21

208 12 0
                                    

*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*


*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

               *Z.W.F.🏝️*

     *MARUBUCIYA*
*UMMU JA'AFAR✍️*


*SHAFI NA 21*

Har Ahmad ya buɗa baki zai yi magana sai yaji anyi magana ta bayan sa ance,

" Wallahi Yaya gwara ka tsareta sai ta gaya muna waye mahaifin mu, wallahi nagaji da wannan gorin da ake min na rashin uba, wasu suce shegu muke ba da uba aka haifemu ba wasu ko suyi min gori akan tafiy son wannan mijin nata akai mu, wallahi Yaya nagaji, duba ka gani haihuwa nazo amma da yake ni bata sona tafisonshi akaina kullum suna cikin ɗaki ita da wannan mijin nata, to wai waye bai san abinda suke ba, ni ko kai, dan haka wallahi Mumy yau sai kin kai mu gidan uban mu,  da inada uba wannan ƙaton mijin naki bazai shigo gidannan ya kwana lafiya ba, gashi nan duk ya kalle min jiki, ko yaro nake shayarwa ya kefamin ido kenan to wallahi ki gaya masa ya kalle haram"....Ahmd ne ya ɗaga mata hannu ganin bata daniyar tsayawa ko tayi numfashi bare ta kai ƙarshin zancin.

Mijin Mama najin haka ya lalabu kayansa ya fice ɗaki batare da yayi mutsin da zasu fahinta ba, dan koda su Ahmad suka duba basu ganshi ba.

Mama kallonsu tayi da kyau kana tace,

" Wannan da na nuna muku to ba shakka shine mahaifinku, dan haka kuje ku sameshi ku tambayeshi".

" Eh naji Mama shine mahaifin mu to miyasa mutane ke faɗin mu shego ne? haka kenan yana nufin mu bata hanyar aure aka haifemu ba".

Cewar Ahmad kenan.

Hannu Mama ta ɗaura a kai ta sanya kuka  yau nutuwar ta ta zo, ashe haka ake ji idan yaro ya girma ya tambayeka ubanshi, tabbas sai yau take ƙara dana sani marar anfani.
Tayi wannan zanci cikin ranta zuciyar ta na ƙuna.

Da Ahamd yaga haka sai ya bar gidan ranshi a matuƙar ɓace.

        Alhaji Abu ne da amaryar sa zaune tsakar gida suna shan isaka suna ta fira haɗi da dariyar , suna cikin haka sai ga Hauwa tashigo gidan ko sallama babu, kallonta amaryar Alhaji Abu tayi tace,

" Hala ke baki iya sallama ba ne da zaki shigo gida ba sallama".

Ko kallonta Hauwa batayi ba saboda yanzu bala'in da take ciki yafi komai ɗaga mata hankali, dan yanzu aka aiko mata akace wani maƙocinsu ya je yaronta wani gida ya lalatashi yanzu haka suna asibuti kuma babu tabbas yaron ya tashi.

Ɗakin lnnarta tashiga, kwance ta tar da lnnarta, da sauri ta ƙarasa jikinta tana kuka, duk kukan da take lnna bata mutsaba har Hauwa ta gaji ta fara tashe ta, shuru bata tashi ba, gaban Hauwa ne ya faɗi, cikin hanzari ta fara girgizata amma shuru aikuwa Hauwa naganin haka ta ɗaura hannu saman kai ta fara ihu azo a taimake ta.

Da gudu Alhaji Abu da matanshi suka shiga ɗakin, halin da suka ga lnna ciki ne yasa suka ɗauke ta Alhaji Abu yace a kaita mota ya kaita asibiti.

Hauwa na kallo aka ɗauke lnna har suka shiga mota amma ta kasa koda mutsin kirki, wallahi tayi kuka kamar ranta zai fita.

Ita yanzu abinda yafi ɗaga mata hankali duk bai fi ace itace sanadin lalacewar Ahamd ba, gashi tun ba'aje ko ina ba Allah ya fara nuna mata abinta, ɗanta wanda tafiso shine aka lalata wataƙila ya tashi ko ya muto, sannan ga lnna wanga wani irin bala'i ne.

Hawayen da suka zuba a idonta ta shafe , kana ta tashi tashiga ban ɗaki ta watsa ruwa ko taji sanyi.

   Gari na waye wa mijin Mumy ya tashi itama ta tashi jiki a sanyaye ta haɗa musu beark, yashi kana ya shiga wanka, sosai yayi wanka ya wanku tas, wata shadda yasa fara ƙal sai ƙyalƙyale take, sak ya fito angonshi, yana cikin shiri abokansa suka zo suka ɗauke shi, har zai fita Mumy ta riƙo hannusa haɗi da faɗawa jikinsa tana saukar da wata ajiyar zuciya.

Janye ta yayi yace,

" ke sauri nake jirana ake lafiya?".

Bai jira jin mizata ce ba yayi tafiyarshi.

Yinin ranar haka Mumy tayi sanyi, har yamma tayi bai dawo ba kuma bata je gidan biki ba.

Tana zaune ya aiko mata da yaro ya kawo mata takarda wadda ke ɗauke dacewa wallahi duk bata zo gidansu biki ba sai yayi bala'in ɓata mata rai.

Tana gama karantawa ta tashi jiki na rawa tashirya, sosai Mumy tayi kyau, daman Mumy mai kyauce junin fulani, ƙaramin jiki ne ga Mumy shiyasa ba duk mutum ke yarda ace itace ta haifi Hansa'u ba, saboda idan suka jera da Hansa'u za'a ce ita ƙanuwar tace.

Mumy ta iya ido na gani na faɗa batada wata makosa.

Kai tsaye gidansu ta tafi, koda taje an fara shirin wanken ango, bayan ta gaishe da iyayensa tazo ta samu waje ta zauna ƴan uwanshi sai yadda mata magana suke, ana cikin haka sai gashi anzo dashi ƴan uwa suyi mishi wa'azi.

Ido huɗu suka haɗa ita dashi, gabanta ne ya faɗi saboda tsabar kyau da taga yayi mata, a wajanshi ma haka ne, saboda yana ganita yaga takoma mishi sak Hansa'u sai da ya ƙara dubanta sannan ya gane ita ce.

Ana farawa ango nashi wasu suna fakewa da nashi suna yadda mata magana dan haka ta tashi kowa bai sani ba ta bar gida.

Kai tsaye gidan mahaifiyar ta taje, da sallama tashiga gidan, karɓa mata tayi kana tashiga, ƴan uwanta mata suma yau sun zo gida ita kaɗay ce baba cikin ɗiyan Gwaggo, saboda tunda ta aure Kabir ko ance tazo gida ana nemanta bata zuwa shiyasa kowa ya barma Kabir ita.

Gwaggo ce ta kalleta tsaf sannan tace,

" Hala yau mijin naki bai san kinzo ba? ko kuma ɓatan hanya ne kimayi?".

" A'a Gwaggo daman cewa nayi bari nazo na gaisheku".

Yayarta ce tace,

" Ai ko mungode, Inna ƴata Hansa'u ko ita kin hana ta zuwa wajanmu saboda tana kawo muna ƙararki ko?".

" A'a wallahi nima najima bangan ta ba saboda ta koma gidan Kakarta Hajiya Sa'a".

Haka suka ciki gaba da fira daga baya Mumy tayi musu sallama ta koma gida, Gwaggo ciki da ta kaicin hali irin na Mumy.

  Tunda Kabir Yayi aure har yau kwana biyi Mumy bata sashi a idonta ba, tayi kiran waya har ta gaji amma yaƙi ɗagawa.

     Kai tsaye part ɗin Mumy ya wuce, zaune ya sameta tana waya da ƙawarta, bayan ta kammala wayar ne sai ya dube Mumy yace,

" Mumy dan Allah ina yarinyar da kuka ɗauke wancan gidan, wallahi Mumy ban ɗauko ta daniyar lalata taba, haka ban ɗaukota dan wata manfa ba, kawai na ɗaukota ne dan na taimaka mata".......hannu Mumy ta daga mishi tace yafita ya bar mata ɗaki bata son jin maganarsa, kuma daga yau yaje ya fara shirin aure dan lokaci na tafiya dan wallahi wannan lokaci aure ba fashi, tunda har ka iya sato mace ka kawo gidanka to tabbas zaka iya zama da mace, da awaye gari kayi wa mace ciki gwara ace yau an ɗaura maka aure".

Durƙusawa yayi gaban Mumy yace,

Dan Allah Mumy kuyi haƙuri, wallahi banda wata manfa akan ta".

Ya faɗi haka kamar zaiyi kuka.

Har Mumy zata buɗa baki tayi magana sai ga Hansa'u tafito cikin ɗaki.

Wajen da Mumy take tazo ta zauna, har zata zauna idonta ya faɗa cikin nashi, da sauri ta duƙar da kanta ƙasa ta gaishe shi, bai karɓa ba tsaki yaje sannan ya tashi ya bar wajan.

Bayan ta fiyarshi ne Mumy ke shaidawa Hansa'u wannan shine Yayanta, shine ɗan da suka haifa, ƙarshin watannan za'ayi masa aure da ɗiyar abokin Daddy shi, sati nasama zaa kai lefe.

Sosai Hansa'u tayi farin ciki da jin haka, lokaci ɗaya sai ta tuna da Babarta....


*Comment and share*

*SUMMY M NA'IGE✍️*

MIJIN BABATA NEWhere stories live. Discover now