29

146 12 0
                                    

*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*


*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

               *Z.W.F.🏝️*

*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*

      

*SHAFI NA 29*

Koda ta isa gidan su lnna bata same ta ba tashiga maƙota wajan barkar haihuwa, zama tayi tayi tagumi tana tunanin yadda rayuwa ta zoma ta da kuma yadda komai ya canza mata lokaci ɗaya, tana cikin haka sai ga lnna tashigo gidan da sallamar ta, koda taga takalmi bakin ƙofar ɗaki bata wani damu ba, ta ɗauka ɗiyan ƴan uwanta ne suka zo ganta.

Kai tsaye tashiga ɗaki, tsaye tayi bakin ƙofar ɗakin ta kasa sakin labulen ɗaki saboda mamakin ganin wadda tagani zaune tayi tagumi ta kifama waje ɗaya ido, da alamu ma bata san lnna tashigo cikin ɗakin ba.

Inna na ganin haka sai tayi gyaran murya, haka yasa Hauwa ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi haɗi da kai dubanta ga lnna cikin azama tace,

" Inna kin dawo? ban jima da zuwa ba wani yaro yace min kin shiga maƙota wajan barkar haihuwa".

Wani kallo lnna ta bita dashi na tsana kana tace,

" Miya kawoki wajena! kin manta abinda nace dake ne? to idan kin manta bari na tuna miki! nace daga wannan lokaci na yafe ma Alhaji Abu ke! kuma ko a hanya kika ganni kika nuna kin sani wallahi wallahi banya femiki ba! to yanzu dakika ɗauko ƙafa kika zo gidan nan mi zan miki? ko kinzo ne idan nayi aure ki zauna tare da mijin nawa ko koma kinzo ki zauna da ƴan uwana ko ƴaƴansu! to bari kiji tun wuri kisa ƙafar da tashigo dake gidannan ta fitar da ke, tun kafin na tsine miki wallahi!".

Hawaye ne suka fara zuba a idon Hauwa, har ta buɗa baki tayi magana cikin hanzari lnna ta dakatar da ita haɗi da nuna mata ƙofar fita.

Sarai tasan halin lnna, tunda har tayi fushi dole ta tafi ta bata waje zuwa kwana biyu, haka Hauwa ta tashi tana kuka kamar ranta zai fita ta bar gidan.

Har ga Allah lnna taji tausayin Hauwa, amma sai taƙi nuna haka saboda tana son ta koye darasi kuma ta nuna mata cewa tayi kuskure babba wajan yadda da Alhaji Abu da ranshin kunyar da take yi.

Hauwa tajima ƙofar gidansu lnna tana kuka daga baya ta kama hanya ta koma gidan ubanta.

          ************
Tun abin bai damun Mumy har ya kai yana damunta, wani abu idan ya yi mata akan ƴarshi har ƴar kwalla take zubarwa, saboda ita har yanzu babu ciki koma babu alamarsa, kuma gashi ƴarta tazo ta ɓata har yau babu labarin ta.

Ko yau Kabir da ƴarsa yazo gidan Mumy, bayan sun gaisa take tambayarshi Baby Amal da ke wasa kamar wata ƴar watanni, hannu Mumy ta miƙa tace ya bata sai yace,

" A'a kibar ta, kawai je ki ƙarasa aikin da ke gabanki".

Murmushi Mumy tayi kana tace,

" Na kammala duk aikin da ke gabana kai kaɗai nake jira dan gaskiya yau ina buƙatar mijina".

Ta faɗi haka tare da kashe masa ido ɗaya.

Wata harara ya afka mata kana yace,

" Yanzu mikike so nayi miki?".

Murmushi tayi haɗi da zama kusa dashi tasa hannuta cikin rigarsa ta fara shafar sumar da ke kwanci a jikinsa kana tace,

" Soyayar ka nake so kabani yanzu gaba ɗaya ka daina nuna min kulawa kamar yadda kasaba min a da''.......tun bata kai ƙarshin zan cin ba ya yi sauri da katar da ita haɗi da buga mata tsawa yace,

" Baki da hankali ne, gaban ƴata zaki riƙa gaya min waɗannan magana, ko dan kin manci zafin haihuwa ne zaki gaya min haka gaba ƴar tawa, to bari kiji,  daga yau kar kisakiyi min haka gaban ƴata in har ba su kike musamu matsala ba!".

Ya kai ƙarshin zancin zuciyar shi kamar ta fito waje saboda ɓacin rai.

Ƴarshi ya ɗauka yafita ya bar gidan gaba ɗaya.

Mumy itako hoto ta koma tana kallon ikon Allah, ƴar da ko wata uku masu kyau bata ƙarasa ba, to mi yarinyar tasani da har zai gaya mata haka?.

             *********

Ranar da Abdul zai yi tafiya ranar yashigo ɗakin Hansa'u abunda bai taɓayi ba, kuma koshi ya shigo ne dan ya tambaye ta idan akwai abinda take so yasa a kawo mata saboda ko ba komai baya son yashiga hakkinta da yawa, dan shi wallahi tausayi take bashi sosai.

Koda yashigo bata ɗakin har zai koma sai yaji kamar mutsin ruwa a ban ɗaki, dan haka ya samu waje ya zauna kafin ta fito.

Koda tagama wanka tasan ita kaɗai ce a ɗakin shiyasa ta fito batare da wata damuwa ba, ɗaure take da wani figegin tawol wanda bai ida rufe mata cinya ba, tana riƙi da ɗaya tana gogar gashin kanta, kai tsaye gaban madubi ta nufa dan tashafa wa jikinta mai har ma da gashin kanta.

Har ta buɗe marfin mai zata fara gogawa jikinta, shiko lokacin ya duba a gogon hannunsa, yaga ko su Mumy bai wa sallama ba, kuma lokaci na tafiya dan haka yace,

" Rashin kunya zakiyi min? dan kin ganni zaune shine zaki fito kina wani karkaɗa jikinki dan na so ki ko, to kinyi a banza in har dan ni ki kayi".

Tsoro taji sosai sai da ta tabbatar da mutum ne sannan tayi sauri ta ɗauko wani hijab ta rufe jikinta dan ita saboda kiɗema bata masan miya yace ba.

Tsaki ya yi kana a jeye mata kuɗi ya fita....

*COMMENT AND SHARE*

*ƴan uwa da abokanan arziki Dan Allah kunu na mun soyayyar ku ta hanyar yimun shering book ɗina na gasar Matasan marubuta 2021 dan Allah🙏 mai suna ƘWAƊAYI KO BURI sannan ranar voting kuje google kuyi mani voting dan Allah*



*SUMMY M NA'IGE✍️*

MIJIN BABATA NEWhere stories live. Discover now