45

228 10 1
                                    

🏝️ *ZAFAFA WRITTERS FORUM* 🏝️

      

   🏝️ *Z.W. F* 🏝️

*🤦‍♀️🤦‍♀️MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*

         *Tsarawa da Rubutawa*
       *(UMMU JA'AFAR)*

          🔚🔚🔚

*ALHAMDULILLAH*

*KOMAI YA YI FARKO ZAIYI ƘARSHI DA IKON ALLAH, INA GODIYA GA ALLAH DA YA ARAMIN NUMFASHINA HAR ZUWA WANNAN LOKACI DANA KAMMALA KUMA CIKIN KOSHIN LAFIYA*

*SHAFI NA 45*

Yana isa ƙofar gidansu Mumy ya samu yaro yace ya shiga gidan yace ana kiran Yasira. ba musu haka yaron ya shiga gidan ya yi sallama kana ya faɗawa lnna abinda aka aiko shi.

Inna da ke zaune tsakar gida ta dubi yaron da kyau kana tace,

" To kace gata zuwa".

Haka yaron ya koma ya sanar da Kabir cewa gatanan zuwa.

Inna ko tashi tayi tashiga ɗakin Mumy ta sanar da ita ana kiranta, tambayar Inna tayi wake kiran ta, sai lnna tace idan ta fita zataga mai kiranta, ba dan ta so ba haka ta tashi ta shirya dan ta fita.

Mutuwar tsaye tayi lokacin da tayi arba da Kabir ƙofar gidansu sai safa da marwa yake, aikuwa yana ganinta da sauri ya ƙaraso gareta ta re da faɗa-ɗa murmushin shi,  har zata juya ta shiga gida saboda yanzu ganinshi bata son yi , da sauri ya sha gabanta yana faɗar,

" Dan Allah ki tsaya ko minti ɗaya ne ki bani ki ji abinda zan gaya miki".

Wani kallo tayi masa mai haɗi da yaronan ka rainani fa.

Ganin da ya yi bata yi magan ba yasa ya fara gyaran murya kana yace,

" Dan Allah kiyi hakuri ki yafe min wallahi  duk abinda na yi maki sharin shaiɗan ne".
yana magana kamar ya yi kuka, daga baya kuma yaci gaba da faɗar kuma daga yau na kama aure na saboda na duba gabas da yamma bana iya rayuwa da ko wace mace sai ke!".

Wani kallo tayi masa na baka da hankali tace,

" Yau wata huɗu da rabowar aurenka akai na taya zaka ce ka kama aurenka, malama katafi sai anjima".

Tana gama faɗar haka tashiga gida ta barshi baki buɗe yana kallonta har ta shiga.

Tana shiga gida ta gayawa lnna ko waye, aikuwa itama lnna ta fara masifa akan ya raina musu da wayo.

Kabir ya jima ƙofar gidan kafin ya tafi.
Tundaga ranar kullum Kabiri na ƙofar gidan ya samu yaro yace akirata, lnna ke leƙa wa da taga shine to bazata fito ba.

Da yaga ko ya aika a kirata bazata fito ba to sai yariƙa tare tsofaffi kan hanya yana cewa dan Allah su shiga su ba matarshi haƙuri ta dawo gare shi, su koma haka zasu ji tausayinshi su shiga su bawa lnna haƙuri sai ta gaya musu abinda ake ciki kafin su fita.

Kaf tsofaffin unguwar ba wanda Kabir ba aika ba akan sai Mumy ta dawo, sosai ya shiga tashin hankali na ganin Mumy na shirin ƙuɓuce masa , iyayenshi suma sun zo, abokanshi duk sun zo an ba Mumy haƙuri amma lnna ta rufi ido tace wallahi ita da Kabir sai lahira.

Ina cikin haka ranar Mumy ta fita ta sayo wani abu bakin ti-ti, saboda bata samu yaro ba, ba dan ta so ba haka tafi.

Tana kaiwa wajan shagon sai ga wani Alhaji ya tsaya da niyar ya saye abu, to tunda idonshi suka afka akan Mumy ya ji ta kwanta masa a rai, dan haka Mumy na barin wajan bai tsaya ɓata lokaci ba ya tambaye wasu mutane dan Allah wannan matar ina take, to da yake cikin waɗanda ya tambaya akwai Yayanta ciki sai ya tambaye shi lafiya yake niman gidansu.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 30, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MIJIN BABATA NEWhere stories live. Discover now