19

212 10 1
                                    

*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*


*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

               *Z.W.F.🏝️*

     *MARUBUCIYA*
*UMMU JA'AFAR✍️*


*SHAFI NA 19*

Har Hauwa zata ɓuda baki ta yi magana sai Inna tace

" karki kuskura ki gayawa mijina magana ai ko ba komai ubanki ne".

Abinda ke damunta ne yasa ta kyalesu ta fara ɗaukar kaya tana kaiwa ɗakin da yace, sai da ta kammala sannan lnna tashi ɗakin haɗi da zama gyafin katifa, kallonta Hauwa tayi idonta taf da hawaye tace,

" Kaicona lnna! lnna bakimin zaɓin uba ba wanda zan nunawa duniya nace shine ubana, kisana yau ina cikin ƙunci da ta kaicin kasancewa ta ƴa ga Babana, ashe lnna Baba na da ɗa Ahamd shine baki taɓa gaya min ba?".

Kallonta lnna tayi ciki da mamakin ta tace,

" Wani Ahamd kuma? ni dai nasan tunda mahaifinki ya sakeni bansanshi da wani ɗa ko ƴa ba wadda akace yau ya aure ya haifa, sai dai idan na matan da yake tare da sune, to wani abu ne ya faru?".

" Barshi kawai lnna bazaki gane ba, danshi ake so mutum yasan wanda zai aura".
Ta faɗi haka lokacin da take tashi ta bar ɗakin.

Tana fita dai-dai lokacin da ake shigo da kayan amaryar Alhaji Abu mata sai kuɗa suke, tsaki Hauwa tayi kana ta dube matanshi da ƴaƴanshi dake tsakar gida kowa na sabgar gabanta tace,

" An daiyi asara, ni banyi dacin uba ba wasu basuyi dacin uba da miji ba".

Tana faɗin haka tasa ƙafa ta bar gidan saboda taje ta samu mafita.

Sosai hankalinshi ya tashi ganin Hauwa ta tafi kodan halin da taga mahaifin shine, wata ƙila haka ne, amma har ga Allah Hauwa tashiga ranshi dan shi yanzu burinshi bai wuce  yaganshi tari da ita sona shan soyayya ba, amma gaskiya Mamarshi bata kyauta ba, da yanzu yana can yana hutawa da Hauwarshi mai kayan ni'ima, yajima tsaye yana tunanin yadda zaiga Hauwa sannan ya samu wasu almajirai manya ya gaya musu aikin da za suyi musu sannan ya dawo wajan mahaifinshi, gyaran jiki da ɗaki akayi haɗi da sanya turare aka sauya mishi ɗaki sannan ya biya su suka tafi.

Bayan ya bashi fura yasha ne yasamu ya buɗe baki da ƙar yace,

" Amadu ina Hauwa'u, ba yanzu nagan ku tare ba, amma gaskiya naji daɗi da kuka san juna".

Kallon Baban Ahamd yayi tsaf sannan yace,

" Baba daman kasanta ne?".

Murmushi yayi irin na ƴan duniya yace,

" Kamar ya nasanta Ahamad, na haifita sannan kace na san ta"......." mikace Baba!".

" Nace nasan wannan aikin iyayenku ne suka haɗa ku, ko dai kun je gidan lya gaishta ta haɗaku, dan haka kasani baka da ƴar uwa kamar Hauwa, duk  nine na haifeku , amma kuyi haƙuri da yadda rayuwa tazo".

Jikin Ahamd ne ya ɗau karkarwa kana yace,

" Kana nufin Hauwa Yaya tace?".

" Eh wallahi hala kai ka ɗauka kaine yaya, saboda ka ganta da ƙaramin jiki ko, kai ko ka biyoni da Babban jiki".

" Nashiga uku, amma Baba kacutar damu dan wallah a halin yanzu Hauwa budurwa tace!!.

Da ƙafi uban ya tashi zaune abinda yajima baiyi ba, kullum yana kwance saboda ya kasa koda tankwashi ƙafar bare asa ran zai iya mutsi yau shine ya tashi zaune saboda razana.

    A hankali yake taka ƙafarshi har ya isa parlour da yake tunanin zai sami mahaifiyar tashi, zaune take tama kallon labarai tayi kyau abinta da ka ganinta ba abinda ke damunta.

Da sallama yashigo, karɓa masa tayi batare da ta ɗago ta kalleshi ba, wanja ƙafarta yazo ya zauna sannan ya gaisheta haɗi da jingina kansa a ƙafarta.

Yajima ahaka amma bai ji tayi masa abinda take masa ba, wato tasanya hannuta akansa tana ya mutsar masa suman kanshi, haka take masa tun yana yaro shiyasa yake son tayi mishi haka.

Dubanta ya yi har ya buɗa baki yayi magana sai yaji muryar Dady na faɗin,

Ɗan Hajiya saukar yaushe?".

" Duk da yanzu ka girma shiyasa naga ko tafiya zakayi babu dole kasanar damu".

Murmushi yayi haɗi da basu haƙuri yace tafiyarce ta zo a bazata, sai Dady yace to muma yau zamuyi maka baza ta, dan tabbas ƙarshin watannan zamu ɗaura maka aure da wadda duk wadda muka ga dama, amma idan kaga mu bamu isa da kai ba kaje kagayawa Hajiyar da ke goya maka baya.

Har ya buɗe baki yayi magana sai Dady yace bana son jin komai daga gareka nariga na gama magana sai ka farashirin karɓar amarya kai da abokanka da ƴan matan ka.

Dady na gama faɗar  haka suka barmishi parlour  kanshi sai juya masa yake.

  Yau saura kwana biyar a ɗaura aure Kabir da amaryarshi Nana, kuma a yau ne Kabir yake so ya gayawa Mumy zaiyi aure, danshi koda gari ya waye ba inda yaje, duk abinda take son shi yake yimata, sai kwasar soyayyya suke ta mutunci, ita ko Mumy sai kafa-kafa take kar tayi abinda zai ɓata mishi rai, ranar gida ya wuni har dare, bayan sunci abinci sunyi wanka, dan yau ko wanka tare sukayi , har man shafawa shi ya shafa mata haɗi da sanya mata kayan bacci waɗanda ranshi ke so, kallonta yayi ciki da nuna mata tsantsar so yace,

" Baby wallahi sonki ko da yaushe ƙara ruruwa yake a zuciya na, dan Allah ki taimaka min kici gaba da zama dani kada ki barni, duk da a halin yanzu ni mai laifine a gareki".

Bata ce dashi koma ba ta haɗa bakinshi da nata waje ɗaya suna kissing ɗin juna, sai da sukayi son ransu sannan tace,

" Baby duk yadda kake sona ni nasan nafika sau dubu wallahi soyayayarka zata illatani dan Allah kar ka barni, burina a koda yaushe naganin tare da kai".

" Muna tare masoyiya ta, ba wanda ya isa ya rabamu ko anƙi ko ansu dole abarmu, amma ina so ki fahince ni, wallahi nima badan son raina haka zata faru ba, kiyi haƙuri kinji, saboda Mumy ce ta haɗa ni da ɗiyar abokiyar ta, wai ita yarinyar ce ta ganni wai ba wanda take so sai ni, duk wanda yafito tace sai ni, shine su Baba suka ce tunda yarinya tace ni take so nayi haƙuri ayi aure, tun kafin na buɗa baki sai Mamarta tace komai ta ɗauke min har sadaki itace zatayi komai, burinta kawai na aure yarinyar, shine Baba yace to tunda haka ne ranar alhamis za'a ɗaura aure".......wata ƙarace Mumy ta sanya wadda gidan gabaki ɗaya sai da ya amsa.....



*SUMMY M NA'IGGE✍️*

MIJIN BABATA NEWhere stories live. Discover now