36

151 14 5
                                    

*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*


*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

               *Z.W.F.🏝️*

*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*

      

*SHAFI NA 36*

Kuma ta kasa tambayar kowa saboda kunya ta cika ta, saboda yanzu ta san kowa yasan miye ciyon ta, shiyasa har suka shiga mota bata ɗago da kanta ta dube su ba , sai da direba zai je Mumy Abdul tace,

" Hajiya sai nazo isha Allahu zan zo babu jimawa".

Godiya Mumy tayi mata sannan direba yaje dan ya tafi.

Lokacin Hansa'u ta ɗago kai ta dube Mumy saboda yanzu tasan ina zasu je, hannun Mumy ta riƙe tana so tayi magana amma takasa saboda kukan da yaci ƙarfin ta.

Hannunta Mumy ta janye sannan direba ya yi gaba, lokaci ɗaya Hansa'u ta sanya kuka tana faɗi ita bazata je ba.

Mumy bata kulata ba har suka isa gida, direba ya ɗau kayan su ya kai musu gida sannan Mumy taje hannuta suka shiga gida.

Godiya Mumy tayi wa diraba kana ya yi musu sallama ya koma gida.

Tana shiga gida ta fara dube-dube gidan yana nan yadda ta barshi ba'a ƙara masa komai ba, suna shiga parlour saman dogowar kijera ta kwanta sai hawaye kemata zuba a idonta.

Mumy bata kulata ba ta fito ta fara shirin abincin rana, ƴan uwatan da mahaifiyar ta takira ta gaya musu halin da ake ciki, sannan ta kira ƙawarta Hajiya Asiya mai gyaran amare ta shaida mata halin da ake ciki, sosai suka taya ta murna na ganin ƴarta, lokaci kaɗan gida ya fara cika da mutane ana zuwa ina mata ja-je.

Koda Hajiya Asiya ta zo tazo da kayan da za'a bata tasha da waɗanda za'a dafa mata saboda suna sun kafin gobe ta koma dai-dai.

Godiya Mumy tayi mata daga baya ta tafi sai koma idan kayan sun ƙare akawo mata wasu.

Har ƴan uwa da abokan Mumy suka zo suka tafi amma Kabir bai dawo ba kuma bai san wanar da ake tuyawa ba, saboda Mumy ta ɗau alwashin bazata sanar dashi ba har sai idonshi sun ganar masa.

Bayan Mutane sun watsi Mumy tayi mata yadda Hajiya Asiya tace, kuma cikin ikon Allah tafiyarta ta fara dawowa dai-dai, kuma sai taji sauki ciyon da take ji.

Bayan sallar isha Mumy ta ɗauko abinci tace Hansa'u tazo suci, da ƙyar dai Mumy ta samu tazo ta zauna suka fara cin abinci, a hankali Hansa'u ke ci, ita ko Mumy ta kifeta da ido tana kallonta, wani so da ƙaunar ta suna shigar ta, lokaci ɗaya hawaye suka fara fita a idon Mumy, Hansa'u bata kula ba, cin abin cin ta kawai take a hankali, shuru taga Mumy ta daina cin abinci ta ɗago ido ta kalleta, a razane tace,

" Mumy mike faruwa ki ke kuka?".

Girgiza kai Mumy tayi haɗi da jawo Hansa'u zuwa ga jikinta tace,

" Kiya femin ƴarta kinji, wallahi na cutar dake kuma na cutar da amanar da mahaifinki ya bani, dan Allah ki yafemin Hansa'u".
Mumy ta kai ƙarshin zanci hawaye masu zafi na fita a idonta.

Hannu Hansa'u tasa ta sharewa Mumy hawaye kana tace,

" Mumy ki daina kuka dan Allah, in har kina so kiga farin ciki na, to karki kuma zubar hawayenki, wallahi ina jin zafi matuƙa".

Murmushi Mumy tayi tace,

" insha Allahu na daina kinji ƴata".
Mumy ta faɗi haka tare da kara matsita jikinta.

Haka suka ci gaba da fira suna cin abinci, suna cikin haka sai ga Kabir yashigo gidan ba ko sallama, kai tsaye ɗakin ya wuce, mutuwar tsaye ya yi lokacin da yaga Hansa'u da Mumy suna cin abinci suna dariya kamar wasu ƙawaye.

MIJIN BABATA NEWhere stories live. Discover now