake akwai haɗari mutum ya zauna batare da mata ba, dan haka nake so ki gayawa Mumy abani matata dan Allah Hajiya natafi da ita".

" Kwantar da hankalinka maigidana, ai ko dama sai da aka gayawa ita mahaifiyar yarinyar da ka dawo yarinya zata dawo ɗakinta, yanzu wai kana nufi ita mahaifiyarka bata gaya maka ba, bare har kaje ka gano ya jikin yarinyar yake?".

" Wallah bata gaya min ba, shine na tambayeki idan kin sani ki gaya min?".

" Bansani ba, amma shi mahaifinka ya sani, ɗauko min waya gata can na kira shi yanzu zai gaya min idan unguwar tasu take sai kaje".

Godiya ya yi ma Hajiya, sannan ya ɗauko mata wayar ta, kiran Alhaji tayi haɗi da ɗanyi masa faɗa, ya za'a tafi da yarinya batare da mijinta ya sani ba, kodan sun aura mishi ita ne za su ce sune da ikonta, sai da tayi masa faɗa ta gaji sannan tace to ya gaya mata sunan unguwar da yarinyar take.

Haƙuri ya bata haɗi da ƙanƙan da kai, kana yace,

" Yanzu zan turu dire ba ya kaiki idan yarinyar take".

" To ina jira karka shanya ni !".
Tafaɗi haka tare da kashe wayar.
Dayaki duk abinda ake Abdul naji shiyasa bai tambaye ta ba yaci gaba da dannanr wayarshi.

Babu jimawa sai ga direba yazo har gidan, sallama Abdul ya yiwa Hajiya sannan suka tafi shi da direba, kowa motarshi yashiga suka kama hanya.

Har ƙofar gidan direba ya nuna masa sannan ya yi masa sallama ya koma, kallon unguwar ya fara, ai kamar wajan ne ya haɗu da ita ranar da ya ɗauko ta, tsaki ya yi kana ya samu yaro ya aikashi yace yaje yace ina kiran Hansa'u.

Koda yaron ya shiga Mumy da Kabir na tsakar gida, ita Mumy na aikin girki, shiko yana zaune kan ƙaramar kujera daga shi sai gajerin wando yana dannanr waya, amma a zahiri gaskiya da Hansa'u ta fito idonshi na kanta, shiyasa duk ta takura ta koma ɗaki, kuma bata iya barin Mumy na aiki ita kaɗai.

Yaro ya shigo da sallamarshi yace "ina kiran Hansa'u waje".

Gabanta ne ya yi masifar faɗuwa da taji haka, to wa tasni da za'a ce ana kiranta ,  Mumy ce tayi sauri tashi daga wajan da take ta dubi yaron tace,

" Wake kiranta?".

Sai yaron yace,
" Wani ne mai mota".

Sai Mumy tace "koma kace waye ke kiranta".

MIJIN BABATA NEWhere stories live. Discover now