35

153 11 3
                                    

*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*


*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

               *Z.W.F.🏝️*

*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*

      

*SHAFI NA 35*

Koda tashiga ɗakin Daddy yana zaune yana azkar ɗin safe, kallo ɗaya ya yi mata ya kauda kansa kyafe, saboda tun jiya fushi yake da ita, saboda tacewa ɗan su kar ya cutar da ɗiyar ta, kenan tafi son ta akanshi.

Mumy tajima zaune, amma da bata ga fuska ba dole ta tashi ta koma ɗakin ta, amma zuciyar ta duk ba daɗi.

Ya jima yana zagayen ɗaki sannan yaji alamar  tashigo war mota a gidan, da hanzari ya fita ko Aliyu ne, shine tare da matarsa, tun bai yi parking ɗin motar ba ya buɗe musu marfin mota, Aliyu bai kula shi ba har sai da ya yi parking sannan ya fito ita ma matarshi ta fito, gaishe da Abdulrazak tayi amma bai tsaya karɓawa ba yace tazo ya kaita ɗakin da Hansa'u take, ɗakin da Hansa'u take ya kaita, kallo ɗaya tayi mata tasan cewa tana jin jiki, dan haka tace Abdul ya basu waje, ba musu ya fice ya koma wajan Aliyu suna fira.

Dubanshi Aliyu ya yi da kyau kana yace,

" Wai kana nufin sai yanzu ka kula ta, gaskiya kaci amanarta, kuma yanzu kazo mata ta karfin tsiya har ka nemi ka halaka ta".

Ajiyar zuciya Abdul ya sauke kana yace,

" Kai dai kawai bar maganar dan ni ban san mi zan gayawa Mumy ba, yanzu haka bana so mu haɗa ido, da matarka ta gama dubata zan bar garin nan bata re da naga Mumy ba, saboda nasan da taga yarinyar nan haka ranta zai ɓaci kuma zata nuna min halinta".

Sun jima suna fira kafin lkilima matar Aliyu ta fito, takar da ta basu tace a sayo  magani saboda anyi mata ɗinki, idan akayi mata alura haɗi da magani zata samu sauki, sai da Aliyu ya zagi Abdul sannan suka fita suka sayo suka dawo, bayan sun bata tayi mata har da magani tasha, ba ɓata lokaci bacci ya yi awon gaba da ita, saboda har da alurar bacci akayi mata.

Yana ganin tasamu bacci ya je ya yi wanka ya shirya ya haɗa duk abinda zai buƙata yafito ya dube matar Aliyu yace taje ta sanar da Mumy halin da ake ciki dan shi kam bazai bari su haɗu ba, ko ba kunya yasan sai yashi faɗa.

Yana gama faɗar haka ya fice, Aliyu na kiran shi amma ko waigowa bai yi ba yaje mota ya bar gida.

Tsaki Aliyu ya yi kana yace,

" Shegen kaya ne Abdul fa, to tashi muje ki sanar da ita sai mu koma gida dan bacci bai gama isana ba".

Ba musu ta tashi suka je part ɗin Mumy, da sallam suka shiga, zaune take parlou tana kallo, kuma a zahirin gaskiya  ba kallo take ba tunanin yadda zata ganin yarinyar nan take, tana cikin haka taji salamar su, da sauri ta kai duban ta ga ƙofa, Aliyu tagani da matarshi, murmushi tayi haɗi da karɓa musu sallama.

Bayan sun zauna suka gaishe ta, amsawa tayi ciki da fara'a a fuskar ta.

Sun ɗan jima shuru sannan Aliyu ya katsi shuru da faɗar,

" Mumy Abdul ne yace mu gaya miki ga Hansa'u  babu lafiya, da yake tun cikin dare yace Hafsat tazo ta dubata, nace da safe zamu zo, to yanzu angama komai har anyi mata ɗinki, yace na gaya miki ya wuce abuja".

Tun ba ida maganar ba Mumy ta sauke numfashin mai ƙarfin gaske kana tace,

" Tau ba komai Aliyu na gode Hafsat, Allah ya yi muku albarka, yanzu da sauki ko?".

" Dukar da kanta Hafsat tayi kana tace,

" Eh Mumy da sauki yanzu haka tasamu bacci".

Godiya Mumy tayi mata kana ta haɗa ta da abin arziki sannan suka yi mata sallama suka koma  gidan.

MIJIN BABATA NEWhere stories live. Discover now